Mutane huɗu da ke da ikon bai wa soja umarni a Najeriya

Lokacin karatu: Minti 5

Tun bayan dambarwar da ta ɓarke bayan jayayya tsakanin ministan babban birnin Najeriya, Abuja, Nyesom Wike da wasu jami'an soji da ke tsaron wani fili da ake gini a birnin, ana ci gaba da tambayoyi game da tanadin doka a kan bayar da umarni da kuma biyayya a tsakanin jami'an tsaro.

Wannan ya biyo yadda ministan da tawagarsa suka nemi shiga filin da sojojin ke tsaro, amma sojojin suka yi turjiya, har ta kai ga musayar kalamai tsakanin bangarorin biyu.

A cikin bidiyon, an ga yadda Mr Wike ya umarci sojojin su kauce domin bari shi da jami'ansa su shiga filin, amma jami'an sojin a ƙarƙashin jagorancin wani matashin hafsan sojin ruwa suka jajirce cewa umarni aka ba su kuma ba za su bari a yi akasin umarnin da suke aiki a kai ba.

Shin mene ne tanadin doka a kan yadda jami'an soji suke ɗaukar umarni a Najeriya?

BBC ta tuntuɓi Navy Captain Umar Bakori mai murabus wanda ya bayyana cewa a tsarin aikin soja ''iri ɗaya yake a ko'ina a duniya'' kuma an gina shi ne kan tsari mai kyau na bayarwa da kuma ƙololuwar biyayya ga umarni daga na sama zuwa na ƙasa, kuma ba tare da jayayya ba.

Jami'in sojin ya ce saboda martaba wannan tsari ne ko a tsakanin waɗanda suka shiga aiki a lokaci ɗaya tsakanin jami'an soja, akwai biyayya da girmamawa tsakanin waɗanda ke riƙe da wasu muƙamai da kuma na ƙasa da su.

Ya yi bayanin cewa akwai wasu keɓaɓɓun mutane da dokar aikin soja ta tilasta wa duk wani jami'in soja yin biyayya ga umarnin su, waɗanda suka haɗa da:

Shugaban ƙasa:

Navy Captain Bakori ya ce kamar yadda dokar ƙasa da kuma dokokin soja suka yi tanadi, shugaban ƙasa ko da farar hula ne, shi ne babban kwamandan hafsoshin Najeriya domin haka yana da ikon bayar da umarni ga kowanne jami'in soja kuma a ko'ina yake dole ya yi biyayya.

Jami'in da ke gaba da shi:

Bayan shugaban ƙasa wani da doka ta tilastawa soja yin biyayya ga umarninsa shi ne na gaba da shi a aiki. Navy Captain Bakori ya ce ''a bisa dokar soji duk wanda ke gaba da kai a muƙami zai bayar da umarni gare ka, kuma wajibi ne ka yi masa biyayya kai tsaye.

Ya ƙara da cewa ''idan na gaba da kai ya bayar da umarni, dole ka aiwatar da abin da aka umarce ka kuma idan ma aka samu matsala har wani babban soja ya gane cewa akwai damuwa to ba zai soke umarnin ba, sai dai ya shawarci shi wancan da ya bayar da umarnin na farko cewa ya kamata ya janye umarnin.”

Ministan tsaro:

Akwai lokacin da ministan tsaro ke iya bayar da umarni ga jami'an soja kuma su yi biyayya kai tsaye. Navy Captain Bakori ya ce ''Yana rubuce a cikin kundin mulki cewa shugaban ƙasa shi ne shugaban majalisar tsaro ta ƙasa, amma minista na zama wakilinsa. Don haka a wannan yanayi yana iya bayar da umarni kuma a yi masa biyayya.

Muƙaddashin shugaban ƙasa:

Jami'in sojan ya kuma bayyana cewa ''Doka ta amincewa duk wani muƙaddashin shugaban ƙasa yana iya bayar da umarni ga jami'an soja kuma dole su yi masa biyayya.''

Navy Captain Umar Bakori ya jaddada cewa baya ga waɗannan mutane babu wani da zai iya bayar da umarni ga jami'in soja kuma ya yi masa biyayya.

Me ya sa soja ya ƙi yin biyayya ga umarnin Wike?

Navy Captain Umar Bakori ya yi bayanin cewa jami’in sojan ya ƙi biyayya ne ga umarnin da ministan Abuja ya ba shi saboda shi ministan ba ya a cikin mutanen da doka ta amince ya yi wa biyayya.

Ya ce ''Dokar da ta fayyace mutanen da jami'in soja zai yi wa biyayya babu ministan Abuja, don haka umarnin da ya bayar ba shi da wani tasiri a kan jagoran sojojin da kuma ƙananan jami'an da suke tare da shi a wannan lokaci.''

