Lalurorin da za a iya haihuwar yara da su sanadiyyar auren zumunci - Bincike

- Marubuci, Luke Mintz
- Marubuci, Sue Mitchell
- Lokacin karatu: Minti 8
A wani gida mai mutane da yawa a Bradford na ƙasar Birtaniya, wasu mata uku ƴan‘uwa na ta hira.
Rana ce mai muhimmanci a iyalinsu: wata mai gyaran jiki na zaune kan kujera tana gyara musu gashi tana musu kwaliyya. Ɗakin na cike da annashuwa da raha. Yanayin ya yi kama da wani yanayi daga cikin littafin Austen.
Kuma kamar akasarin litattafan Austen, hirar tana komawa ga aure ne.
Ƴan‘uwan suna shirin wani biki cikin iyalinsu a ƙarshen mako - bikin da amarya da angon ƴan‘uwa ne.
Wasu da dama za su yi mamakin hakan, sai dai a iyalinsu da ma wasu yankuna a Bradford, hakan ba abin mamaki ba ne.
Ayesha, ƴar shekara 29 ita ce babba cikin ƴan‘uwan mata uku, ita ma ta auri ɗan uwanta na kusa a shekarar 2017. Tana da yara biyu da mijin nata kuma suna cikin farin ciki a auren nasu, in ji ta.
A lokacin ba ta ji wani abu daban ba kan auren ɗan‘uwanta.
Mahaifiyarsu, ƴar Pakistan da ta yi hijira, ta yi tunanin cewa dukannin ƴaƴanta za su yi hakan.
Sai dai Salina mai shekara 26, ƙarama cikin ƴan‘uwa matan, ta shaida mana cewa ta saɓa wannan tsarin ta hanyar yin abin da su ke kira auren 'soyayya', inda ta zaɓo miji da ba ɗan‘uwansu ba ne.
Salina ta ce mana tana da buruka da ra'ayoyin kanta, a cewar ta, auren zumunci ba ya burge ta.
Sannan kuma akwai Mallika, ƴar shekara 27 wadda ita ce a tsakiyar su. Ba ta yi aure ba kuma ta riga ta yanke hukuncin ba za tayi auren zumunci ba.
''Na faɗa wa mamata cewa ba zan yanke hukunci kan ƴan‘uwana ba , amma dai ni ba zan yi ba,'' in ji Mallika.
Ta ce samun ilimi ya samar mata da damarmaki. ''A baya, ko ka yi karatu, ba za a sa ran za ka yi amfani da shi ba, aure kawai za ka sa gaba. Amma yanzu wannan tunanin ya sauya.''
Sabbin alkaluma abin damuwa
A Birtaniya da Turai, auren zumunci na kara fuskantar suka- musamman daga likitoci, waɗanda ke gargaɗin cewa ƴaƴan da aka haifa ta hanyar auren ƴan uwa na kusa na da yiwuwar fama da matsalolin da su ka shafi lafiya da dama.
A yanzu kuma akwai sabbin alkaluma masu tayar da hankali daga Bradford da za a kara kan wanda ake da shi.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Masu bincike a jam'iar da ke birnin na shiga shekararsu ta 18 a cikin binciken 'waɗanda aka haifa a Bradford'.
Wannan shi ne ɗaya daga cikin manyan bincike-bincike irinshi : tsakanin 2007 da 2010, masu binciken sun samu jarirai 13,000 a birnin, sannan su ka bibiye su tun daga yarintarsu zuwa tasawarsu a yanzu kuma zuwa girmar su.
Fiye da yaro ɗaya cikin yara shida a cikin binciken na da iyaye da su ka yi auren zumunci, mafiya yawa daga alumma Pakistani da ke Bradford, wanda ya sanya binciken cikin bincike mafi muhimmanci kan tasirin da auren zumunci ke yi kan lafiya.
A cikin wasu bayanai da aka wallafa a watannin da su ka gabata- kuma akayi fashin baƙi kansu a wani kashi mai zuwa cikin shirin BBC Radio 4 - masu binciken sun gano cewa akwai yiwuwar auren zumunci na da tasiri mai girma fiye da yadda akayi tunani a baya.
Hanya mafi sauƙi da iyayen da suke ƴan uwa za su kara yiwuwar ɗansu ya samu wani rashin lafiya shi ne idan su ka gadar mishi da ƙwayoyin cuta, kamar irin cutar sikila.
A cewar bincike kan ƙwayoyin halittu kamar yadda masanin ilimin halittu Gregor Mendel ya bayyana, idan iyaye biyu na ɗauke da ƙwayar halitta mai ɗauke da wata cuta, akwai yiwuwar ɗansu zai kamu da cutar a ma'unin ɗaya bisa huɗu.
A yayin da kuma iyayen ƴan uwa ne, akwai yiwuwar cewa dukkansu na ɗauke da wannan ƙwayar hallitar. Ɗan ƴan uwa na kusa na da yiwuwar gadar cutar da kashi 6 bisa ɗari, idan aka kwatanta da kashi 3 ga sauran alumma.
Sai dai binciken na Bradford ya duba lamarin a mahanga mai faɗi, kuma ya yi ƙarin haske. Binciken bai mayar da hankali kawai kan ko an gano yaron na da wani cutar ta musamman ba. Binciken ya mayar da hankali kan abubuwa da dama, kamar sanya ido kan komai ciki har da yadda yaran ke magana, da ko sau nawa su ke zuwa asibiti da kuma kokarinsu a makaranta.
Sun yi amfani da wani samfurin lissafi wajen kawar da tasirin talauci da ilimin iyayen domin su mayar da hankali kacokan kan tasirin samun iyaye ƴan uwa wanda a kimiyya a ke kira 'Consanguinity''.
Sun gano cewa bayan an kawar da lamarin talauci, ɗan ƴan uwa na kusa a Bradford na da yiwuwar kashi 11 cikin ɗari na samun matsala wajen magana idan aka kwatanta da kashi 7 na yaran da iyayensu ba ƴan uwa ba ne.
An kuma gano rashin lafiyarsu ta hanyar lokutan da su ka ziyarci asibiti a shekara. Yaran da ƴaƴan ƴan uwa na kusa ne su na zuwa a kiyasi sau huɗu a shekara a maimakon uku.
Ƙaruwar nuna damuwa
Wannan dai a zahiri bincike ne guda ɗaya kacal, kuma mutanen da ke Brandford ba sa wakiltar dukka mutanen da ke Birtaniya.
Sai dai har ila yau, ya na ƙara damuwar da masana kimiyya ke da shi da a yanzu ya janyo hankalin ƴan majalisa a faɗin Turai.
Ƙasashen Scandinavia da ke gabashin Turai sun ɗauki matakin haramta auren zumunci bakiɗaya.
A ƙasar Norway ma, an haramta auren zumuncin a bara, yayin da a Sweden kuwa ana sa ran haramta auren a shekara mai zuwa.

