Jiga-jigan PDP da ke fafatawa a zaben fitar da gwani na shugaban kasa na 2023

A ranar Asabar, 28 ga watan Mayu ne babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya, PDP take gudanar da zaben fitar da gwani na masu son yi mata takarar shugabancin kasar a zaben 2023.
A shekarar 2015 ne PDP ta sha kaye a hannun jam'iyyar APC bayan ta kwashe shekara goma sha shida tana mulkin kasar. Hakan ya mayar da ita babbar jam'iyyar hamayya a kasar, inda take fafutikar ganin ta sake kwace mulki daga APC a 2023.
Manyan 'yan siyasa ne da suka hada da tsohon mataimakin shugaban kasa da gwamnoni masu ci da tsoffin ma'aikatan gwamnati da 'yan kasuwa ne suke neman jam'iyyar ta tsayar da su takara.
BBC ta yi nazarin kan wasu manyan 'yan jam'iyyar adawa ta PDP da ke son gadar kujerar Shugaba Muhammadu Buhari a zaɓe mai zuwa.
Atiku Abubakar

Asalin hoton, Facebook/Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma daya daga jiga-jigan mutanen da suka kafa jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce ƴan kasar ne suka buƙaci ya tsaya takarar shugaban ƙasa a shekarar 2023.
Atiku ya bayyana hakan ne a Abuja lokacin da yake shirin ayyana takararsa.
Yana cikin ƴan takara masu yawan shekaru da ke son zama shugaban ƙasa.
An haifi Atiku Abubakar ranar 25 ga Nuwamban 1946 a Jihar Adamawa da ke Arewa Maso Gabas, kuma ya kasance jigon dan siyasa kuma hamshakin attajiri a Najeriya.
Tun bayan da Najeriya ta dawo mulkin dimokuradiyya cikin shekarar 1999, Atiku Abubakar ya kasance mataimakin shugaban kasar Najeriya na 11, a mulkin Shugaba Olusegun Obasanjo a tsakanin 1999 zuwa 2007
Ya mallaki katafariyar Jami'ar ABTI, wato American University of Nigeria a Jiharsa ta Adamawa.
Kamfaninsa na hada-hadar man fetur, mai suna Intels Nigeria Limited na hada-hada a kasashen Afirka da suka hada da Angola da Equatorial Guinea da Gabon da Sao Tome and Principe.
Tun cikin shekarar 1998 aka zabe shi Gwamnan Jihar Adamawa.
Daidai lokacin da yake a matsayin zababben gwamnan, sai zababben shugaban kasa ya zabe shi don ya mara masa baya a matsayin mataimakin shugaban kasa.
An rantsar da su ranar 29 ga Mayun 1999 a matsayin shugaban kasa da mataimakinsa bayan da suka lashe zabe a Fabrairun 1999.
Yunkurinsa na maye gurbin Obasanjo a karshen wa'adin mulkinsa ya ci tura bayan da ya yi ta yin takun-saka tsakainsa da Obasanjo, sannan ya fuskanci kalubalen shari'a, har ta kai ga daga bisani suka kare a Kotun Koli ta Najeriya, wadda ta bai wa Hukumar zabe ta INEC umarnin sanya sunan Atiku a jerin 'yan takara.
Ya yi takarar shugaban kasa ta farko karkashin tutar jam'iyyar AC, bayan da ya fice daga jam'iyyar PDP, al'amarin da ya haifar masa koma-baya a zaben 2007, inda ya zo na uku, bayan Umaru Yar'Adua na jam'iyyar PDP da Muhammadu Buhari na Jam'iyyar ANPP.
A zabukan da suka biyo bayan na 2007 Atiku ya ci gaba da taka rawa.
Atiku ɗan siyasa ne da aka sani da sauya sheka daga jam'iyyun siyasa.
Atiku Abubakar dan takarar shugaban kasa a karkashin tutar jam'iyyar PDP, ya fafata da Shugaban kasa mai ci, Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC mai mulki a ranar 16 ga Fabrairun 2019, zaben da bai yi nasara ba.