Navy Captain Bakori ya ƙara da cewa a wannan yanayin babu yadda za a yi waɗannan jami'an tsaron na soja su yi biyayya ga duk wani umari na daban da wanda aka ba su da farko. Kuma duk sojan da na sama da shi ya bayar da umarni kuma ya ƙi aiwatar da umarnin to zai fuskanci hukunci mai tsauri.

Ya ƙara da cewa a tsarin aikin soja ba za ka bai wa na ƙasa da kai umarnin da ba zai iya yi ba saboda haka ''duk wanda aka samu da irin wannan laifi zai iya fuskantar hukunci na wanda ya yi sakaci da aiki, ko wanda ya nuna turjiya ga na gaba ko kuma wanda ya yi raini ga tanadin dokar aiki.''

‘Takobi mai kaifi biyu’

To sai dai wani masanin shari’a da ya zanta da BBC, Barista Emmanuel Umorem ya ce abin na da bangarori biyu.

Ya yi bayanin cewa idan aka lura da abin da ya faru tsakanin minista da soja a ranar Talata, kowane bangare na da nasa laifin.

Ya yi ishara ha wasu hukunce-hukunce biyu da Kotun Koli ta Najeriya ta yanke.

Ya ambato hukuncin Kotun Koli tsakanin wani mutum mai suna Onunze da gwamnati a shekarar 2023, da kuma shari’ar Rundunar sojin sama ta Najeriya da James a 2002, wadanda a cewarsa hukunce-hukuncen suka nuna cewa bai zama wajibi sojoji su yi biyayya ga umarnin da ya saba wa doka ba.

Ya ce a lokacin yanke hukuncin, mai shari’a Ogunwumiju ya ce “wajibcin bin umarnin na gaba bai hada da umarnin da babu adalci a tattare da shi ba.

Kowane soja ko dansanda ya yi rantsuwar bin doka a farkon fara aikinsa. Rantsuwar ba tana nufin biyayya ga kowane umarni ba, alkawari ne na “karewa” da “martaba” kundin tsarin mulkin Najeriya daga makiya, na cikin gida da kuma waje”.

Barista Umoren ya ce abin da hukuncin ke nufi shi ne ya kamata a ce sojan ya san cewa ba tilas ne ya yi biyayya ga umarnin da ba ya kan gaskiya ba.

A daya bangaren kuma, ya kafa hujja da hukuncin Kotun Koli a kan shari’ar da ta hada da Gwamnan Legas da wani mutum mai suna Ojukwu. Ya ce abin da ministan Abuja ya yi shi ne “kokarin taimakon kansa da kansa” wanda kuma hakan ya saba wa doka.

Ya yi bayanin cewa Kotun Koli tana jan kunne kan jami’in gwamnati ya yi amfani da salon “taimakon kai da kai” wajen tafiyar da aikin gwamnati.

Idan wani ya mallake filin da ba nasa ba, kuma minista yana son tabbatar da doka, ministan ba ya da ikon daukan kafarsa ya je wurin, domin hakan na nufin yana son ya yi gaban kansa ne wajen tabbatar da doka, kuma doka ta haramta hakan, domin kundin tsarin mulki ya samar da hukumomin warware wadannan rigingimu domin samar da maslaha a irin wannan yanayi.

Wace dama doka ta bai wa Wike a kan abin da ya shafi ƙasa?

Game da jayayayyar da ake ci gaba da yi kan ƙarfin ikon ministan birnin Abuja kan bayar da filaye da kuma magance rikicin da ya taso a kai, Barista Aminu Abdulrashid, wani lauya mai zaman kansa a jihar Kaduna da ke Arewa maso yammacin Najeriya ya ce dokokin amfani da ƙasa, 'Land Use Act' a turance sun fayyace duk wani iko na ministan.

Barista Aminu Abdulrashid ya ce ''ministan birnin Abuja yana da ƙarfin iko daidai da wanda gwamnonin jihohi ke da shi a kan ƙasa'' hakan na nufin shi ne ke da ikon amincewa da bayar da fili ga jama'a a birnin Abuja, kamar yadda gwamnoni ke da iko a jihohin su.

Ya ce sashe na 44 na dokar ya yi tanadin cewa ''idan minista zai ƙwace fili dole sai ya tabbatar da cewa an saɓa wa ƙa'idoji da sharuɗɗan da aka yi amfani da su wajen bayar da filin tun da farko.''

Ya ƙara da cewa dole ne kuma sai an sanar da wanda aka bai wa filin a rubuce ''ta hanyar bayar da sanarwar ƙwace filin a rubuce kuma hannu da hannu, idan hakan ta gagara ana iya liƙawa a wajen da ake jayayya a kai ko kuma duk wata hanya da ake iya samun shi.''

Haka nan kuma lauyan ya bayyana cewa ko da an bayar da takardar ga wanda za a ƙwace wa filin, to za a bayar da lokaci domin ba shi damar yin gyara kan wasu kura-kuren da ya aikata da za su sa a ƙwace filin. Daga cikin irin yanayin da za su haifar da hakan akwai rashin cika ƙa'idar biyan harajin ƙasa.