Asalin hoton, PA Media
A Birtaniya, wani ɗan majalisa a jam'iyyar Conservative Richard Holden ya gabatar da wani ƙudirin haramta auren zumunci, domin ƙara shi cikin jerin auren da aka haramta ( da suka haɗa da auren iyaye, ƴaƴa, ƴan uwa na jini, da kuma kakkanni). Sai dai gwamnatin Jam'iyyar Labour ta ce ''babu wani shiri'' na sanya haramci.
A halin da ake ciki, Birtaniya na bin tsarin ''bayar da shawara kan ƙwayoyin halitta'', wanda ake amfani da shi wajen ilmantar da ma'aurata ƴan uwa makusanta kan illolin da ke tattare da samun ƴaƴa, kuma ana ƙarfafa musu gwiwar zurfafa bincike da gwaje gwaje a lokacin da ake ɗauke da ciki.
Ga mafiya yawa a Birtaniya, lamarin auren zumunci bakuwar lamari ne. Sai dai ba haka abin yake a baya ba. Wanda ya ƙirƙiro bayanin samuwar ɗan'adan, Charles Darwin ya auri ƴar uwarsa ta kusa Emma Wedgwood. Haka zalika Sarauniya Victoria ta auri ɗan uwanta na kusa Yarima Albert.

Asalin hoton, Getty Images
Zuwa ƙarni na 20, adadin auren zumunci ya ragu zuwa kashi ɗaya. Sai dai ya kasance ala'ada a tsakanin ƴan kudancin Asiya marasa rinjaye.
A wasu gundumomi uku a Bradford, kusan rabi, wato kashi 46 cikin ɗari na iyaye mata daga alummar Pakistani sun auri ƴan uwa makusanta ko waɗanda ba na kusa ba, a cewar bayanai daga binciken 'waɗanda aka haifa a Bradford' da aka fitar shekaru biyu da suka gabata.

