Jerin ƙasashen duniya da Trump ya lafta wa haraji

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da ƙarin sabon haraji ga ƙasashen duniya a ranar Laraba bisa dalilin cewa hakan zai bai wa Amurka damar bunƙasa tattalin arziƙinta.
Sabon harajin da Trump ɗin ya sanar bisa dogaro da wani umarnin shugaban ƙasa ka iya jefa matsalar tattalin arziƙi a faɗin duniya.
To amma shi shugaban na Amurka ya yi amannar cewa lafta harajin ya zama dole domin cimma daidaito ta harkar kasuwanci tsakanin Amurkar da sauran ƙasashen duniya da kuma kare ayyukan yi da masana'antu na ƙasar tasa.
Ƙasashen Afirka da harajin ya shafa
- Lesotho - 50%
- Madagascar - 47%
- Mauritius - 40%
- Botswana - 37%
- South Africa 30%
- Najeriya - 14%
- Kenya - 10%
- Ghana - 10%
- Ethiopia - 10%
- Tanzania - 10%
- Uganda - 10%
- Senegal - 10%
- Liberia - 10%
Ƙasashen da aka ɗora wa harajin kaso 10%
Wani babban jami'i a fadar White House ya shaida wa manema labarai tun ma kafin Donald Trump ya sanar da ƙarin harajin cewa Amurkar za ta sanya haraji na kaso 10 ga dukkan wasu kayayyakin da ake shigar da su Amurkar kuma ana sa ran za su fara aiki ranar 5 ga watan Afrilu.
Hakan na nufin cewa duk wani kamfanin da ke shigar da kaya zuwa Amurka to dole ne sai ya biya gwamnati harajin.
Ƙasashen da za su fuskanci wannan harajin su ne:
- Burtaniya
- Singapore
- Brazil
- Australia
- New Zealand
- Turkiyya
- Colombia
- Argentina
- El Salvador
- Haɗaɗɗiyar Dular Larabawa
- Saudiyya
Ƙasashen da za su fuskanci haraji na musamman
Fadar White House ta ce Amurka ta lafta harajin ramuwar gayya kan wasu ƙasashe.
Kuma harajin zai fara a ranar 9 Afrilu.
Jami'an gwamnatin Trump sun ce ƙasance da abin ya shafa suna lafta wa kayayyakin Amurka harajin da ya wuce ƙima. Ƙasashen su ne.
- Tarayyar Turai: 20%
- China: 54%
- Vietnam: 46%
- Thailand: 36%
- Japan: 24%
- Cambodia: 49%
- Afirka ta Kudu: 30%
- Taiwan: 32%
Babu ƙarin haraji kan Canada da Mexixo
Harajin na kaso 10 bai shafi ƙasashen Canada da Mexico ba duk da cewa da farko su ne waɗanda Trump ke haƙo.
A baya dai Trump ya sanya harajin kaso 25 kan duk wasu kayayyaki da ke shiga Amurka daga ƙasashen biyu.
Kaso 25 kan shigar da motoci Amurka
Shugaba Donald Trump ya tabbatar da cewa harajin kaso 25 a kan dukkan motocin da ake shigar da su Amurka ya buɗe sabon babin sabuwar Amurka.
Shi kuma wannan harajin zai fara aiki ne ba tare da ɓata lokaci ba.











