Yadda Trump ya yi wa dokokin duniya hawan kawara da jefa shugabannin Turai cikin ruɗani

Hoton wasan dara.
    • Marubuci, Allan Little
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 8

Wannan ne lokaci mafi wuya da tsaron ƙasashen yamma ya shiga rikita-rikita tun bayan kawo karshen yaƙin duniya na II. Kamar yadda wani masani ya faɗa, "Trump na janyo ce-ce-ku-ce a mulkinsa". Amma waɗanne ƙasashe za su ja gaba yayin da Amurka ke juya baya?

Da misalin karfe 9 na safe a watan Fabrairun 1947, Jakadan Birtaniya a Washington, Lord Inverchapel, ya shiga ofishin harkokin wajen Amurka domin bai wa sakataren harkokin wajen ƙasar, George Marshall, wasu sakonnin diflomasiyya biyu, inda ya jaddada muhimmancinsu; ɗaya a kan ƙasar Greece, ɗayan kuma Turkiyya.

Birtaniya ta faɗa wa Amurka cewa ba za ta ci gaba da tallafawa dakarun gwamnatin Girka ba waɗanda ke faɗa da ƴan ta-da-ƙayar baya, ganin yadda bashi yayi mata katutu da kuma cewa ta gaji da ba da tallafin saboda wasu dalilai.

Birtaniya dai ta riga da ta sanar da shirinta na ficewa daga Falasɗinu da kuma Indiya da kuma Masar.

Amurka ta ga cewa akwai babban barazana da Girka za ta iya faɗa wa ciki, musamman hannun ɓata-gari, ko kuma karkashin kulawar Soviet. Kuma idan ta rasa Girka, Amurkar na tsoron cewa Turkiyya ita ce ta gaba, abin da zai bai wa Moscow iko da tekun Bahar Rum ciki har da watakila mashigar Suez mai muhimmanci.

Ana cikin haka a cikin dare, kwatsam sai Amurka ta tashi haikan don cike giɓin da Birtaniya ta bari.

Shugaba Harry S. Truman.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaba Truman ya ce Amurka za ta marawa ƙasashe marasa karfi

"Wannan zai zama tsari na Amurka wajen tallafawa mutanen da nuna turjiya ga ƙoƙarin iko da su da wasu ke son yi," Shugaba Harry Truman ya sanar.

Shi ne kuma abin da ya faro abin da aka fi sani da manufar Truman. A cikin manufar akwai cewa batun taimakawa wajen kare dimokraɗiyya a waje na da muhimmanci ga muradun Amurka.

Abubuwa biyu sun bi baya na tsare-tsaren Amurka: ɗaya shi ne wani shirin taimako don sake gina tattalin arzikin Turai da ya samu tawaya, da kuma kirkiro da ƙungiyar tsaro ta Nato a 1949, wadda aka yi da niyyar kare mulkin dimokraɗiyya daga Tarayyar Soviet da yanzu ta faɗaɗa ikonta a faɗin sassan gabashin Turai.

Abu mai sauki ne ganin hakan a matsayin yadda jagorancin yamma ya tashi daga Birtaniya zuwa Amurka.

Amurka, ta fito daga yaƙin duniya a matsayin ita ɗaya tilo - inda ta yi ta nuna ikonta a faɗin duniya, ta kuma shafe lokuta bayan yaƙin duniya na II wajen sake gyara kimarta a duniya.

Sai dai ana ganin cewa turbar da Amurkar ke a kai na son sauyawa a yanzu.

Shugaba Trump ya gana da muƙarraban gwamantinsa a Washington

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Donald Trump shi ne shugaban ƙasar Amurka na farko tun bayan yaƙin duniya na II da ya fito ya kalubalanci rawar da Amurka ke taka wa a duniya

Donald Trump shi ne shugaban ƙasar Amurka na farko tun bayan yaƙin duniya na II da ya fito ya kalubalanci rawar da ƙasarsa ke taka na gomman shekaru. Kuma yana yin haka ne ta hanyar da mutane ke ganin cewa tsohon dokar shugaban ƙasa ba ta aki - sannan sabuwar doka ba ta fara aiki ba.

Tambayar a nan ita ce, waɗanne ƙasashe ne za su ja gaba? Kuma, yayin da tsaron Turai ke cikin wani hali da ba a taɓa gani ba, shin shugabanninta za su mayar da martanin da ya kamata?

