Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An fitar da sunayen ɗaliban Kebbi 25 da ƴanfashi suka sace
Shugaban ƙaramar hukumar Danko/Wasagu a jihar Kebbi, inda aka sace ɗaliban sakandare mata ranar Litinin, ya fitar da sunayen ɗaliban da 'yanbindigar suka sace daga makarantar Government Girls Comprehensive Secondary School, Maga.
Hussaini Aliyu ya faɗa wa BBC Hausa cewa dukkan yaran 25 da aka sace Musulmai ne saɓanin abin da wasu ke yaɗawa a shafukan sada zumunta.
Sai dai biyu daga cikin ɗaliban sun kuɓuta, abin da ya sa yanzu 23 ne ke hannun maharan.
Bayan sace ɗaliban, muhawara ta kaure musamman a shafukan sada zumunta kan ko su wane ne ɗaliban, bayan wani ɗan majalisar Amurka Riley Moore ya yi zargin cewa an kai harin ne a "wani yanki mai yawan mabiya addinin Kirista".
Wannan ya ƙara ingiza wutar muhawarar da ake yi kan zargin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi kan cewa ana "yi wa Kiristoci kisan gilla" a ƙasar.
Najeriya ta musanta zargin, inda ta ce matsalar tsaro a ƙasar ta shafi dukkanin al'umma, ba tare da la'akari da addininsu ba.
Kalaman na ɗan majalisar dokokin Amurka kan sace ɗaliban na Kebbi ya sha suka daga mutane da dama.
Wannan ya sa hukumomi a jihar ta Kebbi suka fitar da sunayen yaran, kuma suka tura wa BBC.
Ba za mu iya wallafa sunayensu ba saboda tsaron lafiyarsu.
A ranar Laraba, shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce ya ɗage balaguron da zai yi zuwa taron ƙungiyar G20 a Afirka ta Kudu da kuma birnin Luanda na Angola saboda garkuwa da ɗaliban da kuma harin 'yanfashi suka kai coci a jihar Kwara da ke tsakiyar ƙasar.
Sanarwar da fadar shugaban ƙasa ta fitar ta ce Tinubu na jiran rahoto kan ɗaliban Kebbi daga mataimkinsa Kashim Shettima, wanda ya kai ziyara jihar.
Shettima ya isa Kebbi ranar Laraba, inda ya gana da Gwamna Nasiru Idris a asirce.
Da yake magana a Birnin Kebbi, mataimakin shugaban ƙasar ya tabbatar wa iyayen yaran "irin ƙoƙarin da gwamnatin tarayya ke yi domin kuɓutar da 'ya'yansu", kamar yadda wata sanarwa ta bayyana.
Ya bayyana garkuwa da ɗaliban a matsayin "hari kan 'yan Najeriya baki ɗaya".
Shugaba Tinubu wanda ya ce "ya kaɗu" da ƙaruwar hare-hare a faɗin Najeriya, ya ce bai wa jami'an tsaro umarnin su yi azamar kuɓutar da ɗaliban.
"Na bai wa jami'an tsaro umarnin su yi azama wajen kuɓutar da 'yanmatan a jihar Kebbi," in ji shi.
Manyan hare-hare uku a Najeriya cikin mako ɗaya
Cikin mako ɗaya, an samu munanan hare-hare a sassan Najeriya, musamman a arewa maso gabas, da arewa maso yamma, da arewa ta tsakiya.
A ranar Litinin ne mazauna jihar Borno suka tashi da labarin rasuwar Birgediya Janar Musa Uba a hannun mayaƙan ƙungiyar Iswap, wadda ta ɓalle daga Boko Haram.
Tun a ƙarshen mako rundunar sojan Najeriya ta sanar cewa 'yanbindigar sun yi wa dakarunta kwanton ɓauna tare da kashe soja biyu da 'yan sa-kai biyu, amma ta musanta cewa an yi garkuwa da jagoran ƙaramar rundunar Janar Uba.
Ta ƙara da cewa dakarun nata sun nuna "jajircewa wajen kare harin da kuma fatattakar" maharan a garin Wajiroko da ke ƙaramar hukumar Damboa.
Sai kuma a ranar Talata wani bidiyo ya fara yawo a shafukan sada zumunta, wanda Iswap ta fitar da iƙirarin cewa ta kashe Janar Uba bayan kama shi sakamakon harin na ranar 15 ga watan Nuwamba.
An samu tabbacin mutuwar janar ɗin ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya fitar a ranar Talatar, inda a ciki Shugaba Tinubu ya miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan babban jami'in sojan.
Shi ne janar ɗin sojan Najeriya na biyu da Boko Haram ko Iswap suka kashe, bayan kashe Birgediya Janar Dzarma Zirkusu a 2021.
Wani harin da ya girgiza 'yan Najeriya shi ne na satar ɗalibai mata a jihar Kebbi da ke arewa maso yamma da asubahin ranar Litinin, inda 'yanfashin daji suka yi garkuwa da ɗalibai 25.
Bayan sace ɗaliban daga makarantar sakandare ta Government Girls Comprehensive Secondary School, Maga da ke ƙaramar hukumar Danko/Wasagu, biyu daga cikinsu sun kuɓuta daga hannun maharan.
Maharan sun kuma kashe maigadi da mataimakin shugaban makarantar.
A jihar Kwara kuma da ke tsakiyar ƙasar, harin da 'yanbindiga suka kai wata coci ranar Talata da yamma ya ƙara tayar da hankalin 'yan Najeriya.
Wani bidiyo da kyamarar cocin ta Christ Apostolic Church (CAC) da ke yankin Eruku a ƙaramar hukumar Ekiti ya nuna yadda maharan suka dinga harbe-harbe kafin su shiga cikin cocin domin kwashe jakunkuna da wayoyin masu ibada.
Rahotonni sun ce maharan sun kashe aƙalla mutum uku tare da yin garkuwa da mutum fiye da 30.
Rundunar 'yansandan Najeriya ta ce ta gano gawar mutum ɗaya a cikin cocin da kuma ta wani daban a cikin daji ɗauke da harbin bindiga.