Da gaske ɗaga tutar wata ƙasa a Najeriya laifin cin amanar ƙasa ne?

Masu zanga-zanga a Kano

Asalin hoton, Social Media

Bayanan hoto, A Kano aka fara ganin tutocin Rasha yayin zanga-zanagar da aka fara ranar Alhamis da ta gabata
    • Marubuci, Umar Mikail
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 5

Abubuwa da dama sun faru yayin zanga-zangar da 'yan Najeriya ke yi kan matsin rayuwa, amma ɗaga tutocin ƙasar Rasha da wasu suka dinga yi na kan gaba cikin waɗanda suka fi jan hankalin mahukuntan ƙasar.

Tun daga ranar Asabar - rana ta uku da fara zanga-zanga - aka lura da tutocin Rashar da wasu masu zanga-zanga ke ɗagawa a jihar Kano, daga baya kuma sai abin ya yaɗu zuwa sauran jihohi musamman na arewacin Najeriya.

Rundunar sojin Najeriya ta kwatanta lamarin da "cin amanar ƙasa" kuma ta ce ba za ta amince da yin hakan ba.

“Muna gargaɗi da babbar murya, kuma shugaban ƙasa ya ce mu faɗa muku cewa ba za mu amince da duk wani da ke ɗaga tutar wata ƙasa ba a Najeriya," a cewar Babban Hafsan Tsaro na Najeriya Manjo Janar Christopher Musa jim kaɗan bayan ya gana da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ranar Litinin.

"Yin hakan cin amanar ƙasa ne," in ji janar ɗin.

Sai dai kuma akwai dokokin mulkin Najeriya biyu daban-daban da suka yi tanadi game da cin amanar ƙasa da kuma amfani da tuta da hatimin Najeriya (cort of arms).

Masu zanga-zanga

Asalin hoton, Social Media

Bayanan hoto, Da yawan masu ɗaga tutar Rasha na cewa suna neman taimakon ƙasar ne

A gefe guda kuma, hukumar shige da fice ta ƙasa a Najeriya ta ce ta gano cewa wasu 'yanƙasar ne da ke zaune a ƙasashen waje ke ɗaukar nauyin masu ɗaga tutocin na Rasha.

Shugabar hukumar shige da fice ta Najeriya, Kemi Nandap, ta faɗa yayin taron manema labarai ranar Talata cewa: "Mun tattara sunayensu kuma muna saka musu ido. Muna aiki da sauran hukumomin tsaro...duk lokacin da suka yi ƙoƙarin shigowa Najeriya za mu tabbatar mun miƙa su hannun hukumomin da suka dace."

Da yawan masu ɗaga tutocin kan ce suna neman Shugaba Vladmir Putin na Rashar ya kawo musu ɗauki game da halin matsi da suke ciki a Najeriya, kodayake gwamnatinsa ta nesanta kanta daga kiraye-kirayen cikin wata sanarwa.

Rundunar 'yansandan Najeriya ta ce ta kama wasu telolin da ke ɗinka tutar ta Rasha da ake ɗagawa, amma ba ta faɗi adadinsu ba.

Baya ga tutar ta Rasha da suke ɗagawa, wasu da yawa sun dinga kiraye-kirayen sojojin Najeriya su ƙwace mulki daga hannun 'yansiyasa.

Wani bidiyo da aka yaɗa a intanet ya nuna yadda wasu matasa ke ta yi wa sojoji kirari a harshen Hausa tare da neman su ƙwace mulki yayin da sojojin ke rarrashinsu da su daina yin hakan.

Mene ne cin amanar ƙasa a dokokin Najeriya?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Cin amanar ƙasa gundumemen laifi ne mai faɗi da ya ƙunshi laifuka iri-iri.

Domin fahimtar mene ne cin amanar ƙasa kamar yadda dokokin Najeriya suka tanadar, mun tuntuɓi Farfesa Nasir Adamu Aliyu na Jami'ar Bayero ta Kano kuma mai lambar girma ta babban lauyan Najeriya wato SAN, ga kuma abin da ya ce:

A taƙaice, cin amanar ƙasa ya ƙunshi juya wa ƙasa baya ta hanyar yi wa haɗinkanta barazana, ko zagon-ƙasa wajen kifar da gwamnati, ko kuma shigo da wasu cikin ƙasa domin su taɓa martabarta.

