Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tinubu ya jajanta wa iyalan Birgediya Janar Musa Uba
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya tabbatar da mutuwar jami'in sojan ƙasar Birgediya Janar Musa Uba, wanda mayaƙan ƙungiyar Iswap suka kashe a jihar Borno.
An fara fargabar mutuwar Janar Uba ne bayan ƙungiyar ta yi iƙirarin kashe shi, da kuma fitar da wani bidiyo.
Wata sanarwa da rundunar sojan Najeriya ta fitar ta ce a ƙarshen makon da ya gabata ne 'yanbindigar suka yi wa dakarunta kwanton ɓauna, waɗanda janar ɗin ke jagoranta.
Zuwa yanzu rundunar ba ta ce komai ba game da bidiyon da ke yawo a intanet.
Sai dai cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Talata, Shugaba Tinubu ya ce mutuwar janar ɗin "ta kaɗa" shi.
"A matsayina na babban kwamandan tsaro na ƙasa, na ji takaici da mutuwar sojojinmu a bakin aiki. Allah ya bai wa iyalan Birgediya Janar Musa Uba da sauran dakaru haƙuri," in ji shugaban.
Me ya faru da Birgediya Janar Uba?
A makon da ya gabata ne ƙungiyar ISWAP ta kai wani harin kwanton-ɓauna kan sojojin Najeriya, a ranar Alhamis 14 ga watan Nuwamba a ƙaramar hukumar Damboa ta jihar Borno.
Sai dai tun bayan harin, wani abu da ya shige duhu shi ne makomar kwamandan birged na 25, wato Birgediya Janar M. Uba, wanda shi ne jagoran sojojin.
Bayan iƙirarin da rundunar sojin Najeriya ta yi na cewa babban sojan na nan da ransa a ranar Asabar 15 ga wata, sai ga shi a ranar Litinin 17 ga wata ƙungiyar ISWAP ta sanar da cewa ta kama tare da hallaka shi.
ISWAP ta bayar da wannan sanarwa ne a shafinta na Telegram, inda ta ce mayaƙanta sun kama Uba ne a ranar 15 ga watan Nuwamba bayan harin kwanton-ɓauna da suka kai wa sojojin Najeriya a kusa da garin Wajiroko da ke jihar ta Borno.
Ƙungiyar ta wallafa hoton Birgediya-Janar Uba tana mai iƙirarin cewa mayaƙanta sun kashe "babban kwamanda" wanda ya tsere daga "harin kwanton-ɓauna kan dakarun haɗin gwiwa na Najeriya da masu taimaka mata''.
Bayan haka ne kuma aka ga wasu hotuna har da bidiyo na yawo a shafukan sada zumunta na abin da ake bayyanawa a matsayin lokacin da ƙungiyar ta hallaka sojan.
To sai dai rundunar sojan Najeriya ba ta sake cewa komai ba kan batun.
ISWAP wani ɓangare ne na ƙungiyar Boko Haram, wadda ta ƙaddamar da yaƙi kan hukumomin Najeriya tun a shekara ta 2002 ƙarƙashin shugabanta na farko, Muhammad Yusuf.
Daga baya ƙungiyar ta dare zuwa gida biyu bayan jami'an tsaro sun kashe wanda ya samar da ita, inda a yanzu ake da ɓangarori biyu na ƙungiyar, wato ISWAP da kuma Boko Haram, kuma dukkaninsu na ci gaba da ƙaddamar da hare-hare ne a yankin tafkin Chadi.
Me hukumomi suka ce?
Bayan ɓullar labarin harin kwanton-ɓaunan, rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da cewa an kai wa dakarun nata hari a jihar Borno.
A ranar 15 ga watan Nuwamba, rundunar ta ce an kai wa kwamban motocin sojojin hari ne a cikin dare, ranar 14 ga watan Nuwamba, inda ta ce harin ya yi sanadin kashe mutum huɗu, sai dai ta musanta labarin da ke cewa an kashe Birgediya Uba.
Sanarwar rundunar sojin ta ce an kai wa birged na 25 na rundunar sojin hari ne bayan sintirin da suka yi a kusa da garin Wajiroko da ke Azir Multe a ƙaramar hukumar Damboa.
Suna dawowa ne daga "sintiri wanda aka yi cikin nasara" a dajin Sambisa, wanda ya ƙunshi jami'an soji da kuma jami'an Sibiliyan JTF (CJTF) ƙarƙashin jagorancin Birgediya-Janar M Uba.
"Dakarun masu sintiri sun yi artabu da masu tayar da ƙayar baya waɗanda suka buɗe musu wuta, lamarin da ya tursasa musu janyewa da watsar da manufar tasu.
"A lokacin artabun an rasa rayukan gwarazan sojoji biyu da ƴan CJTF biyu, yayin da suke hidimta wa ƙasarsu," a cewar sanarwar.
Haka nan sanarwar ta ƙara da cewa "rundunar sojin Najeriya na son ƙaryata labaran da ake yaɗawa a wasu kafafen yaɗa labarai cewa an yi garkuwa da kwamandan birged ɗin (Birgediya Janar M. Uba)".
Baya ta haihu
Sai dai rahoton jaridar PRNigeria na ranar Litinin 18 ga watan Nuwamba ya ce akwai ''mummunan labari'' game da yunkurin ceto jami'an tsaron da ƙungiyar ISWAP ta kai wa harin kwanton-ɓauna na ranar 14 ga watan Nuwamba.
A cewar jaridar, majiyoyinta sun gano cewa bayan da babban hafsan sojin ya samu mafaka sannan ya yi waya da abokan aikinsa cewa yana cikin aminci, "mayaƙan sun samu nasarar sauraron wayar da ya yi da abokan aikin nasa, inda suka yi amfani da wannan bayanin wajen gano daidai inda yake a ɓoye, sannan suka halaka shi."
Hakan ya biyo bayan sanarwar da ƙungiyar ISWAP ta bayar ta ikirarin kashe Birgediya Janar M Uba.
Wane ne Birgediya Janar M Uba?
Birgediya Janar M Uba shi ne kwamandan birged na 25 na rundunar sojin Najeriya.
Uba, ya zamo jami'in sojin Najeriya mafi girman muƙami da ƙungiyar ta kashe tun daga shekarar 2021.
Borno na cikin jihohin Najeriya da suka fi fama da hare-haren masu iƙirarin jihadi, inda Boko Haram da sauran ƙungiyoyi ke iko da wasu yankuna.
A tsakiyar watan Janairu ma wasu mayaƙan Boko Haram ko na Iswap sun kai wa wasu manoma da masunta hari a garin Dumba na jihar ta Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Akasarin mazauna ƙananan hukumomin Gudumbari, da Marte, da Abadam na zaune ne ƙarƙashin ikon 'yanbindigar kusan tsawon shekara shida.