Miliyoyin yara na cikin barazana saboda ƙin yarda da riga-kafi a duniya

A young baby wrapped in a blue blanket receives a vaccination in Senegal in 2024

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Dominic Hughes
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin Lafiya
  • Lokacin karatu: Minti 3

Yawan rigakafin da ake yi wa ƙananan yara na wasu munanan cutuka ya ragu cikin shekara 20 da suka wuce - har ma lamarin ya samu koma-baya a wasu ƙasashen - kamar yadda wani binicke ya gano.

Annobar korona ce ta ƙara ta'azzara lamarin, inda ta jawo miliyoyin yara suka kasa samun allurar rigakafin cutuka kamar ƙyanda, da tarin fuka, da kuma shan'inna.

Masu bincike na neman a mayar da hankali wajen samar da cikakkiyar damar samun alluran ga yara.

Masana harkokin lafiyar yara sun yi gargaɗin cewa rage tallafin da ƙasashen duniya ke bayarwa kan rigakafi, da kuma ƙyamar rigakafin, suna jawo "babbar matsala".

Shirin na yi wa yara rigakafi na duniya ya yi nasara sosai.

Tun daga shekarar 1974, fiye da yara biliyan huɗu aka yi wa rigakafi domin kare mutuwar mutum miliyan 150 a duniya.

Cikin shekara 50 har zuwa 2023, masana na cewa yawan yaran da ke samun rigakafin sun ninka.

Amma tun daga 2010 aka fara samun raguwar, har ta kai an fara samun giɓi mai yawa a wasu ɓangarori na duniya.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wani binicike da aka wallafa a jaridar The Lancet ya ce rigakafin ƙyanda ya ragu kusan a ƙasashe 100.

Zuwa 2023, akwai kusan yara miliyan 16 da ba a yi wa rigakafi ba saboda annobar korona, kuma akasarinsu suna yankin kudu da hamadar Saharar Afirka da kudancin Asiya.

Marubucin binciken Dr Jonathan Mosser na cibiyar Institute for Health Metrics and Evaluation a Jamia'r Washington da ke Amurka, ya ce har yanzu akwai yara masu yawa da ba su samu ba kuma ba su samun rigakafin.

"Rigakafin da aka saba yi wa yara na cikin mafiya tasiri kuma masu amfani a fannin shirye-shiryen lafiya da ake da su, amma kuma saboda rashin daidaito, da ƙalubalen cutar korona, da labaran ƙarya game da rigakafin, da ƙyamar da ake nuna kan allurar, duka sun taimaka wajen kawo matsala," a cewarsa.

Dr Mosser ya ce akwai ƙaruwar barazanar ɓarkewar annobar cutuka kamar ƙyanda, da shan'inna, da mashaƙo.

Ya ƙara da cewa ya kamata kowane yaro ya samu rigakafi. Sai dai har yanzu akwai rashin daidaito mai yawa a ƙasashe masu tasowa.

Amma marubutan binciken sun yi gargaɗi cewa an rage yawan rigakafi a nahiyar Turai, da Amurka da sauran ƙasashe masu arziki.

Farfesa Sir Andrew Polland, shugaban cibiyar Oxford Vaccine Group, ya ce abin da suka gano abin damuwa ne.

"Ƙarin yara za su kwanta a asibiti, kuma za su fuskanci jinya ta har abada saboda cutukan da za a iya karewa idan har ba a ɗauki matakin magance matsalar ba.

"Sai dai ma, raguwar kuɗaɗen tallafi daga ƙsashen duniya za ta ta'azzara matsalar ne," in ji Farfesa Pollard.

Dr David Elliman na jami'ar University College London ya ce akwai abubuwa da yawa da suka haifar da matsalar da ake ciki.

"A faɗin duniya duka, ƙasashen da suka shiga wani hali saboda yaƙi da kuma rage kuɗaɗen tallafi da ƙasashe suka janye, hakan ya jawo wahalhalu wajen kai rigakafin wasu yankuna," in ji shi.

"Wuraren da kuma alamu suka nuna ana yin wasu dokoki bisa son zuciya maimakon ilimi, akwai matsala mai yawa," kamar yadda Dr Elliman ya bayyana.

Masu binciken sun bayar da shawarar cewa ya kamata duka ƙasashe su ƙarfafa ɓangaren kiwon lafiya a matakin farko kuma su yaƙi labaran ƙarya game da rigakafi da ke hana iyaye kai yaransu.

Kuma sun nemi a haɗa gwiwa wajen samar da damarmaki masu yawa da za su taimaka wajen samar da alluran a duniya.