Muradu biyar da Donald Trump ke son cimmawa kan ƙarin haraji

Donald Trump

Asalin hoton, Reuters

    • Marubuci, Anthony Zurcher
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, North America correspondent in Washington
  • Lokacin karatu: Minti 5

A makon da ya gabata ne Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da gagarumin ƙarin haraji kan ƙasashen duniya 60, wanda ya jawo durƙushewar kasuwar hannun jari ta duniya da lalata alaƙa tsakanin ƙasar da ƙawayenta.

Amma wannan shirin ko kuma mafi yawansa ya zama na toka tun bayan da Trump ya sanar da dakatar ko kuma rage yawansa a kan ƙasashen tsawon kwana 90, amma kuma ya ci gaba da yaƙin kasuwanci da China.

Saboda wannan jinginewar, ko Trump ya kusa cim ma muradansa kan kasuwanci?

Ga wasu abubuwa biyar da muka yi nazari kan muhimman muradan nasa a fannin kasuwanci?

1) Yarjejeniyar kasuwanci mafi kyau

Abin da Trump ya ce: Tsawon lokaci, ƙasashe sun daɗe ana sace arzikin ƙasarmu, da zalintar ta a kusa da nesa, ƙawayenmu da abokan gabarmu

Shiirin Trump da farko ya nakasa ƙasashe a faɗin duniya, inda aka saka wa kowace ƙasa ƙarin kashi 10 cikin 100 (ciki har da tsibiran da babu mutane a wurin) da kuma "ƙarin ramuwa" kan ƙasashe 60 da ya ce sun fi zalintar ƙasarsa.

Hakan ya jefa ƙawaye da kuma abokan gabar Amurka cikin ruɗani game da tattalin arzikinsu.

Cikin sauri Fadar White ta yi kurarin cewa kusan dukkan shugabannin duniya sun nemi Shugaba Trump domin tattaunawa don ƙulla yarjejeniya da rage harajin - "sama da 75", a cewar sakataren kasuwanci Scott Bessent.

Duk da cewa Trump bai fitar da jerin ƙasashen da ya ce suna "yi masa bambaɗanci" ba, Amurka ta ce tana tattaunawa da Koriya ta Kudu da kuma Japan.

ABIN LURA: Abokan kasuwancin Amurka na da wa'adin kwana 90 kacal don su cim ma yarjejeniya da Trump. Amma tun da ana tattaunawa Trump na da damar cim ma wasu muradansa da ya sa a gaba.

2) Ƙarfafa masana'antun Amurka

Abin da Trump ya ce: Ayyukan yi da masana'antu za su farfaɗo a ƙasarmu...Za mu yi wa masana'antunmu allurar ƙaimi.

Trump ya daɗe yana ikirarin cewa ƙarin haraji babbar hanya ce ta gina tattalin arzikin Amurka. Yayin da wasu masana'antun za su iya ƙara ayyukan samar da abubuwa a yanzu, dole ne wasu su jira lokaci mai tsawo.

Salon sakawa da cirewa na shugaban ƙasar a makon da ya gabata ya jawo rashin tabbas sosai. A yanzu da wuya a iya hasashen inda haraje-harajen za su tsaya, da kuma masana'antun da za su fi samun kariya.

ABIN LURA: Idan ana sakawa ana cire haraji kawai saboda shugaban ƙasa na son hakan, akwai yiwuwar kamfunna - a Amurka da sauran ƙasashe - za su durƙushe kuma su noƙe daga ɗaukar duk wani muhimmin mataki har sai ƙura ta lafa.

3) Yaƙi (na kasuwanci) da China

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Abin da Trump ya ce: Ina girmama Shugaba XI na China sosai, da China kanta, amma suna zalintar mu.

Bayan sanar da ƙarin haraje-harajen ranar Laraba, jami'an White House sun yi gaggawar faɗin cewa Trump ya yi hakan ne saboda dirar wa China abokiyar adawarsu.

"Su ne manyan abokan adawar Amurka a wajen kasuwanci," kamar Sakatare Bessent ya faɗa wa maneman labarai, "tabbas su ne matsalar duniya a wajen kasuwanci", kamar yadda ya ƙara da cewa.

Idan Trump na neman yaƙi da China to ya taro wa kansa - ko da kuwa shugaban da muƙarrabansa sun ce burinsu shi ne a samu matsaya.

