An tisa ƙeyar Murja Kunya da Ashiru da wasu 'yan TikTok biyu gidan yari

Babbar kotun Shari'ar Musulunci da ke jihar Kano ta tisa ƙeyar wasu fitattun matasa da ke ta'amali da kafar sada zumunta ta Tiktok gidan yari.

Matasan da suka haɗa da Murja Ibrahim Kunya da Aishiru Idris Mai Wushirya da Aminu BBC da Sheriff Sadiq Umar Mai Waƙar "A daidai ta nan", ana tuhumarsu ne da yin abubuwan da suka ci karo da tarbiyya da kuma al'ada.

A yayin zaman da aka yi a ranar Alhamis 16 ga watan Fabirairu, Mai shari'a Alƙali Abdullahi ne ya tisa keyar tasu gidan yarin na tsawon mako ɗaya kafin a fara sauraren ƙarar nan gaba a mako mai zuwa.

Baba Jibo Ibrahim shi ne mai magana da yawun kotuna a jihar Kano, ya kuma shaida wa BBC cewa wani mutum biyu ne aka kama a yanzu "Ashiru Idris Mai Wushirya da Sheriff Sadiq Umar".

"Murja Kunya aka fara kamawa a makon jiya, aka tura ta gidan gyaran hali, kuma a ranar Alhamis ɗin nan da aka dawo da ita kotu makonta ɗaya ke nan a gidan gyaran halin".

Ya ce bayan kwana biyu da kamata ne wani matashi mai suna Aminu BBC a manhajar da yake wallafa bidiyonsa shi ma ya naɗi wani sauti na zagin rashin kyautawa, kan kama matashiyar, wanda shi ma aka kama shi kimanin kwana hudu ko biyar baya.

Baya ga haka Malam Jibo ya ce Aminu BBC yana wallafa bidiyo na rashin ɗa'a da kuma suka ci karo da koyarwar addinin Musulunci.

Amma Sheriff Sadiq Umar waka ce ya yi wadda aka riƙa wallafawa a shafin na Tiktok kuma ake batsa ziryan a zahiri, shi ma an shigar da ƙararsa ne gaban wannan kotu kamar dai Murja.

Shi kuwa Ashiru Idris wanda aka fi sani da mai wushirya, abokin Murja Kunya ne, kuma sun jima suna yin bidiyo da hotuna tare.

Abubuwa tsakaninsu sun fara taɓarɓarewa lokacin da aka shigar da ita ƙara gaban kotu, wadda Barista Badamasi Sulaiman Gandu ya shigar, sai dai a wancan lokacin ba a samu tabbatattun hujjojin da za a riƙe ba domin yi mata hukunci.

Amma a yadda mabiya manhajar suka riƙa yaɗawa cewa Ashiru Mai wushirya da ƙawarta Aisha Najamu ne suka shigar da ƙara a kanta tare da gabatar da hujjojin da suka kai ga tisa keyarta gidan yari.

To a ƙarshe shi ma dai an tisa ƙeyar tasa gidan yarin kan tuhumar da aka yi masa na yin wasu bidiyo na batsa da ita Murjar kanta.

Matasa da dama dai suna amfani da wannan manhaja wajen wallafa abubuwan da suka ci karo da al'ada.

Yanzu dai kotun ta ɗage zamanta har sai nan da mako guda inda kuma nan ne za a fara sauraren ƙarar.

Baba Jibo ya ce "duka wannan zaman da aka yi an yi shi ne a matsayin tuhuma, kuma Asiru ya amsa laifinsa amma ita Murja ba ta amsa ba, ta musanta tuhumar".