Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gwamnatin Najeriya ta ce ba za ta yi wa malamai katsalandan ba
Gwamnatin Najeriya ta ce ba za ta rika yin katsalandan a kan yadda malaman addini ke gudanar da fadakarwa ga al’umma ba musamman yayin da ake shirin fara tafsirin Alƙur'ani(mai girma) a watan azumi na Ramadan da Musulmi ke yi a duk shekara.
Gwamnatin ta bayyana hakan ne yayin wani taro na malamai da limamai na addinin Musulunci da majalisar koli kan harkokin shari’ar Musulunci ta gudanar a Kaduna.
Yawancin malaman da suka halarci taron sun yi ta nanatawa tare da nuna cewa lokaci ya yi da malamai za su mayar da hankali wajen nuna muhimmancin da ke tattare da hadin kan al’umma, maimakon rarrabuwar kai saboda sabani ko bambancin akida.
Mataimakin shugaban kasar Najeriya Kashim Shettima wanda mai ba shi shawara kan harkokin siyasa Dakta Hakeem Baba-Ahmed ya wakilta a taron, ya ce baya ga jajircewa wajen fadakar da al’umma a kan hadin kai wajibi ne malaman su kawar da son-rai su rika fada wa al’umma gaskiya.
Ya ce: ''Na daya su gaya wa jama’a abin da suka gani. Na biyu su taimaka mana su ba jama’a hakuri wannan matsaloli da muke da shi ba irin wanda za ka tashi yau ba ne da matsala gobe ka warware. Na uku su nuna wa jama’a Allah Ubangiji Yakan gwada mu da fitina Yana kuma gwada mu da samu.''
Dakta Hakeem din ya ce wasu abubuwa da suke gani a kwanakin nan da jama’a ke yi ba su dace ba.
''Ka ga an ce a fasa mota ko a fasa shago a diba, ba halal ba ne. A tausasa harshe a yi ma jama’a bayani wanda muke ganin shi ne ya kamata a yi,'' in ji shi.
Ya kara da cewa ba wai da wannan kiran suna kokarin rufe wa malaman baki ba ne, '' ‘yan Najeriya suna da ‘yancin su bayyana cewa suna shan wahala.''
A nasu bangaren mahalarta taron sun sha alwashin jaddada muhimmancin hadin kai a tsakanin al’umma.
Daya daga cikin malaman da suka halarci taron karkashin majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci ta Najeriya, Dakta Hamza Umar Assudany, wanda kuma shi ne babban limamin masallacin Juma’a na Al Babello da ke Zariya, ya ce za su fuskanci wa’azin watan azumin da ke tafe wajen karantar da al’umma yadda addinin Musulunci ya koyar da jama’a su yi a lokacin tsananin rayuwa.
Ya ce, ''ya za su yi su yi hakuri da halin da suke ciki da kuma bibiyar wasu hanyoyi da za su samu sassauci da kuma jawo hankalin wadanda za su iya taimaka musu su taimaka musu da kuma harkar abin da ya shafi tsaro da ya damu al’ummar kasa a fuskanci addu’a.''
Malamin ya kuma ce akwai bukatar jama’a su hada kai da jami’an tsaro ta yadda za a samu tsaro da zaman lafiya a tsakanin al’umma baki daya.
A game da yadda ake samun bambanci tsakanin malaman addinin Musuluncin ta yadda suke yi wa juna raddi kuwa, shugaban majalisar malaman jihar Kano Sheik Ibrahim Khaleel, ya ce akwai wasu hanyoyi da za bi domin magance hakan.
Ya ce, ''babban abin da mutane suke bukata tarbiyya, babu abin da ya kai tarbiyya, ilimi kashi talatin ne bisa dari amma tarbiyya kashi saba’in bisa dari.''
‘’ Na farko kowa ne abu za sus oka ko su ce ba daidai yake ba su yi bincike mai zurfi tukuna. Sannan na biyu su yi kokari su dinga yin hanzari a kan abin da ba su gama gane shi ba ko kuma wani ya aikata abin da su ba su fahimce shi ba, bai kamata su dinga garajen yin hukunci ba, ‘’ in ji malamin.
Sheik Ibrahim ya ce asali abin da ke janyo wannan matsala ma shi ne, karancin sanin tsarin ilimi da siyasar ilimi da kuma rashin tarbiyyar ilimi shi yake kawo hakan.
Baya ga wannan kuma ya ce,'' akwai mutanen da su ba malamai ba ne kuma su ce za su sa baki cikin maganar da ake.''