Hanyoyin da sabon harajin Trump zai shafi tattalin arzikin Najeriya

Donald Trump

Asalin hoton, Reuters

Lokacin karatu: Minti 3

Najeriya na cikin jerin ƙasashen duniya da suka fuskanci sabon ƙarin haraji da Shugaban Amurka Donald Trump ya sanya wa kayayyakin da ƙasashen duniya fiye da 50 ke shigarwa Amurka.

A ranar Laraba ne Trump ya sanar da sanya wa Najeriya harajin kashi 14 cikin 100 na kayayyakin da take shigarwa Amurka.

Matakin na zuwa ne a lokacin da tattalin arzikin duniya ke cikin wani hali, wani abu da masana ke fargabar cewa zai ƙara haddasa tashin farashin kayyaki a duniya.

Ƙarin ya shafi wasu ƙasashen Afirka da dama, ciki har da Najeriya da Ghana da Afirka da Kudu da sauransu.

Da fari Shugaba Trump ya sanya harajin kashi 10 kan duka kayayyakin da ake shigarwa Amurka, da kuma ƙarin harajin "ramuwa" kan gomman ƙasashen Afirka da suka sanya haraji kan kayayyakin Amurka.

Ƙasashen Afirkan da Trump ya sanya wa ƙarin harajin "ramuwar" sun haɗa da Afirka ta Kudu (kashi 30) da Lesotho (kashi 50) da Madagascar (kashi 47) da Mauritius (kashi 40), sai kuma Botswana (kashi 37).

Ta yaya matakin zai shafi tattalin arzikin Najeriya?

Kasuwar Legos

Asalin hoton, Getty Images

Farfesa Muhammad Muntaqa Usman masanin tattalin arziki, kuma malamai a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya ya ce matakin zai shafi Najeriya ne saboda martanin da za ta mayar.

Ya ce dama akwai damar mayar da martani, duk ƙasar da ya aka sanya wa haraji tana da damar mayar da martani.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

''Don haka ita ma Najeriya da a yanzu ya sanya wa kayayyakinta da ke shiga Amurka, ƙarin harajin kashi 14, ita ma yanzu za ta mayar da martani ta hanyar ƙara kashi 14 cikin 100 na kayyakin Amurka da ake shigowa da su ƙasar,'' in ji masanin tattalin arzikin.

Ya ci gaba da cewa idan Najeriya ta ƙara mayar da martani to hakan zai shafi tattalin arzikinta da ma walwalar ƴan ƙasarta.

''Ta wani fannin gwamnati za ta samu ƙarin kudin shiga, saboda kayyakin Amurka da ake shigowa da su ƙasar, amma a gefe guda kuma ƴan ƙasa za su wahala, saboda ƙarin da gwamnati ta yi kayyakin Amurka da suke saya'', in ji shi.

Ya ce kayyakin Amurka da ake shigar da su ƙasar za su ƙara tsada, wanda kuma hakan ba zai yi wa ƴan ƙasar masu amfani da kayyakin Amurka dadi ba.

''Kuma tsadarsu zai shafi ƴan ƙasar ta yadda tsadar rayuwa za ta kawu musamman kan wadannan kayayyaki, kuma hakan zai gurguntar da tattalin arzikim ƙasar, musamman idan babu wasu kayan da za a iya canja su da su'', in ji Farfesa Muntaqa.

Kayayyakin da Najeriya ke shigarwa Amurka

Masanin tattalin arzikin ya ce kayayyakin da Najeriya ke fitar da su zuwa Amurka sun haɗa da man fetur, da sauran ƙananan kayayyakin ayyukan hannu.

Akwai kuma ma'adinin haɗa robobi, da cocoa, da ƙarafa, da sanholo, da auduga, da wasu duwatsu masu daraja.

Me ya kamata gwamnatin Najeriya ta yi?

Bola Tinubu

Asalin hoton, Bayo Onanuga/X

Farfesa Muntaqa ya ce abin da ya kamata gwamnatin Najeriya ta yi shi ta sake nazarin kayyakin da take fitar da su zuwa Amurka.

''Su masu tafiyar da tattalin arzikin su tsaya su yi nazari cikin shekara biyar da suka wuce waɗanne kayayyaki ne ake fitar da su zuwa Amurka, shin za a iya karkatar da su zuwa wasu ƙasashen kuma su samu shiga'', a cewarsa.

Sai dai ya ce kasuwa ce za ta tabbatar da haka, ''saboda ba lallai ba ne kayyakin da take fitarwa zuwa Amurka, ana buƙatarsu a wasu ƙasashen kamar Rasha ko China ba''.

Haka ma ya ce yana da kyau da dubi kayyakin Amurka da shigar da su Najeriya, su kuma yi nazarain muhimmancinsu ga rayuwar ƴan ƙasar.

"Misali kamar a ce kayan aikin asibiti, kayan koyo da koyarwa, ko kuma wasu kayyaki ne da ake buƙatarsu domin a ciyar da ƙasar gaba, a duba a yi nazari a gane cewa idan aka sanya wa wadannan kayyaki haraji a matsayin martani, to ina za a samo wasu da za a maye gurbinsu', in ji shi.