Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bidiyo: Yaro dan shekara 8 mai tafsirin Al-qur'ani
Latsa wannan hoton na sama domin kallon hira da malam
Muhammad Shamsuddeen ya zamo wani abin misali a duniyar Musulmi ta yau kasancewar yana daya daga cikin yara masu karancin shekaru da suke nuna bajinta a fagen ilmi.
Malamin mai shekara takwas da haihuwa ya ce ya fara makaranta ne bayan da aka yaye shi.
Muhammad ya ce duk da cewa ya yi makaranta amma ya samu karatu ne ta hanyar baiwa da kuma tallafin mahaifinsa.
Yanzu dai baya ga tafsirin al-qur'ani, Shamsuddeen ya sauke littafai kamar Kawa'idi da Ahlari da Risala da Ishamwiy da Mukhtasar da dai sauransu.
Malamin kan hau kujerar mahaifinsa ta bai wa manya karatu ko kuma tafsirin al-qur'ani mai girma a watan Ramadan.
Sai dai duk da cewa Muhammad Shamsuddeen ya zama shehin malami a fagen addinin Musulunci, burinsa shi ne kasancewa lauya a nan gaba.