Kalubale ga tarihin Truman

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sukar dokokin ƙasa da ƙasa na 1945 da shugaba Trump ya yi har yanzu ba a manta ba.

Kusan shekara 40 da suka wuce, ya soki tsarin Amurka na kare mulkin dimokraɗiyya a duniya, a cikin wasu jaridu guda uku.

"Tsawon gomman shakaru, Japan da sauran ƙasashe na cin moriyar Amurka," ya rubuta a 1987. "Me ya sa waɗannan ƙasashe ba su biyan Amurka rayuka da kuma biliyoyin daloli da take rasa wa wajen kare muradunsu?

"Duniya na yi ƴan siyasar Amurka dariya yayin da muke kare jiragen ruwan da ba namu ba, ɗauke da man da ba mu buƙata, zuwa ga ƙawayen da ba za su taimaka ba."

Matsaya ce da ya sha nanatawa tun bayan komawarsa mulki karo na biyu.

Kuma fushin da wasu suka yi a cikin gwamnatinsa kan abin da suke gani a matsayin dogaro da Turai ta yi kan Amurka, an ga hakan a wasu sakonni da aka bankaɗo na hare-hare kan ƴan Houthi a Yemen a makon nan.

A cikin sakonnin, wani shafi ɗauke da sunan mataimakin shugaban Amurka JD Vance ya rubuta cewa ƙasashen Turai za su ci moriyar hare-haren. Ya ce: "Na tsani sake ceto Turai."

Wani shafi, mai ɗauke da sunan sakataren tsaro Pete Hegseth, ya mayar da martani bayan minti uku: "Mataimakin shugaban ƙasa: Ina tare da kai kan batun tsanar Turai. Abin ya yi yawa."

Shugaba Trump da mataimakinsa JD Vance

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A sakonnin da aka bankaɗo, wani shafi ɗauke da sunan mataimakin shugaban Amurka JD Vance ya rubuta cewa: "Na tsani sake ceto Turai."

Matsayar Trump ba ta tsaya kaɗai ga sukar waɗanda ya ce suna cin moriyar Amurka.

A lokacin fara wa'adin mulkinsa na biyu, alamu sun nuna ya yi na'am da shugaba Vladimir Putin na Rasha, inda ya faɗa wa Rasha cewa ba za a bai wa Ukraine damar zama mamba a ƙungiyar Nato ba, kuma kar ta ɗauka cewa za ta sake samun yankuna da ta rasa a wajen Rasha.

Mutane da dama sun ga haka a matsayin sadaukar da abubuwa biyu kafin ma a fara tattaunawar tsagaita wuta. Bai buƙaci komai daga wajen Rasha ba.

A ɗaya ɓangaren, masu goyon bayan Trump na ganin Putin a matsayin babban jagora mai ɗauke da abubuwa iri ɗaya da Trump.

Ga wasu, Putin aboki ne "a lokacin yaƙi".

Donald Trump da Putin.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Trump ya faɗa wa Rasha cewa ba za a bai wa Ukraine damar shiga Nato ba kuma kar ta sa ran cewa za ta sake karɓan iko da yankunan da ta rasa

Manufofin harkokin waje na Amurka a halin yanzu, ya ta'allaka ne ta hanyar wajabcin kare al'adunta. Tsaron Turai ya shiga cikin wani hali kuma tsakanin masu ra'ayin mazan jiya da ke rashin jituwa kan manufofin Amurka.

Wasu na ganin rarrabuwar kawuna ta zarce ra'ayin Trump kuma Turai ba za ta iya zama kawai tana jiran wa'adinsa na mulki ya kare ba.

Ed Arnold, babban jami'in bincike a wata cibiya da ke Landan ya ce "Amurka ta rabu da kimar Turai." "Wannan yana da wahala [ga Turawa] saboda yana nufin cewa yana da tsari, al'adu da kuma yiwuwar dogon lokaci."

'Ba za mu ci gaba da bai wa Turai tsaro ba'

Fadar White House ta ce ba za ta ci gaba da bai wa Turai tsaro ba, kuma ƙasashen Turai su kare kansu.

"Idan ƙasashen Nato ba su biya ba, ba zan ba su tsaro ba. Ba zan ba su tsaro ba," in ji Trump a farkon watan nan.

A tsawon shekara 80, tsarin tsaron Turai na kunshe cikin daftari na biyar na yarjejeniyar Arewacin Atlantic, wanda ya bayyana cewa hari kan ƙasa ɗaya, tamkar hari kan sauran ƙasashe.