Nyesom Wike

Nyesom Wike - wanda cikakken sunansa shi ne Nyesom Ezebunwo Wike - an haife shi ne a ranar 13 ga watan Disambar 1963, a garin Rumuepirikom da ke karamar hukumar Obio-Akpor ta jihar Rivers a Kudu Maso Kudancin Najeriya.
Tun da farko ya fara aikin lauya ne bayan da ya halarci Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Rivers kafin daga baya ya shiga siyasa, kuma a halin yanzu shi ne gwamanan jihar Rivers na shida cikin jerin gwamnonin jihar da aka yi kawo yanzu.
Dan jam'iyyar adawa ta PDP ne.
Gwamnan jihar Rivers da ke kudancin Najeriya Nyesom Wike ya ce a shirye yake ya dauki nauyin jagorancin Najeriya saboda yana da kwarewar da ake bukata da za ta magance matsalolin rashin tsaro da koma bayan tattalin arzii da kasar ke fuskanta.
Mista Wike ya ce bai dace 'yan Najeriya su ci gaba da karaya ba, musamman kan abin da ya kira koma bayan tattalin arziki da jam'iyya mai mulki ta APC ta janyo.
Gwamnan na jihar Rivers ya fara shiga siyasa ne bayan da aka zabe shi a matsayi shugaban karamar hukumar Obio Akpor ta jihar ta Rivers a shekarar 1999, mukamin da ya rike har zuwa 2007, bayan da aka sake zabensa ga mukamin a 2003.
A 2007, gwamnan jihar a wancan zamanin Rotimi Amaechi ya nada shi shugaban ma'aikata a fadar gwamnan jihar da ke birnin Fatakwal.
A watan Yulin 2011, tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya nada shi karamin minista a ma'aikatar ilimi ta kasar, kuma daga baya ya samu ci gaba zuwa babban ministan ilimi a shekarar 2013.
Sai dai daga baya ya ajiye mukamin domin tsayawa takarar gwamnan jihar Rivers a zaben gwmnanoni 2015.
Bayan ya shafe shekara hudu na wa'adinsa na farko na gwamnan jihar, Mista Wike ya sake tsayawa takarar mukamin kuma ya lashe zaben, kuma an rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu 2019.
Yanzu yana cikin waɗanda suka ayyana kudirinsu na takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar adawa ta PDP.
Aminu Waziri Tambuwal

Asalin hoton, AFacebook/Aminu Waziri Tambuwal
Aminu Waziri Tambuwal shi ne gwamnan Jihar Sokoto da ke Arewa Maso Yammacin Najeriya, kuma yana cikin 'ya'yan jam'iyyar PDP da suka bayyana aniyarsu ta tsayawa takarar mukamin shugaban kasa a shekara mai zuwa.
Tsohon ɗan majalisar wakilan Najeriya ne, har ya taba rike shugaba majalisar a watan Yunin 2011 zuwa watan Yunin 2015.
An haifi Aminu Waziri ranar 10 ga watan Janairun 1966 a kauyen Tambuwal da ke jihar Sokoto.
Ya shiga makarantar Firamare a 1979 sannan ya shiga kwalejin horas da malamai ta Dogon-Daji a 1984.
Daga nan kuma ya shiga Jami'ar Usman Danfodio da ke Sokoto inda ya karanci aikin shari'a a 1991.
Ya kammala karatun koyon aikin shari'a da shekara daya a Legas a 1992.
Tambuwal ya fara koyon harkokin majalisa daga 1999 zuwa 2000 lokacin da yake aiki a matsayin mataimaki kan harkokin majalisa ga Sanata Abdullahi Wali, wanda a lokacin yake rike da mukamin shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa.
A 2003, ya nemi kujerar wakiltar mazabar Kebbe da Tambuwal a Sokoto.
An zabe shi a matsayin dan majalisar wakilai karkashin jam'iyyar ANPP.
'Yan watanni gabanin zaben gwamna a 2007, Tambuwal ya koma PDP tare da tsohon gwamnan Sokoto.
Tambuwal ya rike mukamai a majalisar wakilai. A 2005, ya zama shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai har zuwa lokacin da ya koma PDP.
Bayan an sake zabarsa a 2007, an kuma sake zabarsa a matsayin mataimakin shugaban bulaliyar majalisar.
