APC: Waɗanda suka yi nasara a zaɓen fitar da gwani na gwamnoni a Najeriya

An kwana ana gudanar da zaben fid da gwani na masu neman takarar mukamin gwamna a karkashin jam`iyyar APC mai mulki a wasu jihohin Najeriya, yayin da aka kammala a wasu, wasu kuma ana ci gaba da kirge.
Zaben dai ya gudana lafiya-lafiya a wasu jihohin, yayin da a wasu kuma aka fuskanci turjiya daga wasu `yan takara.
Jihar Kaduna na cikin jihohin da suka gudanar da zaben a cikiin dare, inda Sanata Uba Sani ya samu nasara. Sai dai zaben ya bar baya da kura, kasancewar daya daga cikin abokan hamayyarsa, Alhaji Sani Sha`aban ya ce bai amince ba:
''Idon duk wanda yake wannan guri ya san wannan ba zabe ba ne, kuma ba abin da za mu ce duka dan APC da wani ma dan siyasa da yake Jihar Kaduna abin zub da hawaye ne.''
''Ya kara da kokawa da cwa, ''In dai haka siyasa za ta ci gaba babu wanda zai yi sha'awarta ballantana ya fito ya ce zai yi wani abu.''
''Kowa a sanin kowa ba a yi zaben daligets a Jihar Kaduna ba. An je an yi wani list a gidan gwamnati kuma don ana ma sauri a yi list din wadansunsu ko lamba ma na APC ma ma'anan wai sunan 'yan jam'iyya ne babu su.'' in ji shi.
Ya ce, ''Wannan ba zabe ba ne, in aka ce ba za a bi hakki ba to ai APC ba ita kadai ce jam'iyya ba.''
Jihar Taraba; An yi harbi da bindiga;
A jihar Taraba kuwa, zaben ne ma ya gagara kwata-kwata, saboda wata hatsaniya da ta kaure, har ta kai ga wani harbi da aka yi da bindiga ya samu daya daga cikin malaman zaben.
Hakan ne kuma ya sa babban malamin zaben ya sanar da dage shi har sai abin da hali ya yi.
Jihar Kebbi
A jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriyar lami-lafiya aka yi zaben.
Bayan da malamin zaben, Honourable Idris Yahuza Yakubu, ya sanar da Dakta Nasir Idris a matsayin wanda ya samu nasara, nan take daya daga cikin abokan hamayyarsa, Abubakar Malam Shatiman Gwandu ya yi masa mubaya`a.
Jihar Kano
A jihar Kano mataimakin gwamnan jihar, Nasiru Yusuf Gawuna ne babban malamin zaben, Sanata Tijjani Yahaya, ya sanar ya ci zaben fid da gwanin na APC da kuri'a 2289.
Sai dai dan majalisar Wakilai ta tarayya Sha'aban Ibrahim Sharada, wanda ya zo na biyu da kuri'a 30, ya nuna bacin ransa kan yadda zaben ya gudana, inda tun kafin fara zaben ya aika da wata takardar korafi ga uwar jam'iyyar ta kasa game da yadda aka fitar da wakilai masu zaben, yana zargin an shirya magudi.
Jihar Katsina
A jihar Katsina Dikko Umar Rada ne ya yi nasara da kuri'a 506.
Jihar Jigawa:
A Jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi ne ne ya lashe zaben fitar da gwanin jihar bayan ya samu ƙuri'u 1,220. Cikin waɗanda ya kara da su akwai Ibrahim Hassan Hadejia da Faruk Adamu da Sabo Nakudu.
Jihar Gombe
Gwamnan Jihar Gombe Inuwa Yahaya shi ne ya yi nasara a zaben fitar da gwanin da aka gudanar a Jihar. Gwamnan ya lashe zaɓen fitar da gwanin ne ba tare da hamayya ba.
Borno
A Jihar Borno ma, gwamnan jihar Babagana Umara Zulum ne ya yi nasara a zaben fitar da gwanin ba tare da hamayya ba.
Yobe
Gwamnan Yobe Mai Mala Buni shi ma bai samu hamayya ba wanda hakan ya sa ya lashe zaɓen fitar da gwanin jihar.
Legas
A Jihar Legas, gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu ne ya yi nasara a zaɓen fitar da gwani na jihar.
Zamfara
A Jihar Zamfara kuwa, gwamna mai ci Bello Matawalle ne ya samu nasara a zaɓen fitar da gwani na jihar bayan shi ma ya yi takara ba tare da hamayya ba.
Adamawa
A Jihar Adamawa, Aishatu Binani ce ta yi nasara bayan a zaɓen fitar da gwanin da aka yi na APC. Cikin waɗanda ta kara da su har da tsohon gwamnan jihar Jibrilla Bindow da tsohon shugaban EFCC Nuhu Ribadu da Honarabul Abdulrazak Namdas.
Bauchi
A Jihar Bauchi kuwa, Air Marshal Saddique Baba Abubakar ne ya yi nasara a zaben fitar da gwani bayan ya kara da Nura Manu Soro da Sanata Halliru Jika da Dakta Musa Babayo.
Haka kuma akwai Honourabul Farouk Mustapha da Mahmood Maijama'a da Farfesa Muhammad Pate.











