Yadda za ku kula da lafiyar idanunku

Asalin hoton, Lucy Owen/BBC
Sau da yawa mutane ba su cika mayar da hankali kan lafiyar ido ba, musamman ma waɗanda ba su taɓa fama da wata lalura ta ido ba.
"Muna amfani da idanunmu daga lokacin da muka buɗe su har zuwa lokacin da suka rufe. Kamar dai yadda muke amfani da zukatanmu." In ji Sarah Maling, malama a Kwalejin Ido ta Royal Colege of Ophthalmologist da ke Birtaniya.
"Amma a lokacin da muka yi gudu, bugun zuciyarmu kan ƙara sauri, daga baya kuma sai ya yi sauki. Ba kamar zuciya ba, ba za mu ce za mu daina kallo saboda idanunmu sun gaji ba."
"Amma ba mu cika tunanin mu binciki lafiyarsu ba."
Wannan wani abu ne da abin da ake son ganin an samu sauyi a kai a Ranar Kula da Lafiyar ido ta duniya.
"Muna son mu aika da wannan saƙon ga mutane da dama cewa duba lafiyar ido abu ne mai matuƙar muhimmanci, kuma mu san wuraren da suka kamata mu je domin duba lafiyar idanunmu." In ji Peter Holland, wanda shi ne shugaban Hukumar kare lalurar makanta ta duniya (IAPB).

Asalin hoton, Getty Images
Ma'aikaciyar BBC, Lucy Owen a cikin kwanakin nan ta yi rubutu kan yadda duba lafiyar ido ya cece ta daga samun lalurar makanta.
Lucy ta riƙa amfani da abin taimaka wa gani da ake maƙalawa a ƙayar ido tun tana da shekara 16.
Yanzu ta haura shekara 50 da haihuwa, amma a watan Yunin da ya gabata sai ta fara ganin wani haske na wulgawa ta idonta na dama.
Ta ce "Ba kodayaushe nake ganin hasken ba, yakan faru ne sau ɗaya ko biyu a rana, duk da cewa abu ne da ban saba gani ba, amma ban hanzarta zuwa domin a duba ba.
"Ganin cewa ina gab da cika shekara 52 da haihuwa, sai na ɗauka wani abu ne da ya shafi shekaru."
Ta yarda cewa tabbas ba ta cika zuwa wurin duba lafiyar idanunta kamar yadda ya kamata ba, kuma sau da dama takan manta da batun zuwa duba lafiyar idanunta na shekara-shekara.
To amma da ta ga hasken da ke wulgawa a idon nata na ci gaba da ƙaruwa, sai ta je domin a duba.
A wannan lokaci ne likitan ido ya gano cewar wani ɓangare na ƙwayar idon nata ya fara samun matsala, kuma wannan hasken da take gani alama ce ta lalurar ido.

Asalin hoton, Lucy Owen/BBC
Daga nan ne aka yi wa Lucy tiyata a idon nata na dama.
An kwashe kimanin minti 40 ana tiyatar, inda cikin sa'o'i kaɗan ta bara asibitin.
"Na kwashe mako guda ina kwanciya a ɓari ɗaya, sannan na fara jiran lokacin da ganina zai dawo yadda yake a baya."
Ganin nata ya riƙa inganta a cikin ƴan watanni, yanzu har ta dawo aikinta na gabatar da labarai.
Ta ce "Abin da nake tunanin kawai shi ne na ci sa'a. Na yi dace cewar na je wurin likitan ido a lokacin da na je, kuma sun yi min aiki a lokacin da ya dace."

Asalin hoton, Getty Images
To sai dai, musamman a ƙasashe matalauta, ba kowa ne yake da gatan samun kula da lafiyar ido daga ƙwararru ba kamar yadda Lucy Owen ta samu.
A shekara ta 2023, Hukumar kula da ƙwadago ta duniya ta ce kimanin mutum biliyan 2.2 ne ke fama da lalurar gani ko makanta a faɗin duniya, inda sama da miliyan 1.1 suke fama da lalurar gani da za a iya kare faruwarta.
Matuƙar ba za a mayar da hankali wajen kula da lafiyar ido domin kauce wa lalurorinsa ba to kuwa yawan mutanen zai ƙaru musamman a ƙasashe marasa ƙarfi.

Asalin hoton, Getty Images
Yadda za ka kula da lafiyar ido ba tare da kashe kuɗi ba
- Ka tuna da kula da lafiyar idonka tare da duba su a duk lokacin tunawa da zagayowar ranar haihuwarka.
- Yi wannan domin tabbatar da lafiyar idonka: Ku kalli wani wuri da kuka saba gani da idanunku biyu a buɗe; ku rufe ido ɗaya da tafin hannu, sai ku sake kallon wurin da ido ɗaya; ku juya kan ɗaya idon. Idan ku ka gano cewa akwai bambanci, to akwai buƙatar ko ga ƙwararre.
- Idan kuna da yara ƴan ƙasa da shekara bakwai, kuma ba ku da wata hanyar ganin likita domin duba lafiyar ganinsu, ku sa su su kalli wani abu da ke nesa da su, sannan ku duba ko suna iya ganin abin da dukkanin idanunsu biyu, wataƙila za ku iya fahimtar suna da lalurar rashin ƙarfin gani.
- Ku tuna cewa hanyar tabbatar da lafiyar ido ita ce ta hanyar kare shi daga cuta.
Shawarwari daga Sarah Maling, Kwalejin Lafiyar Ido ta Royla da ke Birtaniya.











