Janar Dzarma Zirkushu: Mayaƙan ISWAP sun kashe janar ɗin Najeriya da sojoji uku a Borno

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da cewa mayaƙan ISWAP da ke iƙirarin jihadi a yammacin Afrika sun halaka Birgediya Janar Dzarma Zirkushu da wasu sojoji uku a lokacin da da suka je kai ɗauki yayin wata ba-ta-kashi da mayaƙan.

A wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar a shafinta na Facebook, ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a Ƙaramar Hukumar Askira Uba da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.

Sojojin dai sun ce sun lalata motoci da makaman ƴan ISWAP ɗin inda suka lalata motocinsu tara da ake girke bindigogi.

Rundundar sojin ta kuma bayyana cewa an tuntuɓi iyalan janar ɗin da sauran sojojin da suka rasu domin shaida musu abin da ya faru haka kuma shugaban sojojin ƙasa na Najeriyar Laftanar Janar Faruk Yahaya ya miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan sojojin.

Tun da safiyar ranar Asabar kafafen yaɗa labarai na Najeriya suka ruwaito labaran cewa an kai hari a Askira Uba.

Wasu mazauna garin sun shaida cewa sun hangi mayaƙan a kan hanyarsu a cikin manyan motoci masu ɗauke da bindigogi da safe kuma suka kai rahoto ga jami'an tsaro kafin su kai harin.

Ko a shekarar da ta gabata sai da mayaƙan Boko Haram suka kashe wani Kanal ɗin sojin Najeriya wato Kanal DC Bako ta hanyar yi masa kwanton-baunan da tagawarsa a yankin Sabon Gari-Wajiroko kusa da Damboa jihar Borno