Asalin hoton, Sam Oddie
A nan Bradford kuwa, abu ne mai sarƙaƙiya. Farfesa Sam Oddie, likitan da ya ƙware a fannin kula da jarirai da ba su kai lokacin haihuwa ba da waɗanda ke mayuwacin hali a asibitin koyarwa na Bradford, ya yi aiki a birnin fiye da shekaru ashirin.
A cikin shekarun da ya yi, ya ga cutukan da ake gado masu tsanani da dama. '' Na ga cutukan fata masu tsanani, cutukan ƙwaƙwalwa masu tsanani da cutukan tsoka masu tsanani'. Ya ce nan take ya gane cewa ana samun yawaitar waɗannan cutukan a Bradford fiye da ko ina.
Ya tuno da wasu misalai masu muni: iyalai da su ka rasa ƴaƴa da dama, ɗaya bayan ɗaya, ga cuta iri ɗaya.
Tasirin ilimi
A maimakon haramtawa, Farfesa Oddie ya jaddada tasirin ilimi - ko kuma abin da ya kira ''ilimin kwayoyin halittu”.
Tsawon shekaru ana ganganmin ilimantarwa a Bradford a alummar Pakistan. Ana bai wa ma'aurata shawarwari daga ƙwararru a lokacin da iyaye mata ke da ciki.

Asalin hoton, Getty Images
Kuma a Bradford ana samun ci gaba, wasu na ɗaukar shawarwarin.
Idan mu ka dawo gidan ƴan uwa matan, dukkanin matan uku da muka zanta da su sun ce al'adar auren zumunci na sauyawa kaɗan kaɗan, a wani ɓangaren saboda kara wayar da kai kan barazanar sa ga lafiya.
''Dole ne ya kasance abu da ke faruwa a hankali- a hankali ya ke tafiya, ba za ka iya yi mishi gaggawa ba,'' in ji Salina, ƴar uwar da ta zaɓi ta yi auren soyayya.
''Mahaifiyata na da ƙarancin shekaru lokacin da ta zo Birtaniya daga Pakistan. Ta na da wasu ra'ayoyi, amma duk sun sauya saboda ta na ƙaunar mu. Kawai na yi mata bayani, 'Mama, ta yaya hakan zai taimaka miki dagewa sai anyi auren zumunci?'.''
Malika, babbar ƴar ta, ita ma ta yarda da hakan.
Itama Ayesha, babbar ƴar su wadda ke cikin auren zumunci ta ce ba ta tunanin ɗaya daga cikin ƴaƴanta za su auri ƴan uwansu ba.
A lokacin da ta aure ɗan uwanta, ta ce, '' ban san mene ya kamata ba. Iyaye na sun rike ala'adar su sosai a lokacin. A yayin da shekaru ke tafiya, al'adar na ɓacewa kaɗan kaɗan.
Ta na sane da illar gadar ƙwayoyin halitta masu ɗauke da cuta a lokacin da ta haifi ƴaƴanta, amma babu ko ɗaya daga cikinsu da ke da wata cuta ta gado.
Tilasta yin auren
Baya ga nuna damuwa kan lafiya, akwai wasu dalilai kuma da suka sa mutane ke son su ga an haramta auren zumunci, wato tasirinsa kan zama tare da haɗin kai. Wannan shi ne babban abin da ke janyo muhawara a ƙasashen Scandinavia. A Norway, inda aka haramta auren zumunci a bara, ƴan majalisa sun ce yin hakan na da alaƙa da auren dole, inda ake tilasta wa wasu baƙin haure mata ƴan kudancin Asiya auren ƴan‘uwansu.
'Taka burki'
A mahangar wasu, haramta auren zumunci kai tsaye na da yiwuwar nuna kamar ana musguna wa wani ɓangare na alumma marasa rinjaye ne.
Ƙudirin dokar Richard Holden dai na jiran karatu na biyu.
Ba tare da goyon bayan gwmnati ba, da wuya in za a amince da shi, sai dai kasancewar akwai wannan ƙudirin dokar da kuma abin da ke faruwa a Scandinavia ya sa ana cigaba da tofa albarkacin baki kan batun na auren zumunci.