Tambuwal ya kuma rike shugabancin kwamitocin majalisar da dama ciki har da kwamitin dokoki da kasuwanci da na sadarwa da kuma na shari'a.
Ya kuma kasance mamba a kwamitin wucin gadi kan yi wa kundin tsarin mulkin kasa garambawul.
A watan Yunin 2011 ne Aminu Waziri Tambuwal ya zama shugaban majalisar wakilan Najeriya ta 10 a cikin wani yanayi mai sarkakiya kuma na ba-saban-ba.
Tambuwal ya karbi ragamar majalisar ne daga hannun tsohon shugaban majalisar Dimeji Bankole.
Sakamakon rashin jituwa tsakanin majalisar ta wakilai da bangaren zartaswa, fadar gwamnati ta yi yunkurin ganin ta dasa shugabannnin majalisa da za su saurare ta.
Amma bisa rashin sa'a sai aka samu 'yan majalisar sun yi wa bangaren zartarwar kwanta-kwanta, inda suka zabi mutumin da ba shi bangaren na zartarwar ke so ba.
A lokacin sai da ta kai ga jami'an tsaron 'yan sanda sun kulle majalisar a ranar da aka sa ran zaben shugabannin majalisu, inda wasu da dama daga cikin 'yan majalisar suka yi ta haurawa gini ta kan katanga.
Rahotanni na cewa shi kansa Aminu Tambuwal sai da ya yi shigar burtu sannan ya samu ya shige duk da cewa wasu rahotannin na cewa Tambuwal ya kwana a cikin ginin majalisar ne.
A zaben fitar da gwani da jam'iyyar PDP ta gudanar domin fitar da dan takarar mukamin shugaban kasa, Aminu Wazirri Tambuwal ne ya zo na biyu a bayan abokin karawarsa Atiku Abubakar.
Yanzu yana cikin waɗanda suka ayyana kudirinsu na takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar adawa ta PDP a zaɓen 2023.
Bala Mohammed

Asalin hoton, Facebook/Bala Mohammed
An haifi Bala Mohammed a ranar 5 ga watan Octoban 1958, a karamar hukumar Alkaleri da ke jihar Bauchi A Arewa Maso Gabashin Najeriya.
Ya fara karatunsa na Firamare a shekarar 1965 a wata makaranta da ke kauyen Duguri, inda ya kammala a shekarar 1971.
Daga nan ya tafi makarantar Sakandire a shekarar 1972, inda ya kammala a shekarar 1976.
Ya halarci Kwalejin Kimiyyar Zane-Zane ta Shiyyar Arewa Maso Gabashin Najeriya daga shekarar 1977 zuwa 1979.
Daga nan kuma sai ya soma karatunsa na Digirin farko a Jami'ar Maiduguri da ke jihar Borno a shekarar 1979, ya kuma kare a 1982, inda ya karanci harshen Ingilishi.
Bala Mohammed ya kuma halarci Kwalejin Horas da Harkokin Gudanarwa a inda ya samu horo na dan wani lokaci.
Alhaji Bala Muhammad, tsohon dan-jarida ne, an shafe tsawon shekaru ana gungurawa da shi a harkar.
Tsohon edita ne da rusasshiyar jaridar 'The Mirage' a shekarar 1982 - 1983, sannan tsohon mai aika rahotanni ne ga kamfanin dillacin labaran Najeriya NAN.
Ya yi aiki da tsohuwar jaridar The Democrat, 1983 zuwa 1984, sannan ya yi aiki da ma'aikatar cikin gida ta Najeriya tsakanin shekarun 1984 - 1994.
Kauran Bauchi ya taba zama babban jami'in shigo da kayayyaki a ma'aikatar albarkatun kasa ta Najeriya tsakanin 1995 - 1997, kazalika ya taba zama mataimakin darakta a ma'aikatar wuta ta Najeriya tsakanin 1997 - 1999
A shekarar 2003 ne ya zama daraktan gudanarwa na hukumar sufurin jiragen ruwa ta Najeriya.
Daga bisani ne kuma ya yi ritaya daga aikin gwamnati a kashin kansa ya kuma tsunduma siyasa.
