Me dokokin Najeriya suka ce kan tsare ƙananan yara a kurkuku?

Wani mutum a gidan yari

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

Ana cigaba da tattaunawa tare da neman ƙarin bayani kan batun kamawa da tsare ƙananan yara a gidajen gyara hali a Najeriya, lamarin da masana suke cewa ya saɓa wa dokokin ƙasar.

A ranar Alhamis ne aka wayi gari da wasu labarai da ke nuna cewa Ministan Harkokin Cikin Gida Najeriya, Olubunmi Tunji-Ojo, yana cewa akwai yara ƙanana da ba za su gaza 26,000 a gidajen yarin Najeriya ba, wanda ake hasashen kusan kashi 30 ke nan na fursunonin ƙasar.

Kafofin yaɗa labarai sun ruwaito ministan na nuna damuwa game da lamarin, wanda ya bayyana da "lamari mai ban takaici da damuwa", sannan ya buƙaci a gaggauta aiwatar da wasu gyare-gyare domin kula da ƙananan yara da sauran masu rauni.

A wata sanarwa da daraktan watsa labarai na ma'aikatar harkokin cikin gidan, Ozoya Imohimi ya fitar, ya ce adadin yaran da suke zaman kason sun yi yawa, kuma bai kamata hakan na faruwa ba.

"Ajiye yara ƙanana a gidajen yari cakuɗe da manya masu laifi, ko masu jiran hukunci ya saɓa da dokokin gudanar da gidan gyara hali na Najeriya," in ji ministan kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Ya ƙara da cewa za su gudanar da bincike "domin gano gaskiya da ma musabbabin ajiye yaran" da zimmar rage yawan yaran da suke zaune a gidajen yarin.

Me doke ta ce kan tsare ƙananan yaran?

Kotu

Akasarin ƙasashen duniya na da tanadi game da yadda ake tuhuma da kuma tsare ƙananan yara, ciki har da Najeriya.

Kakakin gidajen yari na jihar Kano da ke arewacin Najeriyar, CSC Misbahu Lawal Ƙofar Nasarawa, ya faɗa wa BBC cewa suna da tsari na musamman domin ƙananan yara.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Akan samu yara waɗanda ake tsare da su, amma muna kiran inda ake ajiye su ɗin ne 'borstal institutions' wato gidaje ko makaranta ta musamman da ake kula da karatunsu da makamantansu," in ji shi.

Sai dai ya ce babu makarantun da yawa a Najeriya.

"A Najeriya baki ɗaya, yanzu a jihohi uku ne kacal ke da waɗannan makarantun: Kaduna, da Kwara, da Ogun," kamar yadda ya bayyana.

"Kuma sabuwar dokarmu ta bayar da damar cewa lallai ne a gina irin wannan makaranta a kowace jiha. Yanzu haka mu a nan Kano za mu yi wasu gyare-gyare.

"Gidan yarin Kurmawa zai tashi ya koma Janguza. Sai ita Kurmawar ta koma makarantar ta 'borstal Institutions' domin kula da yara ƴan ƙasa da shekara 18 ɗin."

Da BBC ta tambaye shi sahihancin alƙaluman ƙananan yaran da suke zaman kaso, ya ce ai "alƙaluma ne na ƙasa, kuma ka san a doka ko sunan irin waɗannan yaran ba ma a kira a makarantunmu, sai dai a yi amfani da lamba".

"Ana haka ne domin kare su daga fuskantar ƙyama a nan gaba bayan sun fito, kuma ba a san me za su zama ba a nan gaba a rayuwarsu," a cewarsa.

CSC Misbahu ya ce su kansu suna fuskantar ƙalubale tsakaninsu da kotu.

"A al'adar Bahaushe, yadda ake gane yaro ya balaga ko ya girma daban, mu kuma a doka ba wannan tsari muke bi ba. Za ka ga kotu ta kawo mana yaro ta ce shekarunsa kaza, mu kuma likitocinmu idan sun gwada, sai su ce ba haka ba.

"Ba ma karɓar su a nan Kano. Idan aka kawo mana su, akwai abin da ake kira remand home waɗanda a ƙarƙashin jihohi suke, can muke tura su a riƙe su."

Me ya kamata a yi?

Domin jin me kamata a yi, lauya mai zaman kansa, Farfesa Muhammad Hilal a jihar Sokoto ya ce tsare yara a gidajen kaso ya saɓa ƙa'ida.

"Akwai tanade-tanade da aka yi na shari'a domin ƙananan yara, kuma ana kuskure ne tun a lokacin bincike. Tun a lokacin bincike ne ya kamata a tantance waɗanda shekarunsu ba su kai ba. Ko kotun ma akwai 'juvenile court' da ya kamata a dinga kai yara."

Ya lissafa wasu hanyoyi da yake tunanin za su yi kyau domin hukunta ƙananan yara;

  • Tara
  • Aikatau na al'umma
  • Yarjejeniya (plea bargain)

Ya ce ya kamata hukumomi, musamman na gayra hali su tanadi tsare-tsare na cikin gida, "domin karɓar yara, sannan su mayar da su inda ya dace a tsare su," in ji lauyan.

"Zai yi kyau ma'aikatar shari'a ta yi kwamitin aiwatar da hakan, sannan ya kamata a ce akwai sashe na musamman da ke lura da wannan. Idan yaro yana da laifi ko ana tuhumar sa da laifi, sai a duba abin da ya fi dacewa."