'Sojoji sun ce ba za su mayar da Bazoum kan mulki ba'

'Sojoji sun ce ba za su mayar da Bazoum kan mulki ba'

Babban mai shiga tsakani na ƙungiyar raya tattalin arziƙin yammacin Afrika (ECOWAS) domin sassanta rikicin Nijar, Janar Abdulsalami Abubakar ya shaida wa BBC cewa sojojin da suka hamɓarar da Shugaba Mohamed Bazoum sun ce a shirye suke su tattauna da ƙungiyar ECOWAS amma ba za su mayar da tsohon shugaban ƙasar a kan kujerarsa ba.

Ita dai ƙungiyar ECOWAS tana son sojoji su sauka daga kan mulki ba tare da ɓata lokaci ba sannan su mayar da Bazoum a kan mulki ko kuma a ɗauki matakin soji a kan su.

Cikin hira ta musamman da BBC Hausa, Janar Abdulsalami Abubakar ya bayyana cewa tattaunawar da suka yi da shugaban mulkin sojan Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani ta buɗe ƙofar samun maslaha a matsalar da ake ciki.

"Sojojin sun ce za su iya tattaunawa a kan komai da komai amma ba za su iya mayar da Bazoum a kan mulki ba," in ji Abdulsalami.

Wakilin na ƙungiyar ECOWAS ya bayyana cewa "sojojin sun yi roƙo a buɗe musu boda domin su sami magunguna da abinci sannan kuma a dawo musu da wutar lantarkin da Najeriya ta katse musu."

A kan batun yanayin da ake tsare da hamɓararren shugaba Bazoum yake kuwa, Janar Abdulsalami Abubakar ya ce "gaskiya ba ya cikin yanayi mai kyau saboda an yanke masa wuta. Na yi roƙo a mayar masa da wuta amma sojojin sun ce ba za su mayar masa da wutar ba har sai Najeriya ta maido wa da ƙasar lantarkin da ta katse mata."

Tsohon shugaban na mulkin soji a Najeriya ya kuma bayyana cewa yana fatan ba za a lalubo bakin zaren warware rikicin ba tare da an shiga yaƙi ba tsakanin ƙungiyar Ecowas da kuma dakarun Nijar.

A baya dai Shugaban mulkin sojin a Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani ya ce gwamnatinsu ba za ta wuce shekara uku a kan mulki ba.

Tuni ita kuma ƙungiyar ECOWAS ta yi watsi da wannan ikirarin da sojojin suka yi game da mayar da mulki kan tafarkin demokuraɗiyya.