Manyan 'yan siyasa da ke fafatawa a zaben fitar da gwani na takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC na 2023

A ranar Litinin shida ga watan Yuni ne jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, take fara gudanar da zaben fitar da gwani na masu son yi mata takarar shugabancin kasar a zaben 2023.
Jam'iyyar ta APC ta kayar da jam'iyyar PDP a zaben 2015 bayan, PDPn ta kwashe shekara goma sha shida tana mulki. Manyan 'yan jam'iyyar ne suke fafatawa domin ganin sun maye gurbin shugaban kasar Muhammadu Buhari a zaɓen 2023.
Kowanne ɗan takara ya bayyana manufofinsa da yake fatan ganin ya cimma idan ya yi nasara.
Cikinsu akwai mataimakin shugaban kasa da tsoffin gwamnoni da tsoffin ministoci da kuma 'yan majalisar dattawa.
BBC ta yi nazari kan manyan 'yan jam'iyyar APC da ke fatan ganin sun gaji Shugaba Buhari.
Yemi Osinbajo

Asalin hoton, Facebook/Professor Yemi Osinbajo
Mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo na daya daga cikin na farko-farko da suka bayyana aniyarsu ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023.
Farfesa Osinbajo ya bayyana tsayawa takarar ce a wani jawabi ta bidiyo da aka yada ta talabiji da sauran kafofin sada zumunta inda ya yi bayanin irin abubuwan da zai yi idan ya gaji Shugaba Muhammadu Buhari.
Osinbajo, wanda daga Kwamishinan Shari'a na Jihar Legas ya zama mataimakin shugaban ƙasa, ya ce ya tsaya takara ne domin inganta rayuwar 'yan kasar yana mai cewa a matsayinsa na mataimakin shugaban kasa yana da kwarewar shugabancin Najeriya.
"A cikin shekara bakwai, na bauta wa gwamnati a matakai daban-daban, kuma bisa umarnin shugaban kasa, na wakilci kasar nan a muhimman ɓangarori a ƙasashen waje. Na ziyarci kusan kafatanin kananan hukumomin Najeriya. Na je kasuwanni, da masana'antu, da makarantu da gonaki," in ji Farfesa Osinbajo.
Ya kara da cewa ya je gidajen talakawan kasar a yankuna daban-daba, sannan "na tattauna da kwararru a bangaren fasaha a Lagos, Edo, da Kaduna; da kuma taurarin Nollywood da Kannywood; da mawaka daga Lagos da Onitsha da kuma Kano. Kuma na yi magana da kanana da manyan 'yan kasuwa".
Mataimakin shugaban na Najeriya da ke da shekaru 65, ya ce ya samu wannan ƙwarewa ce domin ta zama silar fahimtar matsalolon Najeriya da kuma yadda zai magance su.
Baya ga kewayawa da zai yi a jihohi domin neman magoya baya, 'yan kwamitin yakin neman zaben sa za su shirya kuri'ar jin ra'ayin jama'a domin tattara shawarwari game da matakin da ya dauka na tsayawa takarar a zaben 2023.
Ana ganin Farfesa Osinbajo zai samu magoya baya, amma yadda zai ɓullo a siyasance ya kalubalanci manyan masu sha'awar takarar musamman ubangidansa Bola Tinubu shi ne abin jira a gani.
Bola Tinubu

