'Na yi kewar makaranta': BBC ta ƙaddamar da shirin koyar da yara a yankunan da ake yaƙi

Tareq, ɗan shekara 10 na zaune a kan baraguzai a Gaza, sanye da wando, rigar sanyi da jaka.
Lokacin karatu: Minti 4

Tareq ɗan shekara 10 daga Gaza, da Safaa, ƴar shekara 14 daga Sudan suna rayuwa a wuraren da ke da nisan kilomita 200 tsakani. Ba su taɓa haɗuwa ba, amma su na fuskantar wata matsala iri ɗaya - yaƙi ya hana su samun ilimi.

''Lokacin da na ga makarantarmu a ruguje, wani baƙin ciki ya lulluɓe ni. Ina muradin in ga ta koma yadda take a baya,'' Tareq ya shaida wa BBC a Gaza.

''Duk da abin da ya faru, ban daina neman ilimi ba. Ina karatu a gida, ina tabbatar da cewa ban yi asarar lokacina ba saboda lokacin da zan koma makaranta, zan koma cikin shiri,'' in ji shi.

Safaa na da burin zama likitar fiɗa. ''ban cire rai ba,'' a cewar ta, amma yaƙin basasa a Sudan ya sanya tana cikin kaduwa sanadiyyar irin rayuwar da ta shiga.

''Gawarwaki a baje a ko ina, hakan ya taɓa ni, shi ya sa nake so na zama silar ceton rayuka a maimakon silar rasa su.''

Safaa, ƴar shekara 14 daga Sudan ta na zaune a sansanin ƴan gudun hijira tare da wasu yara su biyar. Safaa na sanye da riga mai dogon hannu da ɗankwali.
Bayanan hoto, Safaa, ƴar shakaru 14 daga Sudan, ta ce ta na da burin zama likitar fiɗa

Tareq da Safaa na daga cikin yara miliyan 30 waɗanda a cewar Asusun kula da ƙananan yara na majalisar ɗinkin duniya, UNICEF, ba sa zuwa makaranta a Gabas ta Tsakiya da kuma Kudancin Afirka.

Sun ƙiyasta cewa fiye da rabin adadin wato yara miliyan 16.5 a Sudan su ke.

A kan haka ne BBC ta ƙaddamar da sannanan shirinta na koyar da alumma da harshen larabci mai suna Dars.

A shekarar da ta gabata a Gaza, fiye da yara 600,000, wato duka adadin yaran da ya kamata a ce suna makaranta a Gaza, ba su sami ilimi ba'', a cewar Saleem Oweis, wani mai magana da yawun UNICEF.

''Muna ganin yadda rikice rikice da rashin tsaro da yaƙi ke kawo tsaiko sosai ga koyo da ilimin yara,'' in ji shi.

A Sudan, kusan shekaru biyu bayan yaƙin basasa ya ɓarke tsakani sojoji da dakarun RSF, miliyoyin yara na rayuwa a sansanonin ƴan gudun hijira waɗanda kawai ke samun ilimi ta hanyar wasu ƴan dabarun gargajiya.

A wata hira da BBC, ministan ilimin Sudan, Ahmed Khalifa ya bayyan girmar matsalar.

''Babu jihar da aka bari,'' inji shi. '' Sudan na da aƙalla makarantun gwamnati 15,000. Tsakanin kashi 60 zuwa kashi 70 duk an lalata su, an lalata gine ginen da kuma littatafai.

''Ko a jihohin da akwai ɗan tsaro, an lalata makarantu saboda hare haren kungiyoyin mayaƙa.''

Wani hoto daga shirin Dars da ke nuna yara biyu, mace da namiji. su biyun sun ɗaga hannu. A tsakiyarsu akwai wani mutum.
Bayanan hoto, Shirin BBC Dars na koyarda karatu ga yara

An ƙaddamar da shirin Dars karon farko a shekarar 2023 saboda yaran da ke Afghanistan, ciki har da yara mata da aka haramtawa zuwa makarantun sakadiri.

Shirin wanda aka tsara domin yara ƴan shekara 11 zuwa 16 ana gudanar da shi duk mako kan darussan da suka haɗa da lissafi da fasaha da sauyin yanayi da lafiyar kwakwalwa.

Ana kuma basu labaran yara kamar su Tareq da Safaa waɗanda duk da yaƙin da akeyi da wasu matsalolin, ba su cire rai ga neman ilimi ba.

A yaɗa kashin farko a ranar lahadi 9 ga watan Fabrairu a tashar talibijin ta BBC News Arabic.

Sabbin shirin kuma za a rika nuna su duk ranar Lahadi da karfe 05:30 agogon GMT, a maimaita da karfe 10:05 agogon GMT a sauran ranakun makon.

Ana kuma iya kallon shirin a shafukan intanet kamar BBC News Arabic a YouTube da kuma gidanjen radiyo a Gaza da Syria.