'Ina takara ne don nuna raunin gwamnati don ta yi gyara'

Bayanan bidiyo, Ina siyasa ne don nuna raunin gwamnati don ta yi gyara - Dan takarar gwamnan Yobe a NNPP
'Ina takara ne don nuna raunin gwamnati don ta yi gyara'

Dan takarar gwamnan jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya a ƙarƙarshin jam'iyyar NNPP, ya ce yana siyasa ne don fito da raunin gwamnati don ta yi gyara.

Alhaji Garba Umar ya shaida wa BBC Hausa haka ne a wata hira da ta yi da shi.

Hirar tana cikin jerin hirarrakin da BBC ke yi da ƴan takarar gwamnoni a jihohin Najeriya.