Newcastle na zawarcin Nunez, Liverpool na son Alexander Isak

Lokacin karatu: Minti 2

Nottinham Forest da Newcastle sun nuna sha'awarsu kan ɗanwasa Darwin Nunez mai shekara 25 wanda kuma yake buga wa Liverpool da Uruguay. Ana ganin ɗanwasan zai iya barin Anfield. (Teamtalk)

Yunƙurin Liverpool na sayen ɗanwasan Newcastle United da Sweden, Alexander Isak mai shekara 25, na ƙara jan hankali. (Givemesport)

Bayern Munich na shirin yin tayin fam miliyan 60 kan mai tsaron ragar Brighton da Netherlands Bart Verbruggen mai shekara 22. (Telegraph - subscription needed)

Kocin Manchester United Ruben Amorim na ƙyalla ido kan ɗanwasan Sporting da Portugal Francisco Trincao mai shekara 25, a matsayin wani ɓangare na ƙudirinsa na yi wa tawagar ƙungiyar garambawul a bazara. (Talksport)

Manchester United da Arsenal da Paris St-Germain da Bayer Leverkusen da Real Madrid da Atletico Madrid na zawarcin mai tsaron ragar Espanyol Joan Garcia, mai shekara 23. (AS - in Spanish)

Arsenal na son Garcia ɗan asalin Sifaniya ya zama golanta na biyu bayan David Raya kuma a shirye yake ya koma. (Athletic - subscription needed)

Arsenal da Manchester United da AC Milan da Bayern Munich na zawarcin ɗanwasan Leipzig Benjamin Sesko mai shekara 21 sai dai ɗanwasan ɗan asalin Sloveniya ya fi son komawa Premier. (Bild - in German)

Shi ma wani shahararren ɗanwasan Leipzig na iya komawa Old Trafford yayin da Manchester United ke nuna sha'awar ɗaukan ɗan wasan tsakiya na Holland Xavi Simons. (Teamtalk)

Aston Villa ce kan gaba wajen neman sayen ɗanwasan Chelsea da Ingila Noni Madueke, mai shekara 23. (Givemesport)

Chelsea da Manchester City na daga cikin ƙungiyoyin da ke duba yiwuwar sayen mai tsaron ragar Roma da Serbiya, Mile Svilar, mai shekara 25. (Caught Offside)

Newcastle sun saki wani bidiyo da ke tallata sabon filin wasa mai ɗaukan ƴan kallo 65,000 a Leazes Park, wata alama da ke nuna cewa suna shirin barin St James Park. (Guardian)

Collette Roche, mai kula da gudanarwa a Manchester United, ta zama ɗaya daga cikin masu neman babban muƙamin shugaban gudanarwa a Newcastle United. (Telegraph - subscription needed)

Southampton ta shirya raba gari da shugaban sashen ɗaukan ƴanwasa Darren Mowbray. (Daily Echo)