'Yara miliyan ɗaya za su iya mutuwa idan Amurka ta dakatar da tallafi'

Gavi ta ce yara miliyan 500 na buƙatar allurar rigakafi a duniya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Gavi ta ce yara miliyan 500 na buƙatar allurar rigakafi a duniya
    • Marubuci, Dorcas Wangira
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa health correspondent
  • Lokacin karatu: Minti 3

Wata cibiyar lafiya ta duniya ta yi gargaɗin cewa ƙananan yara miliyan ɗaya za su iya mutuwa a sanadiyar cututtuka da za a iya karewa, idan har Amurka ta dakatar da tallafin da take bayarwa.

Dokta Sania Nishtar - shugabar cibiyar ta Gavi da ke kula da saye tare da rarraba rigakafi a ƙasashen duniya - ta shaida wa BBC cewa idan Amurka ta dakatar da tallafin da take bayarwa, za a samu "matsala babba a ɓangaren kiwon lafiya a duniya."

Wannan na zuwa ne bayan wani rahoto na jaridar New York Times, inda a ciki aka bayyana cewa gwamnatin Trump za ta dakatar da tallafin da take bai wa Gavi - Amurka ce ƙasa ta uku wajen bai wa Gavi tallafi mai nauyi.

Har yanzu dai Gavi ba ta samu takardar dakatar da tallafin daga Amurka ba, amma a yanzu haka, "tana kan tattaunawa ne domin samun tallafin dala miliyan 300 domin ayyukanta na shekarar 2025, da kuma kuma wasu kuɗaɗe da take buƙata domin wasu da za a daɗe ana yi," in ji Dokta Nishtar.

Amurka ta yi alƙawarin bai wa Gavi dala biliyan 1.6 domin ayyukanta na tsakanin 2026-2030 - kusan kashi 15 na kuɗaɗen da cibiyar ke buƙata a shekarun ke nan.

Tun bayan ɗarewarsa karagar mulki a watan Janairun 2025, Donald Trump ya bayyana cewa zai dakatar da wasu tallafi da ƙasar ke bayarwa.

Hukumar USAID ce ta farko, inda sashen kula da ayyukan gwamnati, ƙarƙashin Elon Musk ya ba Trump shawarar janye tallafin hukumar.

Tuni dai Amurka ta dakatar da dukkan agajin da take bayarwa a ƙasashen waje na kwana 90.

Daga cikin yara miliyan 500 da ke buƙatar rigakafi a ƙasashen duniya, miliyan 75 ba za su samu ba, idan Amurka ta dakatar da tallafin da take ba Gavi, in ji Dokta Nishtar.

Ta ce hakan na iya zama sanadiyar mutuwar yaran da dama a sanadiyar cututtuka da za a iya kiyaye irin su tarin fuka da polio da sauransu.

Ta ƙara da cewa ƙoƙarin da gwamnati da cibiyoyin lafiya na duniya ke yi wajen tabbatar da kiwon lafiya ta hanyar allurar rigakafi ga cututtuka irin ru Ebola da cholera da mpox zai samu tsaiko.

Ita kuma ƙungiyar ma'aikatan jinya ta Médecins Sans Frontières (MSF) ta amince da matsayar ta Gavi.

"Illar da wannan matakin na siyasa za ta haifar na da yawa," in ji shugaban ayyukan MSF a Amrka, Carrie Teicher.

Dr Sania Nishtar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dr Sania Nishtar ta ce Gavi cibiya ce da take aiki tuƙuru

Cibiyar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa da Afirka, ta ce "tana goyon bayan Gavi, kuma "tana tattaunawa" da hukumomin Amurka kan illar da dakatar da tallafin za ta haifar, in ji shugaban sashen ceton gaggawa na cibiyar, Dr Ngongo Ngashi.

Dr Ngashi ya ce "yana matuƙar muhimmanci mu fara lalubo hanyoyin ɗaukar nauyin ayyukanmu."

Gavi dai ta ce za ta fara nemo wasu hanyoyin samun tallafinta daga wasu. Indonesia, ɗaya daga cikin ƙasashen da ke karbar tallafin rigakafi daga Gavi, a bana ita ce ta ba cibiyar gudunmuwa.

BBC ta tuntuɓi sashen kula da harkokin wajen Amurka, wanda ke kula da sauran kuɗaɗen USAID domin jin ƙarin bayani.

Ƙarin bayani daga Nkechi Ogbonna.