GSS Kagara: An sace dalibai 27 da wasu 14 a makarantar da ke jihar Neja

Lokacin karatu: Minti 2

Hukumomi a Najeriya sun sanar da sace mutum ar'bain da biyu a wani hari da aka kai da safiyar yau a makarantar kwana ta garin Kagara.

Gwamnan jahar Neja Abubakar Bello ya ce an kwashe dalibai 27 da ma'aikata uku hadi da iyalansu su goma sha biyu.

Duk da kawo yanzu ba a iya tantance masu alhakin harin ba, satar mutane don neman kudin fansa ba sabon abu bane a Najeriya, kuma jahar Neja na cikin yankunan arewacin kasar da yan bindigar suke aika aikarsu.

Shugaba Muhammadu Buhari ya umurci jami'an tsaron kasar su yi duk mai yiwuwa domin ceto mutanen.

Za a rufe wasu makarantun kwana

Gwamnatin jihar ta Neja ta bayar da umarnin rufe wasu makarantun kwana da ke jihar sakamakon rashin tsaro.

Gwamnan jihar Abubakar Sani Bello ne ya bayyana hakan a sakon da ya wallafa a shafinsa na Tuwita

A cewarsa: "Gwamnatin jihar Neja ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun kwana nan take a kananan hukumomin Rafi, Munya, Shiroro da kuma Mariga saboda rashin tsaro da ake fama da shi a yankunan."

Buhari ya aika sojoji da 'yan sanda

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya samu labarn sace daliban na makarantar sakandaren Kagara, yana mai shan alwashin ceto su daga hannun 'yan bindigar.

A sanarwar da Malam Garba Shehu, kakakin shugaban kasar ya aike wa manema labarai, ya ce "bayan samun wadannan rahotanni, Shugaban kasa ya umarci dakarun soji da na 'yan sanda su tabbatar da ceto dukkan wadanda aka sace ba tare da an yi musu lahani ba."

"Kazalika Shugaban kasa ya aike da tawagar manyan jami'an tsaro zuwa Minna da ke jihar Neja domin sanya hannu kan aikin ceto sannan su gana da jami'an gwamnatin jihar da shugabannin al'umma da iyaye da kuma malaman makarantar," in ji Garba Shehu.

Shugaban ya ce yana yin addu'a domin ganin an ceto daliban da aka sace, sanna ya yi tur da "harin matsorata kan daliban da ba su ji ba ba su gani ba".

'Yan bindiga na matsa kai hari kan makarantu a ci gaba da garkuwa da mutane da suke yi a musamman arewacin Najeriya.

A watan Disamba, an sace dalibai fiye da 300 daga makarantar sakandaren Kankara da ke jihar Katsina lamarin da ya ja hankalin duniya.