Yadda DPO ya lashe gasar karatun Al-Kur’ani a Kano

Shugaban ofishin ƴan sanda na ƙaramar hukumar Takai ya lashe gasar izu 60 ta karatun Al Kur'ani mai tsarki da rundunar ƴan sandan jihar Kano ta shirya.

DPO Mahi Ahmad Ali, ya zo na ɗaya ne a gasar ajin izu 60, inda ya samu kyaututuka da dama da suka hada da kuɗi da kayayyaki na amfanin yau da kullum.

Gasar wacce aka kammala a ranar Alhamis ita ce irin ta farko da rundunar ƴan sandan Kano ta gudanar ga jami'nta.

Ƴan sanda kusan 39 ne suka shiga musabaƙar ta Al Kur'ani ta kwana biyu kuma wadanda suka shiga musabaƙar sun samu kyaututuka daban-daban.

Kakakin rundunar ƴan sandan Kano Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce gasar ta ƴan sanda ce zalla kuma gasar ta ƙunshi izu biyu da izu biyar da 10 zuwa 20 da masu izu 40 da 60.

Sai dai gasar ta maza ce zalla ba mata amma rundunar yan sandan Kano ta ce saboda wannan ne karon farko, tana fatan a gaba za a ƙara shiri.

Game da wanda ya lashe izu 60

SP Mahi Ahmad Ali shugaban ƴan sanda mai kula da ƙaramar hukumar Takai da ke Kano shi ne wanda ya lashe gasar Al Kurani ta izifi 60.

Bayan lashe gasar ya yi godiya ga Allah inda ya ce wannan wata dama ce ta ƙara inganta karatunsa na Al Kur'ani.

"Aikina na ƴan sanda bai hana ni tilawar Al-Kur'ani ba," in ji shi.

Kadif Abubakar Abdullahi Usman daga kwalejin ƴan sanda ta Wudil ne ya zo na biyu a karatun izu 60 yayin da sufeto Ibrahim Abubakar da ke aiki a hedikwatar yan sanda da ke Bompai ya zo na uku.

Manufar musabaƙar ta ƴan sanda

Rundunar ƴan sandan ta ce an shirya musaɓakar ne da nufin zaburar da jami'an 'yan sandan Kano kan kyautata ayyukansu da gyaran mua'malarsu da al'umma, tare da ƙarfafa masu guiwa wajen neman ilimin addini. 

Sama'ila Dikko kwamishinan 'yan Sanda na jihar Kano, ya shaida wa BBC cewa manufar musabaƙar ita ce nunawa jama'a cewa su ma ƴan sanda ba a bar su a baya ba kan sha'anin ilimi musamman ilimin Al-Kur'ani.

"Al Kur'ani ne jagoran rayuwa da ke koya wa al'umma abubuwan da ke gudana da kuma ayyukan da mutane suke yi don mu kara ilimi yadda za mu tafiyar da aikin mu bisa amana da tsoron Allah da kuma gaskiya," in ji

Ya ce kuma an gayyaci malamai kda suka yi nasiha da jan hankali ga al'umma da ƴan sanda kan cewa manufar karatun shi ne don aiki da karatun Al Kur'ani a yayin da suke yi wa ƙasa hidima a koyarwa ta addinin musulunci.

Shiekh Abdulwahab Abdallah na ɗaya daga cikin malamam da suka albarkaci rufe gasar musabaƙar karatun Al Kur'ani yana mai cewa manuniya ce ta cewar an fara samun gyara a tsarin aikin ƴan sandan a Kano.

Ya ce tabbatar da amana ce hanyar da ƴan sandan suka kama a yanzu musamman idan sun riƙe Al Kur'ani.

Taron musabakar ya samu halartar sojojin sama da na ƙasa da jami'an hukumar tsaro ta kare fararen hula da na gyara hali da yan kasuwa da ke Kano.

Jihar Katisna ce ta fara gabatar da irin wannan musabaƙa ta karatun Al Kurani, sai kuma jihar Kano da ta yi a yanzu.

Rundunar ƴan sandan ta ce za ta ci gaba da gudanar da gasar duk shekara.