Ƙasar da yara suka fi shan wahala a duniya saboda yaƙi

Asalin hoton, Joyce Liu / BBC
- Marubuci, Lyse Doucet
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Kassala
- Lokacin karatu: Minti 5
Mahmoud yaro ne mai yawan murmushi duk da cewa ya rasa haƙoransa a wurin wasan yara.
Maraya ne a Sudan, wanda sau biyu ana raba shi da danginsa a mummunan yaƙin da ke faruwa a ƙasarsa - yana ɗaya daga cikin yara kimanin miliyan biyar waɗanda suka yi asarar kusan komai yayin da yaƙi ke tagayyara su daga wuri zuwa wuri a yankin da yanzu ake fuskantar rayuwa mafi muni a duniya.
A yanzu haka a faɗin duniya babu ƙasar da yara ƙananan ke gudun hijira, mutane da dama ke fuskantar matsanciyar yunwa fiye da Sudan.
Tuni aka ayyana masifar yunwa a wani ɓangare na ƙasar, mutane da dama na kan hanyar faɗawa ƙangin yunwa, saboda rashin tabbas na inda za su samu abinci.
Sabon shugaban hukumar jin ƙai ta Majalisar Dinkin Duniya, Tom Fletcher ya ce yaƙi ne da ba a ''san irin illar da ya yi ba''.
"Ƴan Sudan miliyan 25 ne - fiye da rabin al'ummar ƙasar - ke buƙatar tallafi a yanzu haka '', in ji shi.
A daidai lokacin da duniya ke fama da munanan yaƙe-yaƙe, inda yaƙin Gaza da Ukraine suka fi ɗaukar hankalin ƙasashen duniya wajen bayar da tallafi, Mista Flecher ya ce a ganinsa Sudan ce ƙasar da ta fi cancantar tallafi.
"Wannan rikici ba zai ɓoyu ga Majalisar Dinkin Duniya ba, jami'an bayar da agajinmu na filin daga suna jefa rayukansu cikin hatsari domin taimaka wa mutanen Sudan,'' kamar yadda ya shaida wa BBC a yayin wata ziyarar ran gadi ta mako guda.
Mafi yawa daga cikin mutanen da ke aiki da tawagarsa 'yan asalin Sudan ne da suka rasa gidajensu, a wannan yaƙi na kankane madafun iko tsakanin sojojin ƙasar da dakarun RSF.
Yayin ziyarar gani da ido da Mista Flecher ya yi ta farko zuwa Sudan ya je gidan marayu Mahmoud Maygoma a Kassala da ke gabashin ƙasar, inda a yanzu fiye da yara 100 ke cikin gidan, wanda bene ne mai hawa uku.

Asalin hoton, Joyce Liu / BBC
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Suna zaune tare da masu kula da su a Khartoum, babban birnin ƙasar har lokacin da sojojin ƙasar da mayaƙan RSF suka far wa juna a watan Afrilun 2023, lamarin da ya sa gidajen marayun ƙasar suka cika maƙil da ƙananan yara, sakamakon yaƙin da ya ɗaiɗaita ƙasar.
A lokacin da yaƙin ya bazu zuwa gidan kula da marayun, da ke unguwar Wad Madani a tsakiyar Sudan, waɗanda suka tsira sun fice zuwa Kassala.
A lokacin da na tambaye Mahmoud mai shekara 13 game da fatansa, sai ya yi hanzarin buɗe bakinsa - da haƙoransa na gaba suka zube.
"Ina son zama gwamnan jihar nan, domin na sake gina gidajen da suka lalace,'' in ji shi.
Ga 'yan Sudan miliyan 11 da aka sauya wa sansanin 'yan gudun hijira, mayar da su gidajensu domin sake gina rayuwarsu ka iya zama babbar kyauta a gare su.
A yanzu, samun abin da za su ci ma, wata babbar matsala ce ta yau da kullum.
Haka ma ga hukumomin jin ƙai, ciki har Majalisar Dinkin Duniya, samar musu da kayan jin ƙan ya zama wani babban ƙalubale.