Najeriya na da kundin dokoki biyu na Penal Code (wanda jihohin Arewa ke amfani da shi) da kuma Criminal Code (da sauran jihohi ke amfani da shi), kuma dukkansu sun tanadi dokoki kan cin amanar ƙasa.

Sashe na 410 na kundin Penal Code ya ce cin amanar ƙasa shi ne ƙaddamar da yaƙi kan 'yancin ƙasa. Amma kundin Criminal Code ya fi fayyace ma'anar.

Laifin cin amanar ƙasa iri biyu ne; "treason" (babban laifin cin amanar ƙasa) da kuma "treasonable felony" (cin amanar ƙasa mai matsakaicin girma). Sashe na 37 na kundin Criminal Code ya ce duk mutumin da ya yi yunƙurin ƙaddamar da yaƙi don ya firgitar ko kuma tumɓuke shugaban ƙasa ko gwamnan jiha ya aikata cin amanar ƙasa (treason) kuma hukuncinsa shi ne kisa.

Shi kuma "treasonable felony" shi ne mutum ya yi yunƙurin tumɓuke gwamnati ta hanyar da ta saɓa wa doka, kuma hukuncinsa shi ne ɗaurin rai-da-rai. Misali a nan shi ne, mutum ya tara wasu 'yandaba ɗauke da makamai yana zanga-zanga kuma ya ce dole sai gwamna ko shugaban ƙasa ya sauka daga muƙaminsa.

A taƙaice dai, laifin cin amanar ƙasa shi ne yunƙurin tumɓuke gwamnati ba ta hanyar da doka ta tanada ba.

Ɗaga tuta kawai ta wata ƙasa ba laifin cin amanar ƙasa ba ne

Idan muka duba dokar amfani da tuta da kuma hatimin Najeriya (Flags and Coats of Arms Act), wadda ta bayyana yadda yakamata a yi amfani da tuta da kuma hukunci kan wulaƙanta ta, ɗaga tutar wata ƙasa kawai ba zai zama laifin cin'amar ƙasa ba har sai an duba niyyar da ta sa mutumin ya ɗaga ta.

Sashe na uku na wannan doka ya tanadi cewa duk wanda zai ɗaga wata tuta da aka ware wa wani sashe, ko ma'aikata, ko shugaban ƙasa, to dole ne sai ya nemi izini daga ministan da yake kula da ɓangaren, idan ba haka ba kuma ya yi laifi.

Hukuncin saɓa wa wannan doka kuma ya tanadi cin tarar naira 100, ko kuma naira 10 kan duk kwana ɗaya da ya cigaba da aikata laifin bayan laifin farko da aka kama shi da aikatawa.

Amma kuma sashe na biyar na wannan doka ya tanadi cewa duk wanda zai ɗaga wata tuta (kowace iri) ba tare da wani dalili ba sai don kishin ƙasa kawai to haƙƙi ne a kan sa ya ba da hujjar yin hakan.

Saboda haka, idan masu ɗaga tutar Rasha suka ce suna yi ne domin kishin cewa Rasha na taimaka wa ƙasashe kamar Nijar a ɓangaren tattalin arziki shi ya sa su ma suke neman shugaban ƙasa (Bola Tinubu) ya koma hulɗa da Rasha maimakon ƙasashen Yamma to ba su aikata laifin cin'amanar ƙasa ba.

Amma duk wanda ya ɗaga tuta da niyyar neman Rasha ta zo Najeriya ta kifar da gwamnatin ƙasar to ya aikata laifin cin'amanar ƙasa.

Mene ne tasirin ɗaga tutocin Rasha yayin zanga-zanga?

Tun daga lokacin da masu zanga-zangar suka fara ɗaga tutocin na Rasha masu sharhi suka fara kallon abin ta fuskoki da dama.

Ɗaya daga cikinsu shi ne Audu Bulama Bukarti, sanannen lauya ɗan Najeriya mazaunin Birtaniya, wanda ya ce yin hakan akasin 'yanci ne.

"Daga tutar wata ƙasa ba 'yanci ba ne kuma zai ƙara ta'azzara halin da muke ciki ne," kamar yadda ya wallafa a shafukansa na sada zumunta.

Wasu matasa da yawa a shafukan zumunta kan ce sun fara ɗaukar tutar Rasha ne saboda sun lura cewa hukumomin Najeriya sun fi tsorata da ita.