A ranar Laraba, Trump ya zargi tsofaffin shugabannin Amurka, ba China ba, kan halin da ake ciki. Kafin haka, mai magana da yawun Trump Karoline Leavitt ta ce shugaban zai yi "murna sosai" idan China ta nemi a tattauna.

ABIN LURA: Ko da a ce irin wannan yaƙin shi ne abin da Trump ke nema, yin sa da ƙasa ta biyu mafi girman tattalin arziki a duniya da kuma ƙarfin soji, na da haɗari sosai. Kuma akwai yiwuwar Amurka ta ɓata wa wasu ƙawayenta rai da take buƙata domin yin nasara.

4) Ƙarin kuɗin shiga

Abin da Trump ya ce:Yanzu loakci ya yi da za mu ci gaba, kuma a yunƙurin cim ma hakan za mu yi amfani da tiriliyoyin dala wajen biyan bashin da ake bin mu kuma cikin sauri.

Yayin zaɓen shugaban ƙasa da ya gabata, Trump ya sha kurin cewa ƙarin harajinsa zai kawo ƙarin kuɗaɗen shiga, wanda Amurka za ta iya yin amfani wajen cike giɓin kasafin kuɗi, da cike giɓin harajin da aka yafe wa wasu, da kuma kuɗin gudanar da wasu shirye-shiyen gwamnati sababbi.

Wani bincike da cibiyar Tax Foundation ta gudanar a shekarar da ta gabata ya gano ƙarin harajin kashi 10 cikin 100 - wanda shi ne Trump ya zaɓa a yanzu na aƙalla kwana 90 - zai kawo wa ƙasar dala tiriliyan biyu na kuɗin shiga cikin shekara 10.

Domin a gane ƙarara, tsarin rage haraji da majalisar dokokin Amurka ta saka a kasafin kuɗi zai iya lashe dala tiriliyan biyar cikin shekara 10 masu zuwa, a cewar cibiyar Bipartisan Policy Center.

ABIN LURA: Trump na neman ƙarin kuɗin shiga, kuma idan bai janye ƙarin harajin kashi 10 da ya saka wa kowace ƙasa ba, da kuma ƙarin haraji kan wasu kayayyaki na musamman, zai cim ma burinsa - musamman dai har zuwa lokacin da Amurkawa za su koma amfani da kayayyakin cikin gida wanda zai sa kuɗaɗen su rage shigowa.

5) Raguwar farashi ga Amurkawa

Abin da Trump ya ce:Gaba ɗaya, ƙara yawan kayan da ake samarwa a cikin gida zai jawo ƙarin gogayya da kuma saukar farashi. Wannan zai zama babbar dama ga Amurkawa.

Masu sharhi da ƙwararru sun yi ta bayanin dalilin da ya sa Trump ya aikata abin da ya aikata a makon da ya wuce. Shi yana neman sauko da kuɗin ruwa ne, ko kuma rage darajar dalar Amurka, ko kuma jawo ƙasashen duniya da ƙarfin tsiya zuwa teburin tattaunawa kan kasuwanci? Shi kansa shugaban bai yi wata magana kan waɗannan abubuwa ba.

Abin da ya fi magana a kai shi ne, rage wa Amurkawa farashin kayayyaki - kuma ya yi alƙawarin cewa shirinsa zai magance hakan. Yayin da farashin makamshi ya ragu a tun bayan sanar da harajin, babu mamaki saboda rashin tabbas ne kan fargabar da hakan zai jawo.

Abin da masana suka fi amanna a kai shi ne, ƙarin harajin zai jawo hauhawar farashi saboda ana ɗora su ne kan kayan da ake shigarwa. A shekarar da ta wuce, cibiyar Tax Foundation ta yi hasashen cewa haraje-harajen kashi 10 cikin 100 zai jawo ƙarin farashi na dala tiriliyan 1.253 a shekarar farko.

Masana sun ce hakan zai fi shafar Amurkawa da ba su samun kuɗaɗe masu yawa.

ABIN LURA: Ƙarin haraji kan kayayyakin ƙasar waje ba hanya ce mai ɓullewa ba - kuma zai iya jawo wa siyasar Trump matsala da ma kimar jam'iyyarsa a zaɓuka masu zuwa.