Abu biyar game da Liliana Mohammed, Baturiyar da ta sauke Ƙur'ani a Kano

A farkon makon nan ne, hotunan wata dattijuwar Baturiya riƙe da allon saukar karatun al-Ƙur'ani mai zayyana, cikin shigar hijabi, suka karaɗe shafukan sada zumunta.

Mutane sun yi ta bayyana saƙonnin taya murna da fatan alheri ga Malama Liliana Mohammed, saboda wannan gagarumar bajinta da ta yi a rayuwa.

Ba a cika samun masu nisan shekarun da ke yin saukar Al-ƙur'ani ba.

To, ko wace ce dattijuwa Liliana Mohammed?

Ga abu biyar game da rayuwarta:

Asalinta

Ainihinta 'yar ƙasar Bulgaria ce, kuma aure ne ya kai ta Kano. A yanzu, Liliana tana da shekara 62 a duniya. Kuma in ji ta, abubuwa da yawa ne ke burge ta game da Kano, mazauninta na yanzu.

A cewar jaridar Daily Nigerian ta intanet, Baturiyar ta zo Kano ne fiye da shekara 30 a baya, sa'ar da ta auri wani ɗan kasuwa wanda Allah ya yi masa rasuwa yanzu, marigayi Ibrahim Sambo a can ƙasarta ta haihuwa Bulgaria.

Kuma dattijuwar tana 'ya'ya biyu.

Liliana Mohammed ta yi bikin saukar Kur'ani ne, tare da sauran ɗaliban makarantar Islamiyya ta Manba’irrahman a ranar Asabar, 2 ga watan Disamba.

Ta ce yanayi a birnin Kano, na da ƙarfafa gwiwar ayyukan ibada na addinin Musulunci, musamman idan ta kwatanta da ƙasar da ta fito.

"Ta fuskar lokaci. Lokutan sallah da na azumi sun dace matuƙa. Tsawon dare da na rana, kusan ɗaya ne. Ba kamar wani sashen na duniya ba, inda ake da sa'a biyar kawai a lokacin dare."

Ta ce shi kansa tsarin muhalli a Kano, yana da burgewa da ƙarfafa gwiwa. A lokacin kiran sallah, duk inda mutum yake zai ji, in ji Baturiyar. Kuma hakan, a cewarta abin ƙarfafa gwiwa ne, sannan ga mutane a ko'ina suna sallah a lokacin.

Babban abin farin ciki a rayuwa

Liliana Mohammed ta ce saukar karatun Alƙur'ani da ta yi, wani babban abin godiya ne da farin ciki a rayuwarta.

Ita ma, 'yar autar dattijuwar, Hamida Ibrahim Sambo ta ce sun yi matuƙar farin ciki da wannan cikar burin rayuwa na mahaifiyarsu.

A cewarta, shi ne muhimmin abin farin ciki da ya samu rayuwar 'yan gidansu.

"Haƙiƙanin gaskiya ma dai, shi ne abin da ya fi sanya mu farin ciki a duniya. Haihuwa, aure duk ba su kawo wannan farin cikin ba, irin na Musuluncin da ta karɓa."

Hamida ta ce mahaifiyarta sun yi rayuwa da mahaifinsu wanda ya riga mu gidan gaskiya kimanin shekara 13 da ta wuce, ba tare da ta karɓi Musulunci ba, sai da Allah ya yi masa rasuwa.

Ta yi ta maimaita kalmar godiya ga Allah. Tana cewa: "Alhamdulillahi! Ga shi yanzu tana iya ɗaukan Ƙur'ani ta yi karatunta".

Labarin saukarta

Ta ce ta shiga makarantar Islamiyya ta Manba'ir Rahman ne kimanin shekara goma da ta wuce, bayan ta karɓi Musulunci.

“Na fara karatu ne a gida, saboda yawan shekaruna.

"Mai koyar da ni Alƙur'ani, Malama Hafsa, tana zuwa gida ne ta biya mini. Mun fara ne daga farko, inda take min rubutu da haruffan boko, har zuwa lokacin da na fara gane haruffan Larabci.

“Ita ce ta ci gaba da koyar da ni karatun Ƙur'ani da haruffan Larabci, har na zo na fara iya karantawa da kaina."

Liliana ta ce daga nan, sai suka ci gaba, ana biya mata karatu aya zuwa aya, sura bayan sura har zuwa ran da ta yi sauka.

Tasirin karɓar Musulunci

Liliana Mohammed ta ce ɗaya daga cikin abubuwan da take alfahari da su game da karɓar addinin Musulunci a rayuwarta, shi ne samun kwanciyar hankali da nutsuwa.

Ta ƙara da cewa, Musulunci ya taimake ta wajen ƙara fahimtar abubuwa masu yawa a rayuwa.

Wani abin ban sha'awa da Liliana Mohammed ta ce ta fahimta game da Alƙur'ani mai girma da ta sauke, shi ne: "Yayin da kake karanta Ƙur'ani mai tsarki, shi ma Ƙur'ani yana karanta ka.

"Ina jin kwanciyar hankali da nutsuwa," in ji ta.

Karatun Hadda

Liliana Mohammed ta ce ba a gama ilmi a rayuwa. A kullum mutum yana sa burin ya kai, inda bai kai ba.

Ta ce don mutum ya gama makaranta, ba hakan yana nufin ya gama ilmi ba ke nan.

"Mutum yana ci gaba da koyo ne," in ji Liliana.

Ta kuma ce tana da burin ci gaba da karatu,

Duk da yake, ta ce tana ganin kamar shekarunta sun yi nisa ta iya haddace Ƙur'ani, "amma abu ne mai kyau mutum ya sa niyya".

Malama Liliana ta ce bayan mutum ya yi sauka, abu ne mai kyau kuma a mayar da hankali wajen sanin Tajwidi.