Abin da dattawan PDP suka ce kan dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar

Wasu dattawan jam`iyyar hamayya ta PDP daga jihohin arewacin Najeriya 19 sun yi watsi da maslahar da wasu dattawan arewa suka yi ikirarin cewa sun cimma wajen zaben mutum biyu daga cikin masu neman takarar shugaban kasa a tutar jam`iyyar.
Dattawan sun ce PDP ba ta goyon bayan ɓangaranci, don haka ba daidai ba ne a kalli masu neman takarar ta fuskar yankin da suka fito.
A makon jiya ne shugaban ƙungiyar dattawan arewacin kasar, Farfesa Ango Abdullahi ya taka rawa wajen cimma maslahar, bisa jagorancin tsohon shugaban Najeriya Ibrahim Babangida.
Maslahar da suka cimma ita ce ta mara wa Sanata Bukola Saraki da Gwamnan jihar Bauchi State Bala Mohammed baya a matsayin 'yan takarar da arewacin kasar ta amince su tsaya takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP.
Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido wanda ya jagoranci taron dattawan na PDP a ranar Litinin ya ce PDP jam'iyya ce ta Najeriya, ba jam'iyyar arewa ba ko kudanci.
"Ba ma siyasar ɓangare ko addini,"
"Dukkanin ƴan takara sun cancanci zama shugaban ƙasa a ƙarƙashin PDP," in ji shi.
Dattawan sun ce za mu ci gaba da nuna goyon baya da yakin neman zabe domin tabbatar da dan takarar da suka tsayar a babban taron PDP a ranakun 28 da 29 ga watan Mayu ya yi nasara.
Matasayar dattawan
Sule Lamido ya ce ba daidai ba ne wani ya fito ce ya ce ga dan takarar PDP na arewa ko yan takarar PDP na kudu.
Ya ce kuskure ne sun taru su ce fitar da yan takara guda biyu - "domin hatsari ne a wayi gari a ce arewa ta fitar da dan takara, mutuncinmu zai zube."
"Ko ba a so arewa ita ce babba a Najeriya, bai kamata muna ƙorafi ba. Abin da aka ce an yi zai cuci PDP da arewa idan har ba mu yi nasara ba," in ji shi.
Ya ƙara da cewa wadanda suka fitar da ƴan takarar ba yan PDP ba ne kuma ba wakilan jam'iyyar ba ne.
Ya ce abin da suka amince shi ne a fitar da ɗan takarar PDP da zai kasance na ƴan Najeriya ba na arewa ko kudu ba.
Rabuwar kai a Kungiyar Dattawan Arewa

Shugabannin Kungiyar Dattawan Arewa a Najeriya sun nisanta kansu da matsayar da Farfesa Ango Abdullahi suka ɗauka.
Cikin wata sanarwa da babban jami'in da ke kula da yada labarai na kungiyar Dr Hakee Baba-Ahmed ya sanya wa hannu, kungiyar ta ce ba a shigar da kungiyar a cikin hanyoyin da aka bi na yanke wannan shawarar ba.
Sanarwar ta ce "'Yan takarar ne da kansu suka yi wannan yunkuri. Gwamna Aminu Waziri Tambuwal Gwamna Bala Mohammed da Bukola Saraki da kuma Malam Mohammed Hayatudeen sun sanar tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Babangida aniyarsu, kuma sun bukaci ya shiga cikin maganar a matsayinsa na dattijo."
Sai dai ba a matsayinsa na daya daga cikin jagororin Kungiyar Dattawan Arewa ya yi wannan aikin ba - ya yi shi ne a matsayinsa na Farfesa Ango Abdullahi, in ji sanarwar.
Saboda haka ne Kungiyar Dattawan Arewan ta ce ba da ita aka yi wancan aikin ba:
"Kungiyar Dattawan Arewa ba ta da alaka kai tsaye da wata jam'iyyar siyasa ko wani dan takara, kuma ta mayar da hankali ne wajen samar da shugabanni na gari a zabukan shekarar 2023. Kuma ta yi imani cewa akwai nagartattun 'yan takara da ya dace a bar wa jam'iyun siyasar kasar su zabo da kansu."