Asalin hoton, Twitter/@officialABAT
A farkon watan Janairun wannan shekarar tsohon gwamnan Jihar Legas kuma jigo a Jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana anniyarsa ta takarar shuagabanci kasa.
Tsohon gwamnan, mai shekaru 70, ya ce ya ziyarci Shugaba Muhammadu Buhari domin fada masa anniyarsa ta karawa a zaben 2023.
A cewar Tinubu "na faɗa wa Shugaba Buhari aniyata, ban ji abin da ba shi na yi tsammanin ji daga gare shi ba, ya ƙarfafa min guiwa kamar yadda dumokuraɗiyya ta ba ni dama, amma har yanzu ban sanar da jama'ar Najeriya ba tukunna, ina ci gaba da tuntuɓa.
"Na shafe tsawon rayuwata ina fatan zama shugaban ƙasa, don haka me ya sa zan yi tsammanin jin abun da ya saɓa da wannan daga wajen shi, tsari muke yi da dimokuraɗiyya, don haka dole mu tafi a kan haka".
Bayan sanar da takarar tasa, akwai lokacin da ya fito yana shaida wa matasan Najeriya cewa za su yi shugabancin ƙasa amma sai bayan ya yi.
Tinubu ya buƙaci matasa su ba magabatansu dama. "Kun toshe wa magabatanku dama tun kafin ku zama shugaban ƙasa, idan kun zama shugaban ƙasa fa, za ku kore mu ne a gari?"
"Sai kun tsufa za ku zama shugaban ƙasa, kuma sai na riga zama shugaban ƙasa," in ji Tinubu.
Tun a bara ne hotunan takarar Tinubu suka fara karaɗe wasu jihohin Najeriya.
Har yanzu dai bai fito ta kafofin yada labarai kai-tsaye ya yi wa al'ummar Najeriya jawabi kan neman kujerar shugabanci da kuma manufofi ko abubuwan da zai yi idan ya yi nasara.
Amma ana ganin ana iya samun takun saka tsakanin Bola Tinubu da mataimakin shugaban kasa Yemi Osibanjo a neman kujerar mulki.
Ahmed Lawan

Asalin hoton, Twitter/@sen_ahmedlawal
Sanata Ahmed Lawan shi ne shugaban majalisar dattawan Najeriya. A haife shi ranar 12 ga watan Janairun 1959 a Gashua da ke jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya.
Ya yi karatunsa na firamare da Sakandare a Gashua tsakanin 1974 zuwa 1979, sannan ya kammala Digirinsa na farko a fannin Ilimin Kimiyyar Kasa a Jami'ar Maiduguri in 1984.
Ya yi Digirinsa na biyu a fannin Kimiyar Tattara Bayanan Doron kasa a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a 1990, sannan ya yi Digirin Digirgir a fannin Kimiyyar Tattara Bayanan Doron kasa da Fasahar Taswira a Jami'ar Cranfield da ke Birtaniya a 1996.
Ahmed Lawan ya fada harkokin siyasa inda a 1999 aka zabe shi a matsayin dan majalisar wakilai da ke wakiltar Bade/Jakusko a majalisar dokokin Najeriya. An sake zabensa a 2003. Sannan a 2007 a zabe shi a matsayin dan majalisar dattawan kasar domin wakiltar Arewacin Yobe. Sanata Lawan gogaggen dan siyasa ne kuma yana daya daga cikin 'yan majalisar da suka fi sanin harkokin majalisar dokokin kasar.
A yayin da yake bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasar, Sanata Lawan ya ce babban burinsa shi ne aiwatar da shirye-shirye da za su inganta rayuwar 'yan Najeriya.
Rotimi Amaechi

Tsohon Ministan Sufuri Rotimi Amaechi, mai shekaru 56, fitaccen dan siyasa ne da ya yi gwamna da kuma shugaban majalisar dokokin jihar Ribas da ke kudu maso kudancin Najeriya.
Amaechi ya ayyana takararsa ne a wani taron siyasa a garin Fatakwal.
Ya ce: "Na tsaya a gabanku don bayyana aniyata tare da gabatar da bukatar zama shugabanku na gaba".
Rotimi ya ce akwai dimbin ƙalubale da ake fama da su a Najeriya kuma burinsa shi ne share wa 'yan kasar hawayensu.
Ministan da ke bayani kai-tsaye ta shafinsa na Facebook ya ce abubuwan da zai mayar da hankali idan ya yi nasara su ne tsaro da rashin ayyuka da yakar talauci da kuma habbakar tattalin arziki.
Ameachi ya ce ya shafe shekaru 23 yana siyasa don haka yana da ƙwarewar da ake bukata kuma nan ba da jimawa ba zai soma gangami a kowane kusurwar kasar kama daga birni har zuwa kauyuka.
Mista Amaechi ya taba yin daraktan yakin neman zabe na Manjo Janar Muhammadu Buhari, lokacin da yake takarar shugabancin Najeriya.
Yahaya Bello

