Gwamnatin riƙon ƙwaryarmu ba za ta wuce shekara uku ba - Tchiani

Shugaban mulkin soji a Jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani ya ce gwamnatinsu da ta hamɓarar da shugaba Mohammed Bazoum, ba za ta wuce shekara uku a kan mulki ba.

Janar ɗin ya bayyana haka ne a jawabinsa ga 'yan Nijar a kafar talabijin ranar Asabar da yamma.

Shugaban mulkin sojin kuma ya koka da takunkuman da ƙungiyar Ecowas ta ƙaƙaba wa ƙasar, yana cewa ta yaya za a hana shigar da magunguna cikin ƙasa a bar mutane na mutuwa a asibitoci?

"Ba za a tilasta mu amincewa da abin da ba mu yarda da shi ba," in ji Tchiani.

Ya ƙara da cewa "waɗannan takunkumai sun saɓa wa aƙida da manufar kafa ƙungiyar ta Ecowas ko CEDEAO na yancin kai-komon jama'a da dukiyoyinsu".

Shugaban sojin ya ce yana tunanin ƙungiyar Ecowas, ba ta auna illar da harin soji zai haddasa a yankin ba.

Tchiani ya ce ƙungiyar ta manta cewa jajircewar sojojin Nijar ce ta hana yankin Afirka ta Yamma aukawa cikin yanayin rashin tabbas.

Ganawar tawagar Ecowas da Bazoum

Tawagar Ecowas ta musamman da ta ziyarci Nijar ta samu ganawa da hamɓararren shugaban ƙasar, Mohamed Bazoum da shugabannin mulkin sojin ƙasar, a wani yunƙuri na maido da hamɓararren shugaban ƙasar kan karagar mulki.

Tawagar masu shiga tsakanin - ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban Najeriya janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya da Mai alfarma Sarkin Musulmin Najeriya, Muhammad Sa'ad Abubakar lll - ta samu ganawa da shugaban mulkin sojin Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani.

Ziyarar masu shiga tsakanin na zuwa ne kwana guda bayan manyan hafsoshin tsaron ƙasashen Ecowas sun ce sun saka ranar auka wa Nijar da yaƙi, matuƙar sojojin ba su mayar da bazoum kan mulki ba.

Sojojin mulkin sun tattauna da tawagar Ecowas ɗin a birnin Yamai, to sai dai ba su yi bayani a kan abubuwan da suka tattauna ba.

Tattaunawar na zuwa ne a daidai lokacin da ake ɗaukar dubban 'yan sa-kai a Nijar domin kare ƙasar daga farmakin Ecowas.