Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ana zargin Rudiger da Mbappe da Vinicius da aikata rashin da’a a wasansu da Atletico
Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai ta fara bincike game da zargin da ake yi wa 'yan wasan Real Madrid hudu na aikata rashin da'a a lokacin karawarsu da Atletico Madrid a zagayen 'yan 16 na gasar zakarun Turai.
Ana zargin Antonio Rudiger, Kylian Mbappe, Vinicius Jr and Dani Ceballos da yi wa magoya bayan Atletico abubuwan da ba su dace ba a lokacin da Madrid din ta yi nasara a karawar bayan bugun fanareti, wanda hakan ya ba ta damar kaiwa zagayen kwata-fainal.
Hotunan talabijin ya nuna dan wasan baya Rudiger yana yin alamar yanka wuya ga magoya baya bayan kammala bugun fanareti.
Yayin da shi kuma Mbappe aka gan shi yana yin kamar ya kama marainansa.
A makon da ya gabata ne Atletico ta kai wa hukumar ta Uefa koke kan lamarin.
Akwai yiwuwar 'yan wasan su fuskanci hukuncin dakatarwa idan gaskiyar zargin ta tabbata, sai dai babu tabbas ko za a yanke hukuncin kafin karawar Madrid din da Arsenal a matakin kwata-fainal.
Za a buga karawar farko ne tsakanin Arsenal da Real Madrid a filin wasa na Emirates da ke Landan a ranar 8 ga watan Afurilu yayin da za a yi karawa ta biyu bayan mako daya.
A cikin wata sanarwa, Uefa ta ce: "An nada mai bincike da zai yi alkalanci kan zargin aikata rashin da'a da ake yi wa 'yan wasa hudu na Real Madrid.
"Za a sanar da matakin da za a dauka a nan gaba," in ji sanarwar.