Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa Liverpool ke kashe maƙudan kuɗi duk da ɗaukar kofi a bara?
Yayin da har yanzu ake da wata guda cif kafin rufe kasuwar saye da musayar 'yanƙwallo a Ingila, tuni zakarun gasar Premier League Liverpool suka zarce kowa wajen cefano 'yanwasa.
Ita ce ta ɗauki ɗanwasan Jamus daga Bayer Leverkusen, Florian Wirtz, kan fan miliyan 116, adadi mafi yawa kenan da aka kashe kan wani ɗanwasa a tarihin ƙwallon Ingila.
Ga kuma Hugo Ekitike ɗan Faransa da ta ɗauka kan fan miliyan 69, wanda tsarabe-tsarabe za su sa ya kai har miliyan 79.
Hakan ya sa ta zama ta shida a jerin kulobkulob ɗin da suka fi kashe kuɗi a zangon kasuwa ɗaya a faɗin duniya.
Idan Liverpool ta iya sayen Isak daga Newcastle kan fan miliyan 135 ko sama da haka, kenan ƙungiyar ta Arne Slot za ta zama kan gaba wajen kashe kuɗi a kasuwa ɗaya a duniya.
Ƙwararre a fannin harkokin kuɗi na wasanni, Kieran Maguire, ya ce: "Kuɗin da Liverpool ta kashe a kasuwar bana ya sa ta zama ta 48 a duniya wajen kashe kuɗi a tarihi.
"Ko da sun iya sayen Isak kan fan miliyan 140 ba za su wuce mataki na 12 ba."
Wani zai ce me ya sa ƙungiyar ke kashe kuɗi da yawa wajen cefane a yanzu duk da cewa ita ce mai riƙe da kofin a yanzu?
Wannan kashe kuɗi da Liverpool ke yi na nufin ƙungiyar na son ta kafa sarauta a gasar Premier League irin wadda Manchester United ta kafa, inda ta dinga cin kofin gasar babu ƙaƙƙautawa daga 1992 zuwa 2012, inda ta ɗauki 13 jimilla.
Kafin ta ɗauki kofin gasar a kakar 2019-20, sai da Liverpool ta shekara 30 ba ta ci kofin ba. Sake ɗaukar kofin a yanzu na nufin idan ta dage za ta iya mamaye gasar kamar yadda Manchester City ta yi, inda ta lashe shida cikin shekara tara ƙarƙashin Pep Guardiola.
'Yanwasan da Liverpool ta ɗauka zuwa yanzu
- Florian Wirtz – kan £100m daga Bayer Leverkusen (zai iya zama £116m)
- Hugo Ekitike – kan £69m daga Eintracht Frankfurt (zai iya zama £79m)
- Milos Kerkez – kan £40m daga Bournemouth
- Jeremie Frimpong – kan £29.5m daga Bayer Leverkusen
- Giorgi Mamardashvili – kan £25m daga Valencia (zai iya zama £29m)
- Armin Pecsi – kan £1.5m daga Puskas Akademia
- Freddie Woodman – daga Preston North End
Waɗanda suka bar Anfield:
- Luis Diaz – zuwa Bayern Munich a kan £65.5m
- Jarell Quansah – zuwa Bayer Leverkusen a kan £30m (zai iya zama £35m)
- Caoimhin Kelleher – zuwa Brentford a kan £12.5m (zai iya zama £18m)
- Trent Alexander-Arnold – zuwa Real Madrid a kan £8.4m
- Nat Phillips – zuwa West Brom a kan £1m (zai iya zama £3m)
Me Arne Slot ke ƙullawa?
Yayin da yake da Florian Wirtz a tsakiyar fili, ga kuma sababbin 'yanwasan baya na hagu da dama, samuwar ɗanwasan gaba Hugo Ekitike na nuna sabon salon taka leda da mai horarwa Arne Slot ke shirin aiwatarwa.
A kakar wasa ta 2024-25, Mohamed Salah ne ya ci ko ya bayar aka ci wa Liverpool ƙwallo 47 cikin 86 (kashi 55 cikin 100 kenan), wanda ke bi ta ɓangaren dama da kuma rakiyar Alexander-Arnold.
A gefe guda kuma, sabon ɗanwasan baya Jeremie Frimpong yana da yawan kai hari. Hakan zai rage wa Salah wahalar aikin, amma kuma zai iya sakawa ɗan ƙasar Masar ɗin ya ɗan matsa zuwa tsakiya kaɗan domin tallafa wa sabon mai ƙirƙirar wasa Wirtz.
Ganin irin yadda Ekitike ya saba taka leda a fannin cin ƙwallo bisa haɗin gwiwa da wani, ana iya cewa salon zai iya yin aiki da kyau. Ya fi jin daɗin buga wasa a salon 3-5-2 a lokacin da yakle Frankfurt.
Haka nan, a mafi yawan lokaci yakan buga taka leda bisa dogaro da tamkaon wani ɗanwasan a kulob ɗin Reims, inda ya yi suna.
Ko shin Slot zai ƙirƙiri wani abu mai kama da hakan tsakanin Salah da Ekitike? Akwai yiwuwar hakan.
Bugu da ƙari, a salon 4-2-3-1 kuma, salon kai hari irin na Frimpong daga gefen dama zai iya bai wa Salah damar kwararowa tsakiyar fili a matsayin wani ɗan karamin mai jefa ƙwallo a raga tare da Ekitike, sai Wirtz da wani ɗan tsakiyar su dinga kasancewa a bayansu.