Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Newcastle na son sesko, Arsenal na nazari kan Gyokeres
Newcastle United ta gabatar da tayin fam miliyan 65.3 kan ɗan wasan Slovenia da RB Leipzig, Benjamin Sesko mai shekara 23. (Sky Sports)
Manchester United na tattaunawa ita ma da Sesko, wanda har yanzu bai yanke hukunci ba kan zaɓin tafiya Manchester United ko Newcastle. (Fabrizio Romano)
Liverpool za ta sake gabatar da tayi kan ɗan wasan Sweden Alexander Isak mai shekara 25, idan Newcastle ta samu mai maye gurbinsa.. (Daily Mail)
Arsenal na nazari kan Isak kafin ta cimma yarjejeniya da Viktor Gyokeres amma tana nuna shaku kan ɗan wasan gaban a Newcastle. (ESPN)
Ɗan wasan gaba a Koriya ta Kudu Son-Heung Min mai shekara 33, ya amince ya koma LAFC bayan yanke hukuncin barin Tottenham. (GiveMeSport)
An kammala duba lafiyar ɗan wasan baya a Netherlands Jorrel Hato mai shekara 19 a Chelsea kan cimma yarjejeniyar fam miliyan 35.5 a kansa. (Sky Sports)
Manchester United na shirin gabatar da tayin fam miliyan 16 kan ɗan wasan Barcelona da Sifaniya mai shekara 22, Fermin Lopez. (Sport - in Spanish)
AC Milan na tattaunawa ɗan wasan Liverpool da Uruguay, Darwin Nunez mai shekara 26, kan komawarsa San Siro amma kuma akwai Al-Hilal da take zawarcinsa ido rufe. (Sky Sports Italia - in Italian)
Crystal Palace ta gaza a cimma yarjejeniyar fam miliyan 28 kan ɗan wasan Inter Milan da Jamus, Yann Bissek mai shekara 24. (Gazzetta Dello Sport - in Italian, external)