Shin su wa PDP za ta tsayar takarar gwamna a jihohin Najeriya?

A ranar 25 ga watan Mayun 2022 ne Jam'iyyar PDP a Najeriya take gudanar da zaɓen fitar da gwani na gwamnoni a jihohi 31 cikin 36 na kasar.
Akwai ƴan siyasa da dama da suka fito neman takara a waɗannan jihohi, sai dai kamar yadda Hausawa kan ce ba a san maci tuwo ba sai miya ta ƙare.
Domin kuwa da alama za a fafata sosai a wasu jihohin musamman a jihohin da ba a samu sulhu ko kuma maslha ba. Amma tuni wasu daga cikin masu neman takarar suka fara janyewa saboda wasu dalilai.
Misali a Jihar Kaduna, Dakta Datti Baba-Ahmed ya janye kwana guda kafin zaben fitar da gwani sa'annan a yau da za a gudanar da wannan zaɓe, rahotanni sun ce Wilfred Bonse daga Jihar Cross River shi ma ya janye daga takarar.
Haka ma tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Ike Ekweremadu ya janye daga neman takarar a Jihar Enugu.
Ga wasu daga cikin jihohin Najeriya da ake ganin za a fafata:
Kano
Cikin waɗanda ake ganin suna kan gaba a fafatawa wajen neman gwamna a Jihar Kano akwai Ibrahim Al-Amin Little da Muhiyi Magaji Rimin Gado da Jafar Sani Bello.
Haka kuma akwai Injiniya Mu'azu Magaji wato Ɗan Sarauniya da Mohammed Abacha da Adamu Yunusa Ɗan Gwani. Haka ma akwai Saddik Aminu Wali da Dakta Yusuf Bello Ɗan Batta
Kaduna
Cikin manyan ƴan takarar gwamna a Jihar Kaduna akwai tsohon gwamnan jihar Mukhtar Ramalan Yero da tsohon sanatan Kaduna Ta Tsakiya Kwamared Shehu Sani da Isah Mohammed Ashiru da Sani Abbas.
Katsina
A Jihar Katsina kuwa, waɗanda ake ganin su ke kan gaba wurin neman takarar gwamna a PDP akwai Sanata Yakubu Lado Ɗanmarke da Salisu Yusuf Majigiri da Aminu Ahmad Yar'adua da Shehu Inuwa Imam.
Jigawa
A Jihar Jigawa, cikin waɗanda ke kan gaba akwai ɗan gidan tsohon gwamnan jihar Mustapha Sule Lamido da Alhaji Bashir Adamu Jumbo da kuma Alhaji Saleh Shehu Hadejia
Zamfara
A Zamfara kuwa, cikin waɗanda ke kan gaba akwai Dauda Lawal da Mahadi Aliyu Gusau da Ibrahim Shehu Bakauye
Sokoto
Jihar Sokoto wadda jiha ce da PDP ke jagoranci ana sa ran za a fafata sosai, domin kuwa a cikin masu neman takara akwai mataimakin gwamnan jihar Mannir Ɗan Iya da ɗan gidan tsohon gwamna jihar wato Sagir Bafarawa da Shugaban Jam'iyyar PDP a Sokoto Bello Aliyu Goronyo.
Haka kuma akwai tsohon sakataren gwamnatin jihar Umaru Saidu da kuma tsohon mataimakin gwamnan jihar Mukhtar Shagari.
Adamawa da Bauchi
A Jihar Adamawa da Bauchi kuwa, za a iya cewa babu hamayya sossai a PDP kuma jam'iyar ta PDP ce ke mulki a jihohin.
A Adamawa gwamna mai ci Ahmadu Umaru Fintiri zai kara ne da Ambasada Jamil Abubakar Waziri., sai kuma a jihar Bauchi Barrister Ibrahim Kashim ne kawai ya fito sai dai ana raɗe-raɗin cewa gwamnan jihar Bala Mohammed wanda ke takarar shugaban ƙasa ya sayi fom ɗin gwamna a ɓoye.
Enugu
A Jihar Enugu kuwa akwai Chijioke Edeoga da Bart Nnaji da Gil Nnaji da Everest Nnaji. Haka kuma akwai Offor Chukwuegbo da Hillary Edeoga da kuma Peter Mbah
Abia
A Jihar Abia ma akwai masu neman takarar da dama da suka haɗa da shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa Enyinnaya Abaribe da mataimakin gwamnan jihar Ude Oko Chukwu da tsohon shugaban PDP na jihar ta Abia wato Emma Nwaka.
Sauran sun haɗa da Chima Anyaso da Ncheta Omerekpe da Samson Orji da kuma Enyinnaya Nwafor.











