Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matsalar Tsaro: Illar bai wa masu satar mutane kudin fansa a Najeriya
Kwararru kan harkokin tsaro a Najeriya sun yi kira ga jama'a su daina bayar da kudin fansa ga barayin mutane suna masu cewa hakan zai iya kawo karshen matsalar.
Malam Abdullahi Adamu, wani kwararre kan harkokin tsaro da ke jihar Kano a Najeriya, ya shaida wa BBC cewa akwai bukatar duk wanda aka dauke wa dan uwansa ya jure a maimakon biyan kudin fansa.
Ya kuma ce akwai laifi ta bangaren al'umma da kuma su kan su hukumomin kasar game da abubuwan da ke faruwa na matsalar yawan sace-sacen jama'ar.
"A lokuta da dama mutane ba sa bai wa jami'an tsaro gudunmawar da ta dace su bayar a bangaren samar da bayanan sirri da ke cikinsu, wanda ta hakan ne zai taimaka wa jami'an tsaron bin diddigin masu aikata wannan ta'asa".
Sai dai ya yarda cewa rashin tabbacin kare lafiyarsu daga wurin jami'an tsaro na daga cikin dalilan da suke sa mutane rashin fitowa su bayyana wa jam'an tsaron abubuwan da ke faruwa a yankunansu.
Amma kuma masanin ya bayyana hakan da cewa "ai akwai lambobin waya da jami'an tsaro suka rarraba suka ce ba ma sai mutum ya kira su kai tsaye ba za su iya rubuta sako na kar-ta- kwana ya tura," wanda in ji shi ta hakan ne za su iya bin diddigin mutanen su bincika kuma idan suka tabbatar da hakan za su kai su ga hukuma.
"Mu abin da muke fadi a kullum shi ne, su masu satar mutanen nan yanzu an san a cikin dazuka suke, kuma a wasu lokutan ma idan kana hira da mutane daban-daban a Katsina, da Sokoto da Zamfara za ka ji cewar suna ma ganin mutanen nan da bindigogi suna shigowa wasu daga cikin kasuwannin kauyuka suna sayayya su koma,'' in ji masanin, don haka bai kamata a ce mutane suna kin bayar da hadin kai wajen sanar da hukumomi ba kan abin da suka san daga baya zai zamar musu babbar matsala."
Malam Abdullahi ya kuma bayyana cewa akwai kasashe da dama da suke amfani da jami'an tsaro na daji, inda akan ba su bindigogi da kayan sarki, domin su gudanar da ayyukan tsaro da suka shafi laifukan da ake aikatawa ko kuma ake shirya yadda za a aiwatar a cikin dazuka.
"Saboda a cikin dazuka kawai suke gudanar da aikinsu, sun san lunguna da sako na ko ina a cikin dazuka, don haka za su iya bin diddigi su kuma zakulo duk wasu bata-gari da ke ciki", a cewarsa.
Hadarin biyan kudin fansa
Masanin ya kuma bayyana cewa galibi masu satar mutanen kan yi hakan ne domin samun kudin shiga, don haka idan ya zamanto an daina ba su kudin za a samu saukin faruwar hakan a ko ina.
Ya kara da cewa "Idan da kowa zai daure ya ki biyan kudin fansa, ya hakura ya sadaukar da mutum dayan nan, ko da kuwa iyaye ne, musamman ma 'yaya tun da za ka iya samun wasu, ta haka zai rage yawan sace-sacen jama'ar, saboda ai daman saboda su karbi kudin ne suke sace mutanen."
Ta bangaren hukumomi kuma, masanin ya bayyana cewa akwai sakaci sosai a fannin samar da tsaron, wanda ya ce abin yana bani mamaki kwarai da gaske.
Ya kuma ce saboda dazukan nan duka namu ne, kuma akwai jirage masu saukar angulu, kananan jiragen yaki ga su nan a makarantar koyon tukin jirgin sama ta Kano, da Lagos, da Kaduna har ma da Makurdi amma sai ka ga 'yan bindiga sun shigo gari sun shafe sa'oi suna cin karensu ba babbaka, su kwashi mutane su tafi da su, su kuma hau kan babura su shiga daji.
"Dazukan nan kuma a lalace za ka ga tsakaninsu da garin da suka yi satar mutanen sai sun yi tafiyar akalla kilomita ashirin ko sama da haka kafin su isa wurarensu, don haka me zai hana a tashi ire-iren wadannan jiragen tun da dole dai an samu rahoto?", a cewarsa.
Sai dai kuma wannan ra'ayi na masani Abdullahi Adamu kan kin biyan kudin fansa domin magance matsalar ya ci karo da na galibin jama'a a Najeriyar da suke ganin ba daidai ba ne, kuma yana da matukar wahala kana ganin wani naka a hannun 'yan bindiga amma ka kyale shi.