A shekarar 2007 ya tsaya takarar a karkashin jam'iyyar ANPP a matsayin dan majlisar dattawa mai wakiltar Bauchi Ta Kudu har ma ya yi nasara daga shekarar 2007 zuwa 2010.
A lokacin da tsohon shugaban Najeriya Umaru Musa 'Yar aduwa yake cikin halin jinya a Saudiyya, jam'iyyar adawa ta ANPP ta yi ta matsa lamba cewa a mika wa mataimakinsa Goodluck Jonathan mulkin kasar kafin ya samu lafiya.
Sanata Bala Muhammad na daga gaba-gaba wajen ganin an cimma wannan kuduri, don har a gaban majalisar dattawa sai da ya gabatar da bukatar hakan.
Wannan ce ta sa bayan mutuwar shugaban kasa 'Yar aduwa, da Jonathan ya hau mulki sai ya bai wa Bala Kaura mukamin ministan babban birnin tarayya Abuja, lamarin da ya sa Sanatan sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP daga ANPP, kamar yadda Buba Galadima ya shaida wa BBC.
Ya rike mukamin ministan Abuja daga shekarar 2012 zuwa 2015.
An ruwaito cewa akwai kyakkyawar alaka tsakaninsa da Shugaba Jonathan.
A lokacin zabukan 2019 ne Bala Muhammad ya tsaya takarar gwamnan Bauchi karkashin jam'iyyar PDP kuma hukumar zaben Najeriya wato INEC ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.
Wannan lamari ya sa EFCC ta dakatar da binciken da take masa saboda kariya da yake da ita a matsayinsa na gwamna kamar yadda tsarin mulkin kasar ya tanada.
Bayan zuwa kotuna har uku kan kalubalantar sakamakon zaben da abokin takararsa Mohammed Abubakar ya yi a Kotun Sauraron Kararrakin Zabe da Kotun Daukaka Kara, a karshe Kotun Koli ta tabbatar wa da Bala Kaura nasararsa.
Yanzu yana cikin waɗanda suka ayyana kudirinsu na takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar adawa ta PDP a zaɓen 2023.
Abubakar Bukola Saraki

Asalin hoton, BUKOLA SARAKI / FACEBOOK
An haifi Sanata Abubakar Bukola Saraki ne ranar 19 ga watan Disamba na shekarar 1962 a garin Ilorin na jihar Kwara da ke arewa ta tsakiyar Najeriya.
Sanata Bukola da ne ga Alhaji Abubakar Olusola Saraki, fitaccen dan siyasar kasar, kuma tsohon shugaban majalisar dattawa.
Ya yi karatunsa a King's College, Lagos daga 1973 zuwa 1978, da kuma kwalejin Cheltenham a London, tsakanin 1979 zuwa 1981.
Haka kuma ya yi digirinsa na farko a fannin likitanci a Kwalejin kiwon lafiya ta asibitin London tsakanin 1982 zuwa 1987.
Ya shiga harkokin siyasar Najeriya a shekarar 2000, kuma ya yi takarar gwamna, inda aka zabe shi a matsayin gwamnan jihar Kwara a shekarar 2003, sannan aka sake zaben sa a shekarar 2007.
Sanata Saraki, wanda ya shafe shekaru takwas a matsayin gwamnan jihar Kwara, ya daɗe yana fuskantar zargin cin hanci da kuma halatta kudin haramun.
A baya ya fuskanci shari'a bisa zargin kin bayyana kaddarorinsa amma Kotun Kolin Najeriya ta wanke shi a shekara ta 2018.
Haka kuma Sanata Saraki ya zama dan majalisar dattawan Najeriya a shekarar 2011, kuma an sake zaben sa a shekarar 2015.
An zabe shi a matsayin shugaban majalisar dattawa babu hammaya a ranar 9 ga watan Yunin 2015.
Yanzu yana cikin waɗanda suka ayyana kudirinsu na takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar adawa ta PDP a zaɓen 2023.
Anyim Pius Anyim

Asalin hoton, Anyi Pius Anyim / Twitter
Shi ma tsohon kakakin majalisar dattawan Najeriya Anyim Pius Anyim ya bayyana sha'awarsa ta zama shugaban Najeriya a shekarar 2023.
Mista Anyim ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara ne a birnin Enugu na yankin kudu maso gabashin Najeriya.
An haife shi ne a ranar 19 ga watan Fabrairun 1961 a karamar hukumar Ivo ta jihar Ebonyi, kuma ya halarci makarantar Ishiagu High School, inda daga baya ya je jami'ar jihar Imo da ke Uturu daga 1983 zuwa 1987.
Ya shiga siyasa a shekarar 1998 bayan da ya shiga jam'iyyar United Nigeria Congress Party (UNCP) kuma aka zabe shi ga mukamin sanata. Sai dai bayan mutuwar tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya Janar Sani Abacha, a wata Yunin 1998, an soke zaben.
Amma daga baya ya shiga jam'iyyar People's Democratic Party (PDP), a zamanin shugaban Najeriya Janar Abdulsalami Abubakar, inda ya sake tsayawa takara kuma aka zabe shi ga mukamin sanata a 1999.
Bayan da ya fara aiki, sai 'yan majalisar dattawan suka zabe shi a matsayin shugaban majalisar a watan Agustan shekarar 2000, bayan da aka sauke marigayi Chuba Okadigbo daga mukamin, kuma ya rike mukamin har zuwa watan Mayun 2003.
Ya taba rike mukamin sakataren gwamnati tarayyar Najeriya daga watan Mayun 2011 zuwa Mayun 2015.
Tsohon shugaban Majalisar dattawa da sakataren gwamnati ya fuskanci zargin hukumar EFCC na da karkatar da kuɗaɗen al'umma.
Yanzu yana cikin waɗanda suka ayyana kudirinsu na takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar adawa ta PDP a zaɓen 2023.
Dele Momodu

Asalin hoton, DELE MOMODU / FACEBOOK
Sai kuma Otunba Dele Momodu, wanda shi ma ya bayyana aniyarsa ta zama shugaban Najeriya bayan Shugaba mai ci Muhammadu Buhari ya sauka daga mukamin shugaban kasa a shekarar 2023 mai shigowa a karkashin jami'iyyar PDP.
An haife shi ne a watan Mayun shekarar 1960, kuma dan jarida ne mai zaman kansa mai wallafa wata mujalla mai suna Ovation International, baya ga zama da kasuwa.
Ya halarci jami'ar Ife, wadda aka sauya wa suna zuwa jami'ar Obafemi Awolowo University, da ke garin Ile-Ife a 1982.
Ya rike mukamin sakataren tsohon mataimakin gwamnan jihar Ondo Chief Akin Omoboriowo tsakanin 1983 zuwa 1985, kuma daga 1986 Momodu ya koma fadar basarake na Ife - wato Ooni of Ife, Oba Okunade Sijuwade Olubuse II.
Bayan ya bar aiki da Ooni na Ife, sai jami'ar Professional Studies, Accra, Ghana, ta ba shi digirin yabo ta Doctor of Humane Letters.
Ya shiga gwagwarmayar siyasa, inda a 1993, Momodu ya shiga kungiyar siyasa ta Moshood Abiola mai neman shugabancin Najeriya a wancan zamanin.
An kama shi daga baya kuma aka tsare shi a wani ofishin 'yan sanda a Legas, inda ya ce 'yan sanda sun azabtar da shi.
Gwamnatin mulkin soja ta wancan lokacin karkashin Janar Sani Abacha ta sake kama shi a 1995 kuma ta tuhume shi da aikata laifukan cin amanar kasa, kuma cikin laifukan da aka tuhume shi da aikatawa akwai na kafa wani gidan rediyo mai suna Radio Freedom wanda aka sauya wa suna zuwa Rediyo Kudirat (matar marigayi MKO Abiola) daga bisani - bayan da aka kashe ta.
Ya tsere daga Najeriya zuwa Birtaniya inda ya shafe shekaru uku yana zaman gudun hijira
Dele Momodu na da mata daya, Mobolaji Abiodun Momodu wadda ya aura watan Disambar 1992 kuma suna da 'ya'ya hudu.










