Mece ce Ingausa kuma wane tasiri za ta yi ga harshen Hausa?

Farfesa Abdalla Uba Adamu

Asalin hoton, Abdalla Uba Adamu

    • Marubuci, Isiyaku Muhammed
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 5

A duniyar zamani da cigaba musamman a ɓangaren fasaha, harshen Hausa ma yana samun sabbin fuskoki da salo daban-daban.

Ɗaya daga cikin waɗannan sabbin abubuwa da suka bijiro wa harshen Hausa shi ne Ingausa (EngHausa) – wato hanyar haɗa Turancin Ingilishi da Hausa a cakuɗa su wajen magana da rubutu a mu'amalar yau da kullum.

Yanzu haka, matasa da dama, musamman a kafafen sada zumunta, suna amfani da Ingausa wajen bayyana kansu cikin salo mai jan hankali.

Amma mece ce Ingausa? kuma mene ne tasirinta ga harshen Hausa?

Me ya sa ake yin Ingausa?

Engausa

Asalin hoton, Mustapha Habu Ringim

Game da dalilin da ya sa aka fara amfani da Ingausa (EngHausa), Farfesa Abdalla Uba Adamu ya ce harshe tamkar abu ne mai rai da ke buƙatar aro sabbin abubuwa, inda ya ce ''Harshe abu ne da ke mirginawa, yake arowa ya kuma bayar da aro ga wasu harsunan," in ji shi.

Ya ce zamananci ya zo da hakan, "har ya kai matsayin da mun riga mun cakuɗu da harshen Turancin Ingilishi ta yadda ya zamanto wasu abubuwa sai ka yi dogon tunani kafin ka fassara su zuwa Hausa, to idan akwai na Ingilishin kawai sai ka ɗauko ka liƙa, wannan shi ne EngHausa."

Farfesan ya yi misali da kalmar Ingilishi ta 'universe' wadda ya ce ba zai yiwu a fassara ta da sama ba, "saboda sky ke nan. Ita kuma 'universe' ta ƙunshi duniyoyi da dama da taurari," in ji shi, inda ya ce fassara irin wannan kalmar za ta yi wahalar gaske.

A nasa ɓangaren, Injiniya Mustapha Habu Ringim, shugaban kamfanin Engausa Global Tech Hub da ke jihar Kano, wanda ke koyar da matasa sana'o'i da fasahar zamani ta hanyar amfani da EngHausa, ya ce tun tuni suka fahimci akwai alheri a tattare da amfani da tsarin wajen ilimantar da mutane.

"Asali kalma ce da mutane ke amfani da ita, amma ba lallai sai haɗa Hausa da Ingilishi ba, ana nufin kawai haɗa kalmomi a isar da saƙo, har ya kai ana amfani da ita a ilimance."

Ya ce cibiyarsu ce ta fara hango cewa zai yi kyau ya zama ana iya haɗa Hausa da Ingilishi wajen koyar fasahar zamani da sauran ilimomi, "domin zai zama za a fi fahimta cikin sauƙi saboda akwai ƙarancin ƙwarewa a zallar Ingilishin a wajen mutanenmu."

Ya ce akwai matasa masu basira sosai amma Ingilishi yake musu cika wajen cika burinsu.

Amfani da Ingausa a ilimance

EngHausa

Asalin hoton, Mustapha Habu Ringim

Shugaban cibiyar ta Engausa ya ce asali kamfaninsu na One Chosen Global Technology ne ya ware ɓangare na Ingausa, "amma a shekarar 2019 sai muka lura shi ma zai iya zama da ƙafarsa, kuma daga lokacin zuwa yanzu mun koyar da ɗalibai sama da 7,000, wanda daga ciki akwai aƙalla guda 600 da suke buɗe kamfanoninsu, har sun ɗauki wasu aiki."

Ya ce amfani da tsarin ya zama hanya mai sauƙi wajen koyar da mutane, "tun ana ce mana gwamnati ba za ta karɓa ba, ba za mu je ko'ina ba saboda Najeriya tsarin ilimi an yarda ne kawai a koyar da ilimi da harshen uwa zuwa matakin ƙaramar sakandire," in ji shi.

Sai dai ya ce akwai tsari a hukumar NBTEA da ya ba mutane dama na koyar da ilimin sana'o'i da harshen uwa,

Ya ce har a jami'o'i da dama an sha gayyatarsa yana gabatar da lakca kan amfani da IngHausa.

Ko Ingausa zai yi wa Hausa lahani?

Sau da yawa masana na bayar da shawarar amfani da ainahin kalmomin da harshe ke da su, maimakon baƙi waɗanda ake arowa ko baddalawa.

Inda ake kallon hakan a matsayin wani abu da zai taimaka wa harshe daga fuskantar barazanar ɓacewa.

Wannan ne ya sanya wasu ke ganin cewa yawan tsoma kalmomi na Ingausa a cikin zantuka na yau da kullum zai iya haifar da ɓacewar wasu daga cikin kalmomin harshen Hausa na ainahi, musamman a tsakanin matasa.

Farfesa Abdallah ya ce dole hakan ya faru domin "ai ba za a zauna kullum a ce a yi ta amfani da kalma ɗaya ba. Yanzu idan ka ce akushi yara da yawa ba su san shi ba, haka ma masaki. To yanzu don adana su sai mu ce ba za a yi amfani da sababbin abubuwa ba?"

Ya ce al'ummar kowane zamani suna da kalmomin da suke samu, "mun gada kalmomi daga kakakkinmu, su kuma sun gada daga kakanninsu, haka mu ma za mu gadar da wasu ga jikokinmu," in ji Farfesa Abdallah.

Makomar Ingausa

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A game da yadda Farfesa Abdalla ke kallon makomar Ingausa, masanin ilimi ya ce dole nan gaba a amince da shi a tsarin bincike da nazarce-nazarce.

Ya yi misali da karin Ingilishi na Pidgin, inda ya ce da farko bai samu karɓuwa ba, "amma yanzu gidajen jarida na duniya suna watsa labarai da shi kuma ya karɓu."

Sai farfesan ya ce ba yana nufin asalin harshen ya mutu ba ne, "amma aro ya zama dole."

Shi ma Injiniya Rimgim ya ce burinsa cibiyar ta wuce koyar da sana'a, "ina so mu samu damar buɗe jami'a ko kwalejin ilimi da za a riƙa koyar da ilimin fasahar zamani da ƙere-ƙere kuma matasanmu su samu satifiket da zai yi daidai da na ko wace makaranta."

Ya ce yana fata ya ga EngHausa ya samu karɓuwa a tsarin ilimin Najeriya, inda zai zama ana iya amfani da shi a hukumance.

Ya ce a ilimin ƙirƙirarriyar basira, "idan ba mu yi amfani da harshen uwa wajen gina shi ba, to lallai za a tafi a bar mu a baya saboda za ta amfani da abin da take da shi ne."