Bazoum ya nuna ƙarfin hali da ya ƙi yin murabus - Faransa

Shugaba Emmanuel Macron ya faɗa wa wani taron jami'an diflomasiyya a birnin Paris cewa jakadan Faransa a Nijar har yanzu yana cikin ƙasar.

Yana ci gaba da zama a Nijar, in ji shi, duk da yake sojojin da suka ƙwace mulki a watan Yuli sun ba shi wa'adin sa'a 48 a ranar Juma'a don ya fice daga ƙasar.

Wannan mataki dai zai zafafa takun saƙar da ke tsakanin shugabannin mulkin soji a Nijar da kuma ƙasar ta Faransa wadda ta dage cewa ba ta yarda da halarcin mulkin soja ba.

Mista Emmanuel dai ya ce yana jin manufarsu tana kan daidai.

A cewarsa, matakin ya dogara ne a kan ƙarfin halin Shugaba Bazoum, da alƙawarin jakadunmu da ambasadanmu, wanda zai ci gaba da zama a Nijar, duk da matsin lamba kuma duk da haramtaccen iƙirarin karɓar mulki.

Shugaban na Faransa ya ce bai yarda da mulkin sojoji a Nijar ba kuma har yanzu ƙasarsa tana goyon bayan zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Nijar Bazoum Mohamed.

Ana dai ci gaba da tsare shi ne tun bayan kifar da gwamnatinsa a ƙarshen watan Yuli.

Manufarmu mai sauƙi ce, in ji Macron.

Ya ƙara da cewa: "Ba mu amince da masu juyin mulki ba. Kuma har yanzu muna goyon bayan Bazoum, wanda bai yi murabus ba, sannan mun yi alƙawarin ci gaba da mara masa baya".

Shugaban Faransa ya kuma ce ƙasarsa tana goyon bayan ƙoƙarin diflomasiyya na Ecowas da kuma matakin amfani da ƙarfin soja a duk lokacin da za a amince da shi a tsarin ƙawance.

Haka zalika, a ranar Asabar mai zuwa ne wa'adin da sojoji masu juyin mulki a Nijar suka bai wa dakarun sojin Faransa na tsawon wata ɗaya a kan su fice daga ƙasar zai cika.

Hukumomin Nijar dai sun bai wa dakarun sojin Faransa kimanin 1,500 da aka jibge a ƙasar ya zuwa 2 ga watan Satumba a kan su fice.

Makomar dakarun da ke aiki tare da sojojin Nijar tun a 2013 ne suke yaƙi da 'yan ta-da-ƙayar-baya masu iƙirarin jihadi - ƙungiyoyi na masu alaƙa da al-Qa'ida da kuma takwararta ta IS.

Tarayyar Turai a ranar Litinin ta bayyana "cikakken goyon baya" ga jakadan Faransa a Nijar, bayan sojojin da suka ƙwace mulki a ƙasar sun umarci ya fice.

"Shawarar masu juyin mulkin na korar jakadan Faransa, wata sabuwar takalar faɗa ce da ba za ta taimaka ta kowacce irin hanya ba a ƙoƙarin lalubo mafitar diflomasiyya ga rikicin da ake ciki," a cewar Nabila Massrali, mai magana da yawun Tarayyar Turai kan harkokin ƙasashen waje.

Ta ƙra da cewa Tarayyar Turai "ba ta yarda da" hukumomin da suka ƙwaci mulki a Nijar ranar 26 ga watan Yuli ba.