Yadda ƴanmatan Arsenal suka yi wa na Real Madrid yankan-baya

Lokacin karatu: Minti 1

Kowa ya yi tunanin cewa ƙafar Arsenal ɗaya ta fice daga gasar kofin zakarun Turai ta mata, kuma ba za su iya zuwa matakin kusa da wasan ƙarshe ba sai dai wani ikon Allah.

An yi tunanin hakan ne ganin cewa a karawar farko, Real Madrid ta doke Arsenal ne da ci biyu da nema.

Sai ga shi a karawar da aka yi ranar Laraba Arsenal ta fanshe ƙwallayen biyu tare da ɗora wa Real gyara, inda aka tashi Arsenal na da ƙwallo 3 Real Madrid na nema.

Wannan ne ya sanya jimillar ƙwallayen ya zamo Arsenal 3-2 Real Madrid

Ƴar wasa Alessia Russo ce ta haskaka a karawar, inda ta zura ƙwallo biyu a filin wasa na Emirates Stadium.

A yanzu tawagar matan ta Arsenal ta kai wasan kusa da ƙarshe inda za ta kara da tawagar Lyon a gasar cin kofin zakarun turan ta mata.