Harsuna 10 da Hausa ke barazanar shafe su a arewacin Najeriya

...

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Aisha Babangida
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 3

Harshen Hausa ya kusan mamaye duka fannonin sadarwa a yankin arewacin Najeriya.

Ana magana da harshen a ƙauyuka da garuruwa da kasuwanni da makarantu da kafafen yaɗa labarai da sauran hulɗoɗin yau da kullum.

Wannan ya sanya Hausa ta zama harshe mafi rinjaye da mutane daga ƙabilu daban-daban ke amfani da shi wajen mu'amala da juna wanda hakan ya saka wasu ƙananan harsunan asali da dama ke fuskantar barazanar ɓacewa daga gare shi.

Dalilin haka ne BBC ta tuntuɓi Dakta Ibrahim Ahmed Birnin Gwari, malami a shashen nazarin harsunan Najeriya da kimiyyar harshe a jami'ar Kaduna domin samun ƙarin haske kan wannan batu.

Dakta Ibrahim ya ce harshen Hausa na yi wa sauran harsuna a Najeriya da wasu sassan duniya barazana kamar yadda binciken ilimi suka nuna.

Malamin ya ce harshe wani muhimmin al'amari ne a rayuwar ɗan'adam kuma baya ga tunani, harshe shi ne abu na biyu mafi daraja da Allah ya albarkaci ɗan'adam da shi.

"Da harshe Allah Ya bai wa ɗan'adam baiwa yadda zai gabatar da tunaninsa har a fahimce shi.

Harshen Hausa harshe ne na al'umma wadda ake kira da Hausawa kuma bincike da alamu sun nuna cewa harshe ne wanda aka fi amfani da shi musamman a arewacin Najeriya da kuma waɗansu sassa na Kudancin Jamhuriyyar Nijar.

Harsunan da Hausa ke yi wa barazana

Malamin jami'ar ya lissafa wasu daga cikin harsunan da ke fuskantar barazana daga Hausa a arewacin Najeriya da wuraren da ake magana da harsunan a ƙasar.

  • Fulatanci (Fulfulde) - jihohin Taraba da Yobe da Kano da Jigawa da Katsina da Zamfara da Sokoto da Gombe.
  • Katafanci da Kajenci da Jaba da Marwa da Kagoro - jihar Kaduna
  • Gera da Tera da Reshe - jihar Bauchi
  • Gwandara da Eggon - Jihar Nasarawa
  • Dakkaranci - jihar Kebbi
  • Gizimanci - jihar Yobe
  • Gbagyi - jihar Kaduna da Abuja
  • Yerwa da Manga – Reshe-reshen Kanuri da ke Borno
  • Zarma-Songhai – Nijar kusa da Najeriya
  • Shuwa Arab – jihar Borno da Taraba

Dakta Ibrahim ya ce a arewacin Najeriya, inda nan ne harshen Hausa ya yi kakagida, ƙabilu mamallaka sauran harsuna waɗanda ba su buwaya kamar harshen Hausa ba, a mafi yawan lokuta kamar ya zame musu dole su yi magana da harshen Hausa.

Me ya sa Hausa ke yi wa wasu harsuna barazana?

Dr. Ibrahim ya bayyana cewa Hausa tana daga cikin manyan harsunan Afirka da ake amfani da su wajen sadarwa a arewacin Najeriya da wasu sassan Nijar.

Yawan masu amfani da Hausa a matsayin harshe na farko na iya haura miliyan 60, sannan akwai kimanin miliyan 25 da ke amfani da ita a matsayin harshe na biyu.

A cewarsa, Hausa ta samu wannan matsayi ne saboda:

  • Ta fi yawancin ƙananan harsuna girma, shahara da buwaya.
  • Ana koyar da ita a makarantu da jami'o'i, har ma a wasu ƙasashen waje.
  • Ta samu matsayi a hukumomin gwamnati da kafafen yaɗa labarai.
  • Yawancin ƙabilu da ba Hausawa ba suna amfani da Hausa fiye da harshen asalinsu.
  • Hijirar mutane zuwa yankunan da ake magana da Hausa na sa yara su tashi ba tare da koyon harshen iyayensu ba.

'Ban iya harshena na asali ba'

BBC Hausa ta kuma tattauna da waɗansu mutane waɗanda ba Hausawa ba ne amma shi ne harshe na farko da suke amfani da shi duk da cewa suna da nasu harsunan asali.

Maryam Bello, ƴar asalin Fulani daga Kano, ta ce ta tashi ba ta iya Fulatanci ba, saboda Hausa ake yi a gidansu, makaranta da unguwa.

"Idan aka tambaye ni yare na, nakan ce Hausa/Fulani, amma gaskiya ban iya Fulatanci ba."

Bulus Musa, Bakatafe daga Kaduna, ya ce Hausa ta mamaye rayuwarsa tun yana ƙarami.

"Idan na haɗu da mutanen ƙabilata, yawanci Hausa muke yi da su. Idan wani ya yi min Katafanci, wani lokaci sai an fassara min."

Hausa na fuskantar barazana?

Dr. Ibrahim ya ce Hausa ma na fuskantar barazana daga Turanci da Larabci musamman a fannin ilimi da addini, da kuma yawan amfani da Ingilishi na zamani a shafukan sada zumunta da intanet."

Amma kuma malamin ya ce wannan barazanar ba ta kai irin wadda Hausa ke yi wa ƙananan harsuna ba.

Mece ce mafita?

A cewar Dr. Ibrahim, idan ana son harsuna su tsira, dole ne:

  • Iyaye su riƙa koyar da yaransu harsunan asali a gida.
  • A tabbatar da harsuna na gudana daga kakanni zuwa yara.
  • Gwamnati ta tabbatar da adalci ga duk harsuna a tsare-tsarenta.
  • A yi amfani da dukkan harsuna a makarantu.
  • Marubuta da mawaka su ƙarfafa rubutu da waƙa a harsunan asali.
  • A shigar da harsunan asali a shirye-shiryen rediyo, talabijin, da kafafen watsa labarai.
  • A ƙarfafa rubuta tarihi da al'adu a harshen asali.
  • Gwamnati ta kafa dokoki na kare harsuna daga ɓacewa.

Dr. Ibrahim ya ce duk al'umma ita ce ke da alhakin kare martaba da mutunci da daraja da ɗaurewar al'adunta da kuma kare harshenta daga fuskantar baraza da kuma ɓacewa.