Yadda dokar hana fita ta shafi 'yankasuwar Kano

Kasuwar Beirut
Bayanan hoto, Kasuwar Beirut ta sayar da wayoyin hannu ta kasance fayau da tsakar ranar Litinin sai masu gadi kawai
    • Marubuci, Umar Mikail
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 4

Ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi damun mazauna birnin Kano a arewa maso yammacin Najeriya shi ne samun wani dalili da zai hana su fita kasuwa, kuma halin da ake ciki kenan yanzu haka sakamakon tarzomar da ta biyo bayan zanga-zanga kan matsin rayuwa.

Duk da cewa gwamnatin jihar ta sassauta dokar hana fitar da aka saka tun ranar Alhamis, 'yan kasuwar jihar da dama ba su iya fita ba, abin da ya ƙara jefa su cikin halin matsi baya ga wanda suke ciki sakamakon raguwar cinikayya a kasuwannin.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar da saka dokar ce ta tsawon awa 24 bayan wasu ɓata-gari sun farfasa tare da wawashe kayayyaki a shagunan ‘yankasuwa da gine-ginen gwamnati yayin zanga-zangar da aka fara ranar Juma'a.

Ƙarin abin da ya ta’azzara al’amuran ‘yankasuwar na Kano shi ne yadda maƙwabtan jihohi na Kaduna da Katsina da Jigawa suka saka dokar hana fitar, duka saboda tarzomar ɓata-garin.

“Mun gama ciniki da wani, amma ina ji ina gani na haƙura da ribar naira 30,000 da zan samu saboda kafin ya fitar da kayan zuwa jihar Kaduna lokacin dokar hana fita ya yi,” kamar yadda wani ɗankasuwar gwanjo a Ƙofar Wambai ya shaida wa BBC.

Jihar Kano na cikin wuraren da zanga-zangar ta fi rikiɗewa zuwa tashin hankali, inda rahotonni ke cewa an kashe mutane da dama. Sai dai zuwa lokacin haɗa wannan rahoton babu wasu alƙaluma daga gwamnati ko ‘yansanda na yawan waɗanda suka mutu.

A ranar Litinin ma – rana ta biyar – masu zanga-zangar sun fita wasu titunan birnin ɗauke da tutocin Rasha, yayin da rundunar ‘yansandan jihar ta ce tana cigaba da bin sawun kayayyakin da aka sace.

‘Ga kayan ina da su amma sai da na ci bashi’

Kano
Bayanan hoto, Duk da sassauta dokar hana fitar ba a buɗe kasuwar Sabon Gari ba

Bayan kwana biyu da saka dokar hana fitar, gwamnatin Kano ta sanar da sassauta ta, inda jama’a za su iya fita daga ƙarfe 8:00 na safe zuwa 2:00 na rana.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Duk da sassauta dokar, wasu manyan kasuwannin Kano sun cigaba da kasancewa a rufe saboda fargabar abin da ka iya faruwa.

Wasu kaɗan da suka buɗe kuma, kamar Kasuwar Ƙofar Wambai da ke ƙaramar hukumar Fagge, ‘yankasuwar sun ce kawai dai sun je ne bisa wasu dalilai.

“Yanzu fa duk wanda ka gani a kasuwar nan ya zo ne kawai ya nemi wani abu da zai kai gida, bai wai cinikin kasuwa ba,” kamar yadda wani ɗankasuwa a ɓangaren ‘yangwanjo mai suna Salisu ya faɗa wa BBC.

Salisu na da shago, inda yakan raba dilar gwanjo ga ‘yankasuwa. Sai dai tun bayan fara zanga-zanga a ranar Juma’a, da kuma dokar hana fitar da ta biyo baya kayan na cigaba da zaman daɓaro a kasuwa.

“Jiya [Lahadi] sai da muka gama ciniki da wani amma kuma fitar da kayan suka gagara, saboda kafin a kai kayan Kaduna lokacin dokar hana fita ya yi,” in ji shi.

“Ga kayan ina da su amma haka na nemi wani ya turo min bashin kuɗi.”

Shi ma Umar Usman ɗankasuwa ne a Kasuwar Sabon Gari da ke ƙwaryar birnin, wanda ke zaman gida a yanzu. Ita ma Sabon Gari na cikin kasuwannin da ke kulle.

“Mu da muke iya cin abin da muka tara ma Allah ya taimake mu tun da muna da shi,” in ji shi. “Ka san kuma waɗanda sai sun fita za su samo su ne suka fi yawa.”

To ko yaya suke yi da zaman gidan?

“Ai kawai hira muke yi da iyali, sai kuma kallon talabijin,” a cewar Salisu.

‘Dalilin da ya sa ba mu buɗe kasuwa ba duk da sassauta doka’

Kano

Asalin hoton, BBC

Bayanan hoto, Yadda shataletalen Beirut da ke haɗa kasuwannin Kano uku mafiya girma kenan ya kasance

Abu ne mawuyaci a iya ƙididdige asarar da ‘yankasuwa suka yi a ‘yan kwanakin da suka shafe a gida ba tare da fita ba, kamar yadda shugaban Kasuwar Singar Musa Nabanki ya shaida wa BBC.

Singar ce kasuwar kayan abinci da kayan kwali mafi girma a jihar Kano da ma yankin arewacin Najeriya, kuma tun daga fara zanga-zangar mahukuntan kasuwar suka ɗauki tsauraran matakan tsaro don kare dukiyoyinsu.

“Tun da aka fara zanga-zangar nan burinsu shi ne su shigo Kasuwar Singar,” a cewar Nabanki yana nufin ɓata-garin da ke fasa shagunan mutane. “Mun lura cewa mu kaɗai suke hari da ma, shi ya sa mu kuma muka ɗauki matakai masu tsauri. Sun zo an kore su, sun sake zuwa mun kore su.”

Daga cikin matakan da suka ɗauka har da hana bankunan da ke kewayen kasuwar buɗewa. “Saboda idan aka ga banki a buɗe mutane za su zaci an buɗe kasuwa ma, hakan zai sa mutane su kunno kai.”

A cewar shugaban, akwai mutum sama da 10,000 da ke harkoki a kasuwar tasu ta Singar, amma duk da sassauta dokar kasuwar na cigaba da kasancewa a rufe.

“Ni a matsayina na shugaba ba zai yiwu na ce a buɗe kasuwa nan take ba, dole sai mun duba yanayin a hankali tukunna, mun tattauna da sauran shugabanni kafin mu buɗe ta.

“Ganin cewa masu zanga-zangar na kukan yunwa wannan shi ne dalilin da ya sa wasu suka saka mana ido kuma suke ƙokarin su zalince mu. Ko gwamnati ma ai ka ga a hankali take sassautawa.”

'Buɗe kasuwar ya ba da fa’ida'

Kano

Asalin hoton, Getty Images

A gefe guda kuma, kasuwar hatsi mafi girma a Kano da ke Dawanau ta ci a ranakun Lahadi da Litinin na ‘yan awannin.

Shugaban kasuwar, Alhaji Muntaƙa ya ce buɗe kasuwar ya yi fa’ida gare su da kuma al'umar gari.

“Jiya da yau gaskiya kasuwa ta cika sosai, kuma an yi ciniki sosai. Ganin cewa kayan abinci na da muhimmanci sosai a wannan lokacin, buɗe kasuwar ya yi fa’ida sosai,” a cewarsa.