Asalin hoton, YAHAYABELLO/FACEBOOK
A ranar 2 ga watan Afrilu, Gwamnan Kogi Yahaya Bello ya ayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa, ƙarƙashin tutar jam'iyyar APC.
Gwamnan ya sanar da matakin ne a wani taron siyasa a Abuja.
Da yake jawabi ya yi alƙawalin cewa zai mayar da ƴan Najeriya miliyan biyu masu arziki da za su mallaki miliyoyi nan da 2030.
Ya ce ya fahimci cewa ci gaban Najeriya ya dogara ne da fitar da ƴan ƙasar daga talaucin da ya yi katutu.
Yahaya Bello kusan shi ne ke da mafi karancin shekaru cikin mutanen da suka fito zuwa yanzu karkashin inuwar jam'iyyar APC suna neman mulkin Najeriya. Gwamnan yana da shekaru 46 a duniya.
Gwamnan ya yi fice wajen yawan shirya taro da mu'amala da masu harkar fina-finai a Najeriya. Sannan yana cikin na gaba-gaba da ke yi wa shugaban kasar Muhammadu Buhari biyayya.
Sai dai masana na diga ayar tambaya kan kwarewarsa, musamman diba da ci gaban da za a zo a gani a jiharsa Kogi.
Ahmed Sani Yariman Bakura

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara mai shekaru 62, kuma jigo a jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya Senata Ahmed Sani Yarima ya sake ayyana aniyyarsa shi ma ta tsayawa takarar shugabancin kasar a zaben 2023.
Senata Yarima wanda tun a shekara ta 2007 ya fara fitowa takarar shugabancin kasar ya yi watsi da tsarin karba-karba a zaman abin da ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar duk da cewar ana ganin lokaci ne da ya kamata yankin kudancin kasar ya fitar Shugaban kasa na gaba.
Ya ce dama sun dagawa shugaba Buhari kafa ne a 2007, kuma a yanzu tun da wa'adinsa ya kare lokaci ya yi da zai fito a kara da shi.
Sanatan ya ce ya san matsalolin 'yan Najeriya na talauci da jahilci, kuma shi zai mayar da hankali wajen yakar wadannan abubuwa biyu.
Ya ce matsalolin tsaron da ake fama da shi duk saboda rashin ayyukan yi ne, don haka zai bijiro da tsare-tsaren da zasu saukaka wahalhalun 'yan Najeriya.
Rochas Okorocha

Asalin hoton, @REALROCHAS/TWITTER
Tun cikin watan Janairu tsohon Gwamnan Imo kuma ɗan Majalisar Dattawa, Sanata Rochas Okorocha, mai shekaru 59, ya bayyana sha'awarsa ta tsayawa takarar shugabancin Najeriya a babban zaɓen 2023.
Ya bayyana hakan ne cikin wata wasiƙa da ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan, inda shi kuma ya karanta wasiƙar a zaman majalisar.
Okorocha, wanda ɗan jam'iyyar APC ne mai mulkin Najeriya, na cikin 'yan kudu maso-gabashin ƙasar da ke bayyana aniyarsa ta yin takara a APC.
Rochas ya yi fice wajen ayyukansa na agaji musamman a jihohin arewacin Najeriya. Sai dai hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zangon kasa, EFCC, ta kama shi a makon jiya.
David Umahi
David Nweze Umahi wanda aka fi sani da Dave Umahi dan siyasa ne da yanzu haka yake matsayin gwamnan Jihar Ebonyi State da ke kudu maso gabas.
Mai shekara 58, Umahi ya tsunduma harkokin siyasa ne a 2007 a matsayin shugaban jam'iyyar People's Democratic Party, PDP, na riko na Jihar Ebonyi. Daga 2009 zuwa 2011, ya rike shugabancin jam'iyyar na jiha.
A 2011, Umahi ya zama mataimakin gwamnan jihar Ebonyi lokacin Gwamna Martin Elechi. Sai dai ya koma jam'iyyar APC inda aka zabe shi a matsayin gwamna a 2015.











