Zaben 2023: Wa Buhari yake goyon baya ya gaje shi a jam'iyyar APC?

Hankali ya karkata kan ɗan lelen Buhari wanda shugaban ke goyon bayan takararsa a jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.
Manyan ƴan siyasar APC da dama ne suka ayyana sha'awarsu ta gadar kujerar shugaba Buhari. Yawancinsu makusanta ne ga shugaban kuma waɗanda suka yi tasiri ga samun nasararsa ta zama shugaban ƙasa.
Manyan ƴan siyasar da ake ganin na hannun daman Buhari sun haɗa da tsohon gwamnan Legas kuma jagoran APC Bola Ahmed Tinubu da mataimakin shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo da ministan sufuri Rotimi Ameachi da Rochas Okorocha da gwamnan Ekiti Kayode Fayemi.
Dukkanin Ƴan siyasar suna dogaro da samun goyon bayan shugaba Buhari, kuma har yanzu ya ƙi fitowa fili ya bayyana wanda yake goyon baya, kamar yadda ya nuna goyon bayansa ga wanda yake son ya zama shugaban jam'iyyar APC.
Ko da yake a kwanakin baya Buhari ya taɓa cewa duk da ba shi da wani ɗan takara da yake goyon baya a jam'iyyarsu ta APC mai mulki ya gaje shi amma idan ya bayyana shi za a iya halaka shi.
A wata hira da kafar talabijin ta Channels, shugaban ya ce "Ban damu da wanda zai gaje ni ba," yana nuni da cewa yana da ɗan takarar da yake goyon baya.
"A'a ba zan faɗa ba, saboda idan na faɗa za a iya kawar da shi. Gara na bar shi a sirrance," a cewarsa.
Wa Buhari yake goyon baya? Shin shugaban na tsaka mai wuya ne?
Sharhin Dakta Abubakar Kari
Masana kimiyar siyasa a Najeriya kamar Dakta Abubakar Kari na Jami'ar Abuja na ganin abu ne mai wahala a yanzu shugaban ya fito ya bayyana ɗan takararsa kada ya ƙara jefa jam'iyyarsa ta APC cikin ruɗani.
Masanin ya ce bai yi tsammanin Buhari yana tsaka mai wuya ba kan wanda zai goyi baya idan an zo zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar APC
A cewarsa maganar da Buhari ya yi kan yana da ɗan takara ba ya son ya fito fili ya bayyana, ya riga ya yi nazari ne kan wa yake so ya goyi baya. Don haka babu maganar yana cikin tsaka mai wuya.
Daga cikin waɗanda suka nuna sha'awarsu ta gadar kujerar Buhari akwai na ƙud da ƙud ga shugaban waɗanda a cikinsu ne ake ganin yake goyon bayan ɗaya daga ciki.
Tinubu - Ya yi tasiri sosai ga samun nasarar Buhari, yana cikin daya daga cikin tsanin da Buhari ya taka ya zama shugaban ƙasa saboda goyon bayan da ya ba shi a 2015 da 2019 a shiyar kudu maso yamma, ya yi tasiri sosai.
Osibanjo - mataimakin Buhari ne wanda suke tare tsawon shekarun mulkinsa, kuma akwai fahimtar juna tsakaninsu kuma fitowarsa ta samu sahalewar shugaban
Amaechi - Za a iya cewa rawar da ya taka kusan daidai ta ke da irin rawar da Tinubu ya taka ga samun nasarar shugaba Buhari a zaɓen 2015. Akwai rade-raden cewa kudin rotimi sun yi tasiri sosai wajen samun nasarar APC.
Amaechi shi ya yi wa Buhari daraktan kamfen a zaɓen 2015 - kuma cikin minisctocin Buhari babu wanda za a ce ya yi ayyukan da za a tuna Buhari kamar Rotimi Amaechi.
Wasu na ganin Amaechi dan gidan Buhari kuma da wahala idan ba shi shugaban yake goyon baya ba.
Rochas - Ya taka rawa ga samun nasarar shugaba Buhari a yankin ƙabilar Igbo da shugaban ke fuskantar adawa.
Okorocha ya daɗe yana ɗaga wa Buhari ƙafa a siyasa, musamman a zaɓukan fitar da gwani.
Amma mutum uku bisa dukkanin alamu - daga cikin wadanda suka ayyana sha'awar takarar shugaban kasa daga cikinsu ne ake ganin ɗan lelen Buhari zai fito.

Ƙalubale
Masananin na ganin za iya samun sarƙaƙiya a karshe kan wanda Buhari yake goyon baya ko zai iya nasarar samun tikiti.
Idan Buhari har ya fito fili ya ce ga wanda yake goyon baya, zai yi mumunan tasiri ga ita kanta takarar - wasu za su tirje sai sun yi takarar wanda zai iya kawo rarrabuwar kai kuma abu mai hatsari ga jam'iyyar gabanin zaɓen 2023.
Amma yadda shugaban ya ce yana goyon bayan wani, kamar ya yi wa sauran ƴan takarar hannun ka mai sanda ne, cewar suna iya yin takara amma yana da wanda yake goyon baya.
Kuma saurin fitowa ya bayyana wanda yake goyon baya ƙarara, zai iya sa wasu manyan jiga-jigan jam'iyyar su ji haushi su fice jam'iyyar.
fitowa a yanzu ya bayyana wanda yake so, zai iya tada kura da hayaniya a yi ta rikice wanda ba zai yi wa jam'iyyar kyau ba.











