Bidiyon rawa: Sheikh Daurawa ya yi bayani

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya ya yi bayani game da wani hoton bidiyo da ake zargin shi ne a ciki yake rawa da matarsa a bainar jama'a.

Hoton bidiyon wani mutum da matarsa suna rawa a wurin wani biki ya yi ta yawo a shafukan sada zumunta, inda wasu ke zargin cewa Sheikh Aminu ne da iyalinsa.

A wani sako da ya fitar a shafinsa na Facebook daga kasar Saudiyya, Malam Aminu ya ce ba shi ba ne a cikin bidiyon, bai san mutumin da ke ciki ba, kuma bai san a inda aka yi ba.

"Tsakani da Allah wannan ba ni ba ne kuma ban ma san ko wanene ba. Watakila ina ga wasu kamanceceniya ne aka dan samu na kama tsakanina da wanda aka gani a wannan bidiyo," inji shi.

Fitaccen malamin ya yi bayanan ne bayan wasu daga cikin wadanda suka ga hoton rawar sun tura masa, suna kuma neman karin bayani daga wurinsa.

Hoton dai ya nuna wani mutum yana rawa da wata mata a wajen wani biki yayin da amaryar da ango suma su ke rawa a kusa da su.

A bidiyon, an ji mutane na suwwa da tafi a lokacin da mutumin ya shiga fagen rawar.

Masu amfani da shafukan sada zumunta musamman Instagram sun yi ta muhawara kan cewa Malamin ne ko mai kama da shi, inda wasu suke ganin ba zai yiwu Malam Daurawa ya yi rawa ba musamman ma a cakude da mata.