'Ni na kira ɗana zuwa wurin zanga-zanga, ashe ajali ne'

Saadatu Hassan

Asalin hoton, Saadatu Hassan

    • Marubuci, Muhammad Buhari Fagge
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Abuja
    • Aiko rahoto daga, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 4

Ga wasu, zanga-zanga wata gwagwarmayar neman 'yanci ce wadda ba za a taɓa mantawa da ita ba. Amma a wajen wasu wani ciwo ne da raɗaɗinsa ba zai taɓa warkewa ba.

Irin haka lamarin yake a wajen wata uwa da ake kira Maryam Musa da ke rayuwa a jihar Kano a Arewacin Najeriya.

Tarihin zanga-zangar da aka fara a Najeriya saboda tsadar rayuwa ranar 1 ga watan Agusta ba zai taɓa gogewa ba daga zuciyarta da kuma kwakwalwarta.

Domin kuwa a wannan zanga-zangar ne ta rasa ɗanta mai suna Usman Isma'il Muhammad, matashi ne ɗan shekara 21.

"Ni na kira ɗana zuwa wurin zanga-zanga ashe ajali ne, ashe ajali ne ke kiran shi," in ji Malama Maryam.

A tattaunawar da ta yi da BBC, Maryam ta ce ɗanta ya yi shirin tafiya zanga-zangar da aka kwashe kimanin wata daya ana ta shaida wa gwamnati ranar fara ta.

"Ya fito da wani takalminsa kafa ciki da bai cika sawa ba, ya ba da aka wanke masa, ya fito da wandonsa Jeans shuɗi da farar riga a matsayin kayan da zai sa.

"Da safe lokacin zanga-zanga ya yi, zan fita yana ɗaki a kwance, sai na ce masa ba za ka je ba ne, sai ya ce in tafi yana nan tahowa.

"Bayan na fita muna kan titin unguwar Sharada sai na sake kiransa, saboda a ƙafa muke tafiya ba ma sauri, ya ce zai zo, ba dadewa na sake kiransa ya ce ya fito. Kira na ƙarshe sai ya ce yana Kofar Ɗanagun". in ji mahaifiyar.

Daga nan suka ɗinguma suka tafi gidan gwamna da nufin kai masa ƙorafinsu a rubuce.

Ta ce ba daɗewa da zuwansu aka fara sa'insa da jami'ai, wannan ya ja suka fara harba hayaki mai sa hawaye. Rabuwarta da ɗanta kenan.

"Kasan hayaƙi mai sa hawaye akwai yaji, ana harba wa sai muka gudu kowa ya yi ta kansa. Sai kuma na ji an fara harbi. Kawai sai na ji gabana ya faɗi," in ji Maryam.

Daga nan ne ta ruɗe aka kai ta gida a babur.

'Na gane an kashe ɗana tun kafin a kawo gawarsa'

h

Asalin hoton, Saadatu Hassan

"Babu wanda ya fada min Usman ya mutu. A wajen da aka fara harbi jikina ya gaya min kamar an kashe shi.

"Ina shiga gida aka kira wayarsa, wai ana neman ɗan uwansa a ba shi ɗinki. Na ce ku faɗa min gaskiya ina Usman ɗina. Suka ce wai ɗinki za su bayar. Na ce ƙarya ne ku faɗa min an kashe shi.

"Suka ce jikkata ya yi, na ce to su kawo shi gida na gan shi. Na gane an kashe ɗana kafin a kawo gawarsa.

"Ina zaune aka shigo da gawarsa," in ji mahaifiyar marigayin.

Daga nan ne ta ce suka duba jikinsa suka ga an harbe shi a wuri biyu. A bayansa da kuma wajen kafaɗarsa.

Mahaifiyar ta ce sai da ta sha magani kafin ta samu ta yi barci saboda tunani.

'Shi ke daukar dawainiyata da ta 'yan uwansa'

B

Asalin hoton, Saadatu Hassan

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Maryam ta ce ita da ɗanta Usman fanni ɗaya suka karanta a rayuwa.

Usman ya kammala diflomarsa a makarantar koyar da aikin jinya a 2022. Maryam kuma ta fara a 2017 ta kammala a 2019.

Sai dai su duka biyun ba su da aikin yi.

Dalilin da ya sanya Maryam ɗaukar Usman ta kai sa wajen ƙaninta da yake kasuwanci.

"Usman ne na biyu cikin 'ya'yana shida. Yayarsa mace ce tana da shekara 23. Sai kuma wata macen da ke binsa mai shekara 19 da ƙaninta mai shekara 17. sauran ƙanana ne mace da na miji," in ji Maryam

Maryam ta ce da abin da yake samu a kasuwa da shi yake taimaka mata yake taimakawa mahaifinsa wanda a baya shugaban jam'iyyar siyasa ne a matakin ƙaramar hukuma.

"Matan mahaifinsa uku. Usman shi yake ɗawainiya da mu. Domin siyasa yanzu ta ba yi da mahaifinsa.

"Ko a ranar Laraba an biya shi albashinsa. Ya biya bashin abincin da ake bin mu. Sauran kuɗin na jikinsa, ko da aka kawo gawarsa an kwashe duka kuɗin jikinsa," in ji Maryam tana fada cikin damuwa.

Tabon rabuwa da shi ba zai taba barin cikin zuciyata ba, inji mahaifiyarsa.

Muna son gwamnati ta bi mana haƙƙinmu

Kamfani Beacon Consulting mai bincike kan sha’anin tsaro a yammacin Africa ya ce akalla mutane 20 aka kashe a zanga zangar da aka fara ranar Alhamis.

A cikin rahoton da ya fitar, ya ce an kashe mutane 6 a jihar Neja, hudu a Kano, hudu a Borno, uku a Kaduna biyu a Jigawa sai kuma daya a Kebbi.

Babu kuma wanda ya san adadin waɗanda suka raunata dalilin wannan zanga-zanga a faɗin Najeriya.

Usman yana cikin mutanen da aka kashe, waɗanda har yanzu gwamnati ba ta ce komai ba a kai.

Amma mahaifiyarsa da ba ta da wanda za ta rike domin ya taimaketa, ta ce tana fatan gwamnati ta shiga lamarinta, ta bi mata haƙƙin ɗanta da ta yi zargin jami'an tsaro ne suka kashe shi.