Abin da ya sa na dawo aikin shugabancin Hisbah - Daurawa

Shugaban hukumar Hisbah na jihar Kano, Malam Aminu Ibrahim Daurawa, ya sanar da cewa ayyukan hukumar za su ci gaba da gudana kamar yadda aka fara na gangamin kawar da baɗala da tsarkake jihar daga ɓata-gari.

Malam Daurawa ya yi wannan bayani ne jim kaɗan bayan sulhu tsakaninsa da gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf,.

Sheikh Daurawa ya sanar da yin murabus ne a ranar Juma'a bayan kalaman da gwamna Kabir Yusuf na kalubalantar yadda hukumar Hisbah ke gudanar da ayyukanta.

Amma a hirarsa da BBC bayan janye murabus ɗinsa, Daurawa ya ce shaiɗan ne ya shiga tsakani.

"An kawar da shaidan a tsakani an kuma fahimci juna kan manufar ayyukan hukumar da gwamnan na jihar Kano, inda ya ce wannan sabani tamkar taki ya karawa hukumar," in ji shi.

Ya ƙara da cewa gwamnati za ta ba su kudaden tafiyar da ayyukan ci gaba da gyaran tarbiyya a jihar.

''Abubuwan da aka fara su za a ci gaba da yi na tsaftace Kano daga badala, da gyaran tarbiyya da hukumar Hisbah ta dauko yi. Mai girma gwamna ya ce zai samarwa Hisbah kayan aiki da ba ta goyon baya a kan dukkan ayyukan alhairin da ake yi."

Shehin malamin ya ce gwamnati ba ta karbi takardar murabus dinsa ba, a yanzu kuma sun fahimci juna.

"Gwamna ya roke ni da na ci gaba da zuwa ofis, ya yi alkawarin ba mu hadin kai dari bisa dari, kuma na dawo bakin aikin shugabancin hukumar Hisbah in sha Allahu,'' in ji Daurawa.

'An ƙara zaburar da Hisbah'

Wasu dai na ganin abubuwan da suka faru a baya-bayan nan za su kawo cikas ga ayyukan hukumar Hisbah, kuma a matsayin Malam Daurawa na kwamandanta tamkar an sanya masa takunkumi ne.

Amma Daurawa ya musanta hakan, inda ya ce an ma karfafa hukumar ne, don haka ne ma suka fito da wani sabon tsari na kara tsaftace ayyukansu.

'Malamin ya ce hukumarsa ta ba 'yandaudu da karuwai da duk masu aikata baɗala wa'adin mako biyu, wanda yake son tuba ya zo ya tuba.

"Mun samar da wani fom mai suna na tuba da mutum zai cike. Za a koya ma sana'a da jari, idan ba dan jihar Kano ba ne za a mayar da shi garinsu, wanda kuma bai tuba ba y na ganin zai ci gaba da karya doka, to gara ya tattara kayansa ya bar Kano domin Kano ba matattarar badala ba ce.''

Daya daga cikin maganganun da gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi shi ne yadda ma'aikatan Hisbah ke gudanar da samamen kama masu aikata laifi da ya ce hakan bai dace ba ana dibarsu kamar awaki da rarakarsu da gora.

Kwamandan Hisbah ya ce za ta ci gaba da inganta ayyukanta, ta hanyar daukar matakan bai wa ma'aikatansu horo, inda ya ce ma'aikatun gwamnati ana samun kurakurai tare da ba da misali da kuskuren rundunar sojin Najeriya ta hanyar jefa bam kan masu mauludi a garin Tudun Biri na jihar Kaduna da ya haddasa mutuwar mutane da dama.

'Za mu kara inganta aikin ta fannin ilimi da kwarewa, za mu samar da sashen shari'a da na fasahar zamani da za a dinga tantance ayyuka da bibiyarsu. Kuma muna kokarin kafa makaranta mai suna Hizba Training School da za a dinga karatu na matakin NCE da Difloma, har da digiri a kan aikin Hisbah,'' in ji Sheikh Daurawa.

Gamayyar malaman addinin Musulunci ta jihar Kano ce suka sasanta gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf da Kwamandan Hisbah Malam Aminu Ibrahim Daurawa bayan rashin jituwar da ta kai ga ajiye aikin shugabancin hukumar.

Bayan wata ganawa da ta gudana a daren ranar Litinin a gidan gwamnatin jihar ta Kano, sakataren Gamayyar malaman, Dakta Sa'id Ahmed Dukawa, ya bayyana cewa sun shiga tsakani ne sanadiyyar kiraye-kiraye daga ciki da wajen jihar na ganin an warware matsalar.

A cewarsa, matsayar da aka cimma na nufin cewa a yanzu babu batun murabus din Sheikh Daurawa daga shugabancin Hisbah.

Dukawa ya ce: "Ya (Daurawa) dawo aiki, zai ci gaba da aikinsa".

A ranar Juma'ar makon da ta gabata ne Sheikh Aminu Daurawa ya sanar da saukarsa daga kan muƙamin na shugaban Hisbah.

Daurawa ya ce ya yi hakan ne bayan kalamai na kashe ƙwarin gwiwa daga gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf, amma gwamnan ya ce bai amince da ajiye aikinsa ba.