Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kullum sai na yi magana da Bazoum - Shugaban Faransa
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya faɗa a ranar Juma'a cewa kullum sai ya yi magana da Bazoum Mohamed, hamɓararren shugaban Nijar, wanda sojoji suka tuɓe a wani juyin mulki.
"Kullum sai na zanta da Shugaba Bazoum. Muna goyon bayan sa.
Ba mu amince da 'yan juyin mulki ba, ba za mu martaba su ba. Duk shawarar da za mu cimma, ko ma waɗanne ne, za su kasance ne bisa zantawar da muke yi da Bazoum," a cewar Macron.
An wallafa waɗannan kalamai ne a shafin sada zumuntar fadar gwamnati Elysee kuma ya bayyana haka ne lokaci da yake jawabi game da harkokin ilmi a kudancin Faransa.
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin mulkin sojan Nijar ke cewa "ranta ya ɓaci" da kalaman Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, wanda a ranar Litinin ya nanata goyon bayan gwamnatinsa ga hamɓararren shugaban ƙasar, Bazoum Mohamed.
Mai magana da yawun gwamnatin Nijar ya bayyana lamarin da "tsabagen katsalandan".
Kalaman da Macron ya yi ranar Litinin, "ƙarin wani tsabagen katsalandan ne a harkokin cikin gida na Nijar," a sanarwar da Kanal Amadou Abdramane ya karanta ta talbijin a faɗin ƙasar.
Sanarwar ta ce "Kalaman Macron da kuma ƙoƙarinsa babu ƙaƙƙautawa na ganin an kai wa Nijar mamaya, wata manufa ce ta dawwamar da mulkin mallakar zamani a kan al'ummar Nijar, waɗanda su babu abin da suke nema sai a bar su, su zartarwa kansu makomar da za ta fisshe su."
Abdramane ya ce "bambancin" Nijar da Faransa ita ce "kada a taɓa kowa a kan dangantaka tsakanin mutanenmu ko a kan ɗaiɗaiku, amma a kan fa'idar kasancewar sojojin Faransa a Nijar."
Faransa na da dakarun soji kimanin 1,500 a Nijar, da yawansu an jibge su ne a wani sansanin sojojin sama da ke kusa da Niamey, babban birnin ƙasar.
An tura su ne don su taimaka wa ƙasar a yaƙin da take yi da miyagun 'yan ta-da-ƙayar-baya masu iƙirarin jihadi.
Tana fama da rikicin 'yan ta-da-ƙayar-baya guda biyu -- ɗaya wanda ya fantsama zuwa kudu maso gabashin Nijar daga rikicin da ya daɗe a Najeriya mai maƙwabtaka, da kuma masu iƙirarin jihadi a kudu maso yamma, waɗanda ke tsallaka wa cikin Nijar daga Mali da Burkina Faso.
A makon jiya ne dai, gwamnatin mulkin sojan ta bai wa jakadan Faransa a Nijar, Sylvain Itte sa'a 48 don ya fita daga ƙasar. Faransa dai, ta sa ƙafa ta shure umarnin, tana cewa sojoji masu mulkin Nijar ba su da iko a shari'ance na yin wannan kira.
Sojojin dai sun bayyana cire wa jakadan duk wata rigar kariya da alfarmar diflomasiyya, kuma sun umarci 'yan sandan Nijar su iza ƙeyarsa ya bar ƙasar.
Mai magana da yawun rundunar sojin Faransa, Kanal Pierre Gaudilliere, ya yi gargaɗi a ranar Alhamis cewa "dakarun Faransa a shirye suke su mayar da martani kan duk wata rikita-rikita a zaman ɗar-ɗar ɗin da ake ciki, matuƙar za ta iya cutar da harkokin diflomasiyya da na sojin Faransa a Nijar".
Motocin abincin agaji sun maƙale a kan iyaka
Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗi a kan yiwuwar shiga matsalolin jin ƙai a Nijar, bayan sabbin shugabannin mulkin sojin ƙasar sun dakatar da ayyukan hukumomin Majalisar, a inda suka kira yankunan da sojoji ke ayyuka na musamman.
Sojoji sun ƙwace mulki a ƙarshen watan Yuli a ƙasar mai fama da rikice-rikicen 'yan ta-da-ƙayar-baya.
Mutane sama da miliyan uku ne tun tuni ke fama da yunwa a Nijar, kuma tun bayan juyin mulkin an samu hauhawar farashi da kashi 20 cikin 100.
Majalisar ta ce tana ƙoƙarin tuntuɓar shugabannin juyin mulkin Nijar, bayan dakatar da ayyukan hukumominta da na sauran hukumomin ba da agaji.
Mai magana da yawun majalisar, Alessandra Vellucci ta faɗa wa manema labarai a Geneva cewa "Mun ga rahotanni.
Muna ƙoƙarin tuntuɓar hukumomi da ke mulki a Nijar don inganta fahimtar abin da hakan yake nufi da illolin hakan ga ayyukan jin ƙan ɗan'adam.
Kalamanta na zuwa ne bayan ma'aikatar harkokin cikin gida da maryacen ranar Alhamis ta ba da sanarwar cewa an dakatar da hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya da ƙungiyoyin ba da agaji da sauran hukumomin duniya daga aiki a yankunan da sojoji ke gudanar da ayyuka na musamman.
Sanarwar ba ta ce ga ayyukan da matakan suka shafa ba, amma ta ce an ɓullo da matakan ne "saboda yanayin tsaro da ake ciki a yanzu".
"Duk wasu aikace-aikace da kuma zirga-zirga a yankunan ayyuka na musamman an dakatar da su na wani ɗan wani lokaci," a cewarta.
Sabbin shugabannin mulkin sojan Nijar sun ƙwace iko a wani juyin mulki na ranar 26 ga watan Yuli, lokacin da dakarun soji suka hamɓarar da Shugaba Bazoum Mohamed.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato Majalisar Ɗinkin Duniya a ranar Juma'a tana cewa akwai tan 7,300 na kayan tallafin abincin da za a kai Nijar amma ya maƙale a kan hanya saboda rufe iyakokin ƙasar, yayin da ƙasar ta yankin Sahel ke fama da takunkumai masu alaƙa da juyin mulkin 26 ga watan Yuli.
Hukumomin majalisar sun kuma ce "fiye da mutum miliyan bakwai ne (kimanin kashi 28 na al'ummar ƙasar) ke cikin hatsarin auka wa matsalar yunwa saboda hauhawar farashi da toshewar hanyoyin neman abinci wadda rikicin siyasar da ke ci gaba ya haifar".