Asalin hoton, Joyce Liu / BBC
Yayin ziyarar Mista Fletcher ta kwana huɗu tare da ganawa da jami'ai a Port Sudan, shugaban mulkin sojin ƙasar, Abdel Fattah al-Burhan, ya bayyana a shafinsa na X cewa ya bai wa Majalaisar Dinkin Duniya damar shigar da ƙarin kayan agaji zuwa ƙasar, tare da amfani da filayen jiragen ƙasar uku domin wannan aiki.
Sabuwar sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya,(WFP), ya samu damar isa wasu yankunan filin daga da ke ƙarƙashin ikon RSF, ciki har da sansanin Zamzam da ke yankin Darfur, da ke ɗauke da mutane kusan rabin miliyan, inda a baya-bayannan aka tabbatar da annobar yunwa a wurin.
"Mun shafe watanni muna ƙoƙarin samun damar isa waɗannan yankuna,'' in ji Alex Marianelli, wanda ya jagoranci ayyukan WFP a jihar Port Sudan.
A bayanmu gidan aana abinci na WFP ne, inda leburorin Sudan ke loda wa manyan motoci abinci domin kai wa wuraren da aka fi tsananin buƙatar ayyukan jin ƙai.
Mista Marianelli ya ce bai taɓa aiki a irin waɗannan wurare da ke cike da hatsari.
Daga cikin hukumomin bayar da agaji, wasu na sukar Majalisar Dinikin Duniya, da cewa an ɗaure hannayenta saboda amincewa da Janar Burhan a matsayin shugaban sojin ƙasar.
Janar Burhan da hukumomin Sudan ne ke da iko da shigayen bincike'', in ji Mista Flecher.
"Dole idan muna son zuwa irin waɗannan wurare sai da amincewarsu."
Yana kuma fatan cewa mayaƙan RSF za su sanya muradun fararen hula a gaba.
"Zan je ko'ina, zan yi magana da kowa, domin tabbatar da kai kayan agajin nan domin kare rayuka,'' in ji Mista Flecher.
A yakin na sudan, an zargi duka ɓangarorin biyu da amfani da yunwa a matsayin makamin yaƙi.
Haka ma cin zarafi na lalata, wadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana a matsayin ''bala'i'' a Sudan.

Asalin hoton, Joyce Liu / BBC
Na kuma tambayi wasu mata da suka saurari jawabin Mista Flecher a ziyarar tasa.
"Muna tsananin buƙatar taimako, amma babban aikin na kan 'yan Sudan,'' in ji Romissa, da ke aiki da wata ƙungiyar agaji da ke ƙasar, wadda ta bayyana mana irin munanan abubuwan da ta gani a Khartoum tun bayan fara yaƙin.
" Lokaci ya yi da 'yan Sudan za su haɗa kai don ƙwato wa kansu 'yanci''.
'Yan Sudan na ƙoƙarin yin abin da ya kamata da ɗan abin da suka mallaka.
A wani gida mai ɗakuna biyu da ake kula da matan da aka ci zarafinsu da yara marayu ana ƙoƙarin taimaka wa mutanen da aka zalunta.
Wadda ta kafa ta, Nour Hussein al-Sewaty, wanda aka fi sani da Mama Nour, shi ma ya fara rayuwa a gidan marayu na Maygoma.
Ita ma ta gudu daga Khartoum don kare waɗanda ke hannunta. Wata mata da ke zaune tare da ita a yanzu an taɓa yi mata fyaɗe kafin yaƙin, sannan bayan fara yaƙin aka yi garkuwa da ita, tare da sake yi mata fyaɗe.
Ita kanta Mama Nour wadda a baya ke cike da ƙwarin gwiwa a yanzu tana cikin tashin hankali.
"Mun fara gajiya da wannan aiki, muna buƙatar taimako," in ji ta.
"Muna son shaƙar isakar yancin gudanar da ayyukanmu ba tare da takura ba, muna son mu san cewa akwai sauran mutane a duniya da suka damu da mu, mutanen Sudan."