A watan da ya gabata a Downing street, kafin ziyararsa zuwa fadar White House, Firaministan Birtaniya Sir Keir Starmer ya faɗa min a wata tattaunawa cewa ya yi na'am kasancewa Amurka ce babbar mamɓa a ƙungiyar Nato har yanzu kuma Trump ya ci gaba da tsayawa kan daftari na biyar.

Wasu ba su da tabbas kan haka.

Donald Trump.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaba Trump ya faɗa a farkon watan nan cewa ba zai bai wa ƙasashen Nato tsaro ba idan ba su biya kuɗaɗe ba.

Ben Wallace, wanda shi ne sakataren tsaro a gwamnatin Conservative da ta gabata, ya faɗamin a farkon watan nan cewa: "Ina tunanin daftari na biyar na Nato na buƙatar goyon baya.

"Idan Tura, ciki har da Birtaniya ba su tashi haikan ba, suka mayar da hankali kan tsaro da kuma ɗaukar batun da muhimmanci, to karshen Nato ya zo kuma hakan karshen daftari na biyar ne.

"A yanzu, ba zan iya tabbatar wa gidana cewa daftari na biyar ɗin zai yi aiki ba idan Rasha ta iya kai hari... Ba zan iya cewa ko Amurka za iya kai ceto ba."

A cewar kuri'ar ra'ayin jama'a da wani kamfani a Faransa mai suna Elabe ya gudanar, ya ce kusan kashi uku na Faransawa a yanzu na tunanin cewa Amurka ba ƙawar Faransa ba ce. Yawancin mutane a Birtaniya da da kuma da yawa a Denmark, waɗanda suka kasance ƙawayen Amurka a tarihi, ba su tunani mai kyau a kan ta yanzu.

"Ba za a iya kwatanta irin ɓarnar da Trump ya yi wa Nato ba," a cewar wani mai sharhi kan al'amuran yau da kullum Robert Kagan, wanda kuma ya kasance mawallafi a wata cibiya a Washington - da ya kasance dadaɗɗen mai sukar Trump.

"Ƙawancen ya dogara kan Amurka wanda kuma ba shi da wani alfanu a yanzu, idan za mu faɗi gaskiya".

Haka kuma, Trump ya kasance shugaban Amurka na farko da ya faɗa wa Turai cewa su nemi kuɗaɗe don tallafawa tsaronsu. A 2016, Barack Obama ya buƙaci ƙawayen Nato su ƙara kuɗaɗen da suke warewa ɓangaren tsaro, inda ya ce: "A wasu lokuta Turai tana sako-sako da batun tsaronta."

Shin an fara samun rarrabuwar kawuna ne tsakanin ƙasashen yamma?

Duka wannan babban farin ciki ne a wajen Putin. "Ɗaukacin tsarin tsaron Turai na taɓarɓarewa a kan idonmu," kamar yadda ya faɗa a bara. "An ɗanne Turai a ɓangaren ci gaban tattalin arziki, da saka cikin ruɗani da kalubale kamar ƙaura da rasa ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da kuma al'adunta.

A farkon watan Maris, kwanaki uku bayan ganawar Volodymyr Zelensky mai muni da Trump da mataimakinsa Vance a fadar White House, wani mai magana da yawun fadar Kremlin ya ayyana cewa "lokacin karyewar yamma ta fara".

Ganawar shugaba Donald Trump da shugaba Volodymyr Zelensky a fadar White House da ke Washington

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ganawar Zelensky mai cike da ruɗani da Trump da mataimakinsa Vance a fadar White House a farkon watan nan ta janyo mai magana da yawun fadar Kremlin cewa "karyewar yamma ta fara"

"Ka dubi abin da Rasha ke son cimmawa a Turai," a cewar Arminda van Rij, shugaban shirin Turai a Chattam House. "Abin da take so shi ne janyo ruɗani da wargaza Turai. Tana so ta karya Nato, kuma ta samu Amurka ta janye dakarunta daga can.

"Kuma a halin yanzu lokaci ake jira. Saboda Rasha na janyo ruɗani a faɗin Turai. Tana karya gwiwar Nato. Ba ta samu ganin Amurka ta janye dakarunta ba a Turai ba, amma a cikin watanni kaɗan, waye ya san inda muka dosa?"