Cikin yaran da ake yi wa fyaɗe a Sudan 'har da ƴan shekara ɗaya'

Hala

Asalin hoton, Unicef

Bayanan hoto, Hala (ba asalin sunanta ba) tana cikin ƙananan yara da aka yi fyaɗe
    • Marubuci, Barbara Plett Usher in Port Sudan & Natasha Booty in London
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 4

Gargaɗi: Wannan maƙalar ta ƙunshi bayanan cin zarafi ta hanyar lalata da za su iya tayar wa wasu hankali.

Masu ɗauke da makamai na cin zarafi da kuma yi wa yara ƴan shekara ɗaya fyaɗe yayin da ake tafka yaƙin basasa a Sudan, kamar yadda asusun yara na Majalisar Ɗinkin Duniya Unicef ya bayyana.

An gano yadda ake amfani da zalinci ta hanyar lalata a matsayin makamin yaƙi a ƙasar tun bayan fara yaƙin shekara biyu da suka wuce.

Amma rahoton na Unicef, shi ne na farko da ya bayar da cikakken bayani kan yi wa yara fyaɗe a Sudan.

Ɗaya cikin uku na yaran da ake zalinta maza ne, waɗanda ke fuskantar "ƙalubale na musamman" wajen bayar da rahoton irin laifukan da ake aikata musu da kuma neman agajin da suke buƙata.

Unicef ya ce duk da cewa karo 221 kawai na fyaɗen aka bayar da rahoto a hukumance tun daga fara yaƙin a 2022, akwai yiwuwar adadin ya zarta haka sosai.

Rahoton na UNicef ya bayar da bayanai masu tayar da hankali game da cin zarafin yaran.

Daga cikin waɗanda suka fi tayar da hankali shi ne 16 daga cikin yaran 'yan ƙasa da shekara biyar ne, cikinsu har da jarirai huɗu.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Unicef bai faɗi wanda ya aikata ba, amma sauran hukumomin MDD sun zargi dakarun Rapid Support Forces (RSF) da aikata mafi yawan laifukan, inda suka ce suna amfani da fyaɗe domin tayar da hankalin fararen hula da kuma daƙile adawa da ayyukansu.

RSF, wadda ke yaƙar dakarun gwamnatin Sudan, da sojojin na Sudan duka sun musanta zargin.

"Mummunan tashin hankalin da ake aikatawa ta hanyar lalata a Sudan abin kiɗimarwa ne," a cewar Mohamed Chande Othman, shugaban wata tawagar jin bahasi ta MDD a rahoton da ta wallafa a watan Oktoba.

A cewar hujjojin da ƙungiyoyin kare haƙƙi suka gabatar, mutanen da aka zalinta a yankin Darfur da ke hannun RSF, akan kai musu hari ne saboda baƙaƙen fatar Afirka ne ba na Larabawa ba, da zimmar korar su daga Sudan.

Tuni kuɗaɗen da MDD ke samu na kai agaji a Sudan suka ragu sosai. Dakatar da tallafin da Amurka ta yi ana tsammanin zai ƙara ta'azzara lamarin wajen dakatar da shirye-shiryen tallafa wa mutanen.

Nau'in bayanan da ke fitowa daga rahoton Unicef na jaddada girman matsalar da ake ciki.

"Bayan ƙarfe tara na dare, wani ya buɗe ƙofa riƙe da bulala, ya zaɓi ɗaya daga cikin yaran mata, ya kai ta wani ɗakin. Ina jiyo ƙara da ihun yarinyar. Suna yi mata fyaɗe" kamar yadda Omnia (ba sunanta na gaskiya ba ne) ta bayyana - wata da ta tsira daga sharrinsu bayan tsare ta a ɗakin maza.

"Duk lokacin da suka yi mata fyaɗen sai ta dawo jikinta duk jini. Har yanzu 'yar yarinya ce. Sai asuba ta yi suke sakin yaran kuma su dawo kusan ba a cikin hayyacinsu ba. Kowacce tana kuka tana magana sama-sama. Tsawon kwana 19 da na yi a wurin, sai da na kusa kashe kaina."

Yawan mutanen da yaƙin ya raba da muhallansu ya ƙara jefa mata da yara cikin haɗari - uku cikin huɗu na yara matan da suka isa zuwa makaranta ba su zuwa, in ji MDD.

Janye tallafin Amurka

Ɗaya daga cikin abubuwan da ke ƙara munin lamarin shi ne mutanen da aka zalinta ba su da inda za su je domin neman agaji, saboda an lalata wuraren kiwon lafiya da yawa, an sace komai ko kuma dakaru ne ke zaune a wurin.

Janye tallafin da Amurka ta yi ka iya jefa sauran da suka rage cikin haɗari.

Unicef ta daɗe tana bai wa yara mafaka ta hanyar 'yan gwagwarmaya mazauna yankin da suka kafa wata hanyar jin koken mutanen da abin ya shafa.

'Yan gwagwarmayar sun dogara ne sosai kan tallafin Amurka, kuma tuni aka tilasta wa wasu suka rufe cibiyoyinsu, a cewar wata tawaga da ke bin diddiginsu a Sudan.

BBC ta fahimci cewa aƙalla ɗaya daga cikin ƙungiyoyin mata masu bayar da agaji da ake kira "She Leads" ta rufe ayyukanta saboda katse tallafin.

Ba wasu kuɗi ne masu yawa ba, amma dai suna isar ma'aikata su gano aƙalla mutum 35 duk wata da suka tsira daga zalinci, in ji Sulaima Elkhalifa, wata mai kare haƙƙi a Sudan.

Waɗanda 'yanbindiga suka yi wa fyaɗe "ba su da lokacin ma da za su yi jinyar matsalar ƙwaƙwalwarsu", kamar yadda ta shaida wa BBC.