Ƙungiyoyin Premier shida na zawarcin David, United na son Ekitike

Lokacin karatu: Minti 2

Newcastle ta bi sahun Manchester United da Tottenham da West Ham da Chelsea da kuma Liverpool a zawarcin ɗanwasan Lille ɗan asalin Canada Jonathan David mai shekara 25. (i Sport)

Manchester United na ƙyalla ido kan ɗanwasan Everton Jarras Branthwaite, mai shekara 22. (Sun)

Liverpool za ta fafata da Arsenal a zawarcin ɗanwasan Franfurt mai shekara 22 Hugo Ekitike a kasuwar musayar ƴanwasa ta bazara. (Mirror)

Sai dai Manchester United da Newcastle da wasu manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Turai na rige-rigen sayen Ekitike. (Football Insider)

Nottingham Forest da Arsenal da Liverpool sun nuna sha'awar ɗaukan ɗanwasa Lorenzo Lucca, mai shekara 24., yayin da Manchester United da West Ham ke bibiyar ɗanwasa Oumar Solet mai shekara 25. (Messaggero Veneto, in Italian)

Liverpool na shirin buga kakar wasa mai zuwa da ɗanwasan Ingila Jarell Quansah, da rahotanni ke cewa Newcastle na zawarcinsa, sai dai Liverpool ɗin ba ta tunanin cefanar da ɗanwasan mai shekara 22. (Athletic - subscription required)

Besiktas, da ke ƙarƙashin tsohon kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer, na sha'awar sayen ɗanwasa Jaden Philogene, mai shekara 23 a kan aro. (Fotomac - in Turkish)

Manchester City na shirin sake ƙulla yarjejeniya da ɗanwasan Bayer Leverkusen Jeremie Frimpong mai shekara 24, daidai lokacin da ita ma Liverpool ke zawarcin ɗanwasan na Netherlands. (Teamtalk)

Nottingham Forest ta nuna sha'awar sayen ɗanwasan Belgium Alexis Saelemaekers kan aro daga hannun AC Milan. (Calciomercato - in Italian)

Liverpool na dakon babban tayi daga gasar Saudi Pro kan ɗanwasan Uruguay Darwin Nunez mai shekara 25. (Football Transfers)

Everton na zawarcin ƴanwasan Sunderland - Chris Rigg mai shekara 17 da Dan Neil mai shekara 23. (Teamtalk)

Millwall da Hibernian na daga cikin ƙungiyoyin da ke nuna sha'awarsu kan ɗanwasan Cheltenham Jordan Thomas mai shekara 23. (Football Insider)

Tottenham ta bayyana sha'awar dawo da tsohon daraktan wasanninta Fabio Paratici sai dai AC Milan ma na zawarcinsa. (Radio Rossonera - in Italian)

Bayern Muich na iya duba yiwuwar kiran ƴanwasan aro don su samu damar taka leda a Club World Cup, har da ɗanwasan Tottenham mai shekara 19 Mathys Tel. (Kicker - in German)