Kalmomin Hausa 15 da wasu matasan yanzu ba su sani ba

Asalin hoton, Getty Images
Masana harshen Hausa na cikin wani yanayi na gaba kura baya sayaki dangane da yadda harshen na Hausa ke saurin karɓar baƙin kalmomi da kuma yadda wasu kalmomin harshen ke ƙara ɓacewa maimakon su zama ƙari ta yadda za su ƙara yalwar harshen.
Duk da cewa sun amince da nazarin da ke nuna cewa babu wani harshen da zai samu cigaba a duniya ba tare da zama hankaka ba wato ya mayar da ɗan wani nasa ba, kamar yadda harshen Hausa ke yi a kullum - wani abu da ya sa ake ganin haɓakar harshen a kullum.
Farfesa Sai'id Muhammad Gusau na daga cikin masu bayyana takaici dangane da ɓacewar da wasu kalmomi ke yi amma kuma a lokaci guda ya yarda da karɓar baƙin kalmomin da harshen ba shi da su.
"Aro al'ada ce ta duk wani harshe mai yaɗo. To amma ya kamata a kiyaye wajen aron kalmomin. Ya kamata a yi ƙoƙarin gaske wajen ganin an fassara baƙin abubuwa zuwa Hausa domin ka da watarana a wayi gari babu kalmomin na Hausa.
Amma idan babu yadda za a yi a nan ne sai a yi aro ɗin," in ji Farfesa Gusau, tsohon malami a sashen nazarin harsunan Najeriya da ke jami'ar Bayero, Kano.
Farfesa Gusau ya ce akwai kalmomin Hausa da dama da matasa a wannan zamanin kodai ba su san su ba ko kuma ma sun daina amfani da su sakamakon samun madadinsu.
Taure
Wannan kalma da a shekarun baya Hausawa ke amfani da ita wajen kiran bunsuru da ya riƙa.
To sai dai sakamakon cuɗanya da al'adu da al'ummu kalmar ta dusashe musamman a wannan ƙarni na 21, inda matasa da ƴan birni ke amfani da sabbin kalmomi.
"Yanzu sai dai ka ji ana kiran taure da kodai bunsuru ko kuma namijin akuya," in ji Farfesa Gusau.
Shela
Kalmar "Shela" na nufin sanarwa inda a zamanin da har zuwa ma wasu ƴan shekaru ake samun wani mutum da ke yawo kwararo-kwararo domin yin 'shela' wato sanarwa ga al'ummar gari ko kuma unguwa.
To amma a ƴan shekarun nan da wuya ka ji Hausawa na amfani da kalmar "Shela" a zantukansu da muhawarorin da kuma labarai a kaffaen watsa labarai.
Dauri
Ita ma wannan kalma ce ta harhsne Hausa da Hausawa a da ke amfani da ita da ke nufin "asali " ko kuma "tale-tale".
Wati idan aka ce abu ne da aka gada tun "dauri" ana nufin abu ne tun na asali ko kuma aka gada daga kaka da kanni a ƙasar Hausa.
To amma saboda yanayin zamani da sauyawar al'umma da harshen ba kasafai za ka ji jama'a a amfani da kalmar dauri ba.
"Tana daga cikin kalmomin da yanzu idan ka faɗa ƴan zamani ma ba za su fahimce ka ba,' in je Farfesa Gusau.
Mussa

Asalin hoton, Getty Images
A baya Hausawa na amfani da kalmar "Mussa" wajen bayyana dabbar da aka fi sani a yau da mage ko kuma kyanwa.
"Yanzu ka kwana kana cewa matasa mussa ba za su fahimta ba sai idan ka ce mage ko kuma kyanwa.2," in ji Farfesa Gusau.
Zazzafe ko Zazzahe
Wannan kalma na nufin ɗumame wato abincin da ya kwana aka ɗumama shi wadda harwayau ake yi wa kirari da zafi biyu.
"Lallai yanzu idan za ka kwana kana cewa matasa zazzahe ba za su taɓa fahimtar ka ba saboda su a yau abin da suka sani shi ne dumame," in ji Farfesa Gusau.
Fatari
A zamanin da Bahaushe yana kiran ɗantofi da fatari wani abu mai kama da gajeren wando da mata ke sakawa a zamanin da.
Mata kan saka shi ya zamar musu sutura da kuma wurin ajiya kamar su adana kuɗi a ciki wani lokacin ma sukan iya saka abinci kamar rogo.
Za a iya cewa fatari ya ɓace a halin yanzu sakamakon zamani da ya kawo "skirt" na mata.
Bante
Ita ma wannan kalmar malam Bahaushe ce ta "dauri" wanda ke nufin gajeren wando na maza amma ya fi kama da "pant" wato wandon ciki da maza ke sakawa a zamanin da.
A zamanin na da za ka iya ganin mutum sanye da bante kawai ba tare da riga ko wani abun da ya rufe jikinsa ba sakamakon a lokacin akwai talauci da kuma rashin cigaban zamani.
Dutse uku
Dutse uku na nufin "murhu" wanda ake girki a kai musamman a zamanin da lokacin da ake amfani da duwatsu guda uku wajen kafa murhun da za a dafa abinci.
To amma sakamakon zamani da kawo cigaba da ya yi wajen girki ya sa kalmar dutse uku ta ɓace tunda ba a amafani da duwatsu wurin yin murhu.
A yanzu haka ana amfani duwatsun ne kawai a lokutan bukukuwa da suka haɗa da bikin sallah inda ake dafa da soya nama da abinci mai yawa wanda ke buƙatar a kafa murhun duwatsu saboda yawansa ko kuma buƙatara a babaka masa wuta.
Adiko
Kalmar na nufin dankwali wanda mata ke ɗaurawa. Amma a yanzu kalmar ta ɓace sakamakon zamani da kuma yadda shi kansa ɗankwalin ya zowa al'umma.
"Ada ana kiran ɗan kwali da ko dai adiko ko kuma fatala. Duka mata ne ke ɗaura shi a kansu. Amma yanzu idan ba ka ce ɗankwali ba to da wuya a samu wanda zai fahimce ka," in Gusau.
Taguwa
Wannan kalmar Hausa ce da Hausawa a zamanin da ke amfani da ita wajen kiran riga da ake dora babbar riga a kai, amma sakamakon sauyin zamani kalmar ko dai ta ɓace ko kuma an bar wa tsoffi da mutanen ƙauye da manazarta.
"Ina takaici wai maɗinka su ce maka ba su san taguwa ba sai dai ka ce musu ƙaramar riga. Har gwara ma mutum ya kira ta da ƴarciki. Har yanzu a Sakkwato haka ake kiran ta," in ji Farfesa Gusau.
Tagiya

