Tsohon gidan yari tilo a duniya da ake 'kulle 'yan luwaɗi zalla'

Cooma jail

Asalin hoton, The Greatest Menace

Bayanan hoto, Gidan Yarin Cooma ya kasance na garƙame 'yan luwaɗi kaɗai
    • Marubuci, Gary Nunn
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Sydney

Gidan yarin da aka gina a gari mafi sanyi da iska na ƙasar Australia, Cooma na ƙunshe da rufa-rufa mai muni.

Ba sake buɗe shi kawai aka yi a 1957 ba don a dinga kulle masu aikata laifukan luwaɗi, an ce an yi amfani da shi a matsayin wani wurin gwaji da zimmar kawo ƙarshen ɗabi'ar luwaɗi a cikin al'umma.

An yi imanin cewa Gidan Yarin Cooma ne kaɗai aka sani da ake garƙame 'yan luwaɗi a faɗin duniya, a cewar wani sabon shirin sauti na podcast.

Har zuwa yanzu, wasu daga ma'aikatan gidan yarin kan ce sun kasa fahimtar dalilin da ya s aake nuna wa 'yan luwaɗi wariya a wurin.

Les Strzelecki mai shekara 66 ya fara aiki da gidan yarin a matsayin jami'i a 1979, kuma daga ba ya kafa sashen tarihi na Corrective Services Museum a Cooma. Ya bayyana cewa yana ganin ana tura 'yan luwaɗi wurin ne don kare rayuwarsu.

"Cooma cibiyar ba da kariya ce. Muna buga wa 'yan luwaɗi sitamfi da cewa 'N/A' wato non-association da ke nufin ware su daga sauran fursunoni," kamar yadda ya faɗa wa BBC. "Sun kasance cikin haɗarin shiga tashin hankali."

Sai dai wani tsohon ma'aikaci, Cliff New, ya yi iƙirarin cewa ba haka abin yake ba. Ya faɗa wa shirin podcast mai suna The Greatest Menace cewa ƙwararru kan tunani da lalurar ƙwaƙwalwa "sun sha zuwa a kodayaushe" bayan sake buɗe bursin ɗin a 1957.

Yana ganin ana yin hakan ne da zimmar sauya su: "Suna ƙaƙarin su mayar da su kan hanya "madaidaiciya"...Sun yi imanin cewa za su iya warkar da su."

Kuma dalilin da ya sa kenan ake tsare fursunoni a ɗakuna daiɗai, a cewarsa. "Ba za a haɗa biyu a wuri ɗaya ba...ɗaya daga cikin manyan matsalolinmu kenan - sanya ido a kansu," a cewar Mista New wanda yanzu ke da shekara 94.

Les Strzelecki

Asalin hoton, Thomas McCoy

Bayanan hoto, Les Strzelecki (hagu) ya yi aiki a gidan yarin kafin ya kafa sashen tarihi da nufin kawo gyara na Corrective Services Museum

Wasu takaradun tarihi sun nuna cewa Ministan Shari'a na New South Wales (NSW), Reg Downing, na alfahari da kafa gidan yarin.

An ruwaito cewa ya nuna "alfaharinsa" game da abin da ya samar, yana mai faɗa wa jaridar Sydney Morning Herald a 1957: "Ban taɓa ganin gidan yari a Amurka ko Turai ba inda ake ware 'yan luwaɗi da sauran fursunoni."

Wata sanarwa a 1958 daga Mista Downing ta ayyana Comma a matsayin gidan yari "ɗaya tilo da ke matsayin mahukunta a faɗin duniya da aka ware kawai saboda a tsare masu aikata laifin luwaɗi".

Ana tsare fursunoni a Cooma saboda kasancewarsu 'yan luwaɗi, ko wasu laifuka masu alaƙa da luwaɗi: ba a haramta luwaɗi ba a NSW har sai a 1984.

Wata sabuwar doka a 1955 ta nemi kawo ƙarshen 'yan luwaɗi. Hakan ya biyo bayan matsin lamba daga kwamashinan 'yan sanda na lokacin, Colin Delaney, wanda a cewar antoni janar, ya ji cewa "dokar ta neman gyara wani yunƙurin gaggawa ne na kawo ƙarshen shaiɗanci".

"Sabbin tanadin dokar sun ƙunshi kama mutum ko da kuwa hira kawai ya yi da wani namiji," a cewar masanin tarihi Garry Wotherspoon cikin hirarsa da BBC.

Ana hukunta laifin jima'i ta baya da shekara 14 a gidan yari. Yunƙurin jima'i ta baya kuma shekara biyar ne, amma a wata tsattsaurar doka da aka ƙara, an ce "ko da izinin ɗaya mutumin ko babu izininsa".

Reg Downing

Asalin hoton, State Library of NSW

Bayanan hoto, Reg Downing ya bayyana alfaharinsa kan ware 'yan luwaɗi da sauran fursunoni

"Sukan yi amfani da wasu 'yan sanda don su ɗana wa mazaje tarko inda suke tunzura su su yi jima'i akasari banɗakin gine-ginen kasuwanni," a cewar Mista Wotherspoon.

A 1958, gwamnatin NSW ta kafa kwamatin bincike kan "abin da ake yi wa 'yan luwaɗi".

Ta bayyana gidan yarin Cooma a matsayin "wata cibiya ta ɗaurarrun 'yan luwaɗi" wanda zai sa "a gudanar da binciken".

Cooma from above

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Cooma gari ne na mutum kusan 7,000

Babu tabbas game da lokacin da aka daina tura mutane Cooma. "An lalata abubuwan tarihi da dama," in ji Mista Wotherspoon.

Hukumomin NSW sun ƙi yarda su ce komai game da zarge-zargen.

Abboud ya yi imanin cewa an ci gaba da tura 'yan luwaɗi zuwa Cooma har zuwa farkon shekarun 1980, yana mai ambato wata sanarwa daga ministan gidajen yari.

2px presentational grey line