Dambarwa ta barke a jam’iyyar PDP a jihar Yobe

Jam'iyyar PDP

Har yanzu tana kasa tana dabo, dangane da batun takamaiman dan takarar kujerar majalisar wakilai ta tarayya a jam’iyyar PDP ta mazabar Gujba da Gulani da Damataru da kuma Tarmasuwa a jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya.

 Hakan ya biyo bayan ja-in-jar da ake yi tsakanin Abdullahi Idris, wanda ya ce shi ne sahihin dan takarar wannan kujerar da aka zaba ba tare da hamayya ba, da kuma wasu shugabannin reshen jam'iyyar PDP a jihar ta Yobe, da suka ce wannan dan takara shi ya janye takarar tasa, saboda haka ake kokarin maye gurbinsa da wani.

 Duk wannan dambarwa, har yanzu dan takarar kujerar na farko Abdullahi Idiris, na nan a kan bakansa cewa shi ne dan takarar wannan kujera.

 Abdullahi Idris ya shaida wa BBC cewa shi ne cikakken dan takarar da ya sayi tikitin takara ya cike, kana kuma shi ne mutumin da aka tantance a matsayin dan takara.

 Ya ce “Ni ne kuma mutumin da aka bai wa takardar cewa ni ne na ci zaben fitar da gwani wanda kuma babu abokin hamayya, sannan ni ne wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta tabbatar a matsayin halattaccen dan takara.”

 Abdullahi Idris, ya ce a don haka a halin da ake ciki a yanzu ya garzaya kotu inda a karshe ma har kotu ta bashi takararsa.

Ya ce, “ Duk da wannan hukunci na kotu har yanzu wasu shugabannin jam’iyya wanda wasunsu ne a cikinsu ke son a tunkubeni su kawo wani wanda ba a ma sanshi sun ce basu yarda ba.”

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

 Dantakarar na PDP, ya ce saboda biyayyarsa ga jam’iyyarsa da ya ga wannan dambarwa ta kunno kai ya nemi ayi sulhu amma wasu shugabanninsu suka ki.

 Abdullahi Idris, ya ce sun ce wai shi da kansa ya janye, sam shi dai ya san an kira shi an zauna da shi a kan cewa akwai wanda ya dawo jam’iyyarsu daga APC, to ana so ya janye ya bar masa Takara shi kuma ya ce sam.

 Dan takarar kujerar majalisar wakilan a PDP, ya ce, “To muka tashi ba a cimma yarjejeniya ba, sai kawai naji cewa wai har an kai sunan wanda suke son INEC, a nan ne na dauki matakin da naga ya dace ya dauka.”

 Cewa suka yi wai ni na rubuta takarda a kan cewa na janye na bar wa wancan takara, ni ma sai na rubuta ta wa takaradar nace bani na rubuta takarda da hannuna ba, in ji shi.

Ko da BBC ta tuntube mai bawa jam’iyyar ta PDP a Yobe shawara kan abubuwan da suka shafi shari’a, Barista Ahmed Idris Waziri, ya ce yanzu magana tana kotu har ma an yanke hukunci, to amma tuni suka daukaka kara.

 Ya ce,” Mu wanda muka sani a matsayin dan takararmu a wadannan kananan hukumomi shi ne Honourable Ummaru Kulluma.”

 Yanzu dai muna jira ranar da za a ware mana don zama a kotun da muka daukaka kara, inji shi.

 A yanzu dai kallo ya koma kan yadda zata kaya game da ainihin dan takarar kujerar majalisar wakilan mazabun Gujba da Gulani da Damataru da kuma Tarmasuwa a jihar ta Yobe karkashin jam’iyyar ta PDP.