Tagiya kalma ce da Hausawa ke bayyana suturar da a zamanin yau ake kira da hula wadda ake sanyawa a kai domin suturce shi.
"Mu a da tagiya muka sani amma yanzu idan ka kwana kana cewa tagiya ƴan zamani ba za su fahimta ba. Sai ka ce hula.
To gwara-gwara ma ita wannan kalmar ba za ka ce ta ɓace ba tunda har yau akwai masu kiran ta da tagiya. Irin wannan ake cewa ƙaruwa a harshe idan aka samu ƙarin kalmomi a daidai lokacin da ake ci gaba da amfani da kalmomin harshen." Kamar yadda Farfesa Gusau ya yi ƙarin haske.
Kuyafa
Kalma ce da ke nufi "cokali" a yau duk da dai a zamanin da can Hausawa na amfani da kuyafa wanda aka sassaƙa daga itace ne, to amma bayan zuwan cokali da ludayi na bature sai aka zubar da na sassaƙar tare da sunan nasu.
"Kai zamani ma da cigaban da aka samu ya sa ma a yau cokali ya zama na roba ba ma ƙarfe ba. Amma mu a zamaninmu kuyafa muka sani kuma wanda aka saƙa daga itace kamar dai yadda ake sassaƙa akushi," in ji Gusau.
Akushi
Kafin zuwan Bature da ya kawo tangaran da kuma haduwar Bahaushe da mutanen kudancin Najeriya da suka fito da kwano, a ƙasar Hausa abin da aka sani a matsayin abin zuba abinci shi ne akushi.
Akushi ana sassaƙa shi daga itace kamar yadda ake sassaƙa turmi ko kuma kuyafa da masu sana'ar sassaƙa ke yi a zamanin da.
"Shi wannan akushi yana mazaunin kwanon cin abinci ne ko kuma 'food flask" da zamani ya zo da shi. Akushi na iya riƙe zafin abinci har na wani lokaci." In ji Farfesa Gusau.
Talle
Talle ita ce kalmar da Hausawa ke amfani da ita ga tukunyar ƙasa wadda ake yin miya da ita a zamanin da.
Masu sana'ar gini ko kuma magina ne ke yin ta domin dafa miya. Kuma ana dora ta ne a kan murhu dutse uku irin na da a yi ta ba ta wuta har sai miyar da naman cikinta sun nuna.
Idan talle ta daɗe ana amfani da ita ta akan ga tana tsatstsafo da mai daga cikin saboda yadda ta saba da shan mai sakamakon yin ta da aka yi da ƙasa.
Duk da cewa kalmar ta ɓace amma wasu a wannan zamanin sakamakon wasu `bayanai da suke ji kan ingancin tallen ya sa yanzu haka gidaje har na ƴan zamani na amfani da talle wajen girka miya.
Tulu

Asalin hoton, Getty Images
Tulu ma ya fuskanci barazanar zamani inda yanzu haka idan ba a ƙauye ba ko kuma wurin da babu sukuni da wuya ka ga tulu idan dai ba a magina ba.
Tulu shi ne wata dabarar da Bahaushe ke da ita ta adana ruwa ya yi sanyi tunda a lokacin ba shi da na'urar sanyaya ruwa ko abinci wato firji.
Hausawa kan ajiye tulu ƙari a kan randa. Yayin da ake amfani da tulun domin sanyaya ruwa kamar firji ko kuma "dispenser" a yanzu, ita kuma randa akan yi amfani da ita ne a matsayin wurin tara ruwan da za a yi amfani da shi wato kamar a yanzu